Sashe 69
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Amma uncle fa? Uncle fa Amma. Ya ma za'a yi ace uncle ne mijina? Ya za'a yi na aureshi?”
Nana ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, Ta kifa kanta kan cinyar Amma tana jan numfashi. Shafa bayanta Amma ta dinga yi a hankali cike da tausayinta ta ce“to mene ne Nana? Ba uncle ɗin ki bane. Kuma ai kin san ba zai taɓa cutar dake ba ko?”
Sake ɗago kanta ta yi tana kuka ta ce“Amma ya za'a yi na zauna dashi a matsayin miji? Uncle ne fa. Ya za'a yi na aureshi? Ni wallahi ba zan iya baaa!”
Ta sake faɗawa jikinta tana kuka har da birgima. Shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba dan ta san ba saurarenta zata yi ba, Ta ɗauke kanta tana kallon ƙofa, ita kanta ba son auren nan take ba. Saboda Abdusammad ya yi wa Nana girma. Ta sauke zazzafan numfashi tana maida idanunta kanta jin har sannan bata daina kukan ba yasa ta ce
“Ni ɗagani idan ba zaki yi shiru ba. Mene ne dan kin aureshi? Ina ruwanki da kasancewarsa uncle ɗinki? Ke ba matsayin miji zaki ɗaukeshi ba.”
Tashi zaune ta yi cikin gunjin kuka ta ce“to me yasa za'a ce na aureshi? Ita Maimoon ta auri Yaya Aliyu, ita Amrah ta auri Yaya Sultan, ita kuma Hamida ta auri Yaya Hamid. To sai ni kuma a aura min uncle? Bayan kuma tsoho ne!”
Ta faɗa tsakiyar gado tana kuka kamar ranta zai fita. Murmushi Amma ta yi dan cikin kukan nata har da na banza, ta tashi dan ba zata iya da halin Nanar ba ta ce
“Abdusammad ɗin ne tsoho?”
“wallahi tsoho ne Amma. Kalli fa babu mai aure sai shi, kuma har ƴa ce dashi. To ni ya za'a yi na zauna dashi a haka?”
Amma ta ɗan waro idanunta tana kallonta ta ce“au dan yana da aure shi ne ya tsufa? To shi Aliyun ba kusan sa'ansa bane. Daga shi naga sai shi”
Ɗago kanta ta yi tana murza idanunta cikin kuka ta ce“to ai dai ya girme shi, duk fa ya girmi kowa.”
Amma ta ɗan ja tsaki ta ce“to tun da ba zaki haƙura ba bari zan je na faɗawa Abban naki shi sai ya san yanda zai yi dake.”
Daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin. Nana ta sakko ƙasan gadon ta zube a wajen ta sake fashe da wani sabon kukan mai cin rai, a fili kuma ta dinga cewa
“na shiga ukuna, wayyo Allahna. Wallahi bana sonsa.”
Ta dinga maimata maganar can kuma ta baje a wajen tana birgima.
Amma na fita ɗakin Abba ta shiga, zaune ta same shi gefen gado ya gama shirin kwanciya. Ta ƙaraso ciki ta tsaya jikin mirror ta yi shiru, kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana gyara zama pillow ɗin gabansa ya ce
“Madam lafiya dai?”
Sauke numfashi ta yi tana kallonsa ta ce“Ni ko baka ganin auren nan akwai matsala?. Nana yarinya ce ƙarama, shekarunta 17 fa kawai. Abdusammad kuma ya girme mata, girma bana wasa ba. Sai nake ganin kamar zamansu ba zai yi dai-dai ba.”
Abba ya dinga kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa, Can kuma ya yi mata alama da ta zo da hannunsa. A sanyaye ta ƙaraso wajen ta zauna gefensa, Abba ya kama hannunta na dama yana murzawa a hankali ya ce
“Rabi'a kenan. Ya kamata a ce kin kwantar da hankalinki, na san kin san wane Abdusammad, kin san abin da zai iya da kuma wanda ba zai iya ba. Bana da damuwa akansa na san zai kula da Nana, kulawa irin wadda ba kowane namiji ne zai yiwa mace ba. Ba zai taɓa bari ta yi kuka ba, saboda ba tun yau ba na san yana sonta, kawai ba zai iya faɗa bane saboda yana ganin kamar hakan bai kamata ba. Yanzu kuma da ya samu dama kina ganin zai bari ta yi kuka a gidansa? Kina ganin zai gaza wajen kulawa da ita?.”
Numfasawa Amma ta yi ta girgiza kanta kana ta ce“nima na san ba zai bari ta yi kuka ba, amma fa ka sani ba shi kaɗai bane. Yana da mata har da ƴa, sannan matarsa babba ce wadda ta mallaki hankalin kanta, kuma tana da wayo. Sannan ita ce ta yi yunƙurin cutar da Nana, yanzu kana ganin idan ta shiga gidan a matsayin kishiyarta zata barta ta zauna lafiya? Nana yarinya ce. Duk da rashin jinta da kuma neman faɗanta bata da wayo, cikin ruwan sanyi za'a iya cutarta ba tare da ta gane ba. Tana da saurin yarda da mutum. Shi ne abin da nake tsoro wallahi”
Abba ya yi shiru yana nazarin maganarta, tabbas tana da gaskiya, Nana bata da wayo ko kaɗan. Ya sauke numfashi sannan ya ce“Duk wannan ba zai zama damuwa ba in sha Allah. Babu abin da zai faru, mu yi musu fatan zaman lafiya” jiki a sanyaye Amma ta ce“tam shikenan, Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka cikin auren.” murmushin jin daɗi ya yi kafin ya ce“Amin ya rabbi.”
Ta mike tsaye tana fadin“sai kuka take yi na yi nayi da ita taƙi shiru.”
Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“Allah sarki, tausayi take bani, zata shiga cikin wata rayuwa wadda bata san da ita ba. Ki barta ta yi kukan, ba koda yaushe ake hana mutum kuka ba, tana buƙatar ta yi, so just leave her.”
Jinjina masa kai Amma ta yi ta ce“daman na rabu da ita in sha Allah. Gobe da safe zan kira Ramlah ta zo” okay ya ce mata sannan ya zare glasses ɗin idanunsa ya kwanta dan dare ya yi sosai, Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta nufi ƙofa ta fita dan bata gama abin da take ba.
Daren ranar kasa bacci Nana ta yi, ta dinga kuka har sai da muryarta ta dashe, ganin dare ya yi sosai ya sanya ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta zura hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila, bayan ta gama ta zauna a wajen ta dinga addu'o'i neman yafiyar ubangiji sannan kuma da samun zaman lafiya. Daga bisani kuma ta ci gaba da kukanta har asubahi, Gari ya fara haske wajejen 6 na safe aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, bata iya ɗaga kanta ba, hasalima bata san an shigo ɗin ba saboda tunanin da ta yi zurfi a cikinsa. Abba ya ƙaraso gaban gado ya zauna yana kallonta ganin yanda ta kifa kanta kan cinyoyinta. Ya dade yana kallonta kafin ya yi gyaran murya ya taɓata, a firgice ta buɗe idanunta, ganin shi ne ya sanya ta sunkuyar da kanta jiki a sanyaye ta ce
“Abba ina kwana”
Duk da muryarta da bata fita hakan bai hana shi jin abin da ta ce ba. Sai dai bai amsa ta ba, Madadin hakan ma sai ya sakar mata murmushi, ya yi mata alamar ta zo ta hannunsa. A danya ta mike ta dawo kusa da shi ta zauna Abba ya ware mata hannayensa duk biyun, kamar jira take kuwa ta shige jikinsa tana sakin wani marayan kuka, Kuka take mai tsuma zuciya, kuka ne wanda ke nuna irin rauninta gaban mahaifin nata. Shi kansa Abba sai da jikinsa ya yi sanyi, Ya dinga dukan bayanta a hankali ba tare da ya yi yunkurin hanata kukan ba, Madadin hakan ma sai ya dinga cewa
“Cry! Cry Nana, cry as much as you can. Cry Nana.”
Kamar kuwa turatan yake haka ta dinga ƙara sautin kukan nata tana ƙanƙameshi. Shima ya sanye duk hannunsa biyun ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya, Allah ya sani yana mugun sonta, yana son gudaliyar ƴar tasa fiye da tunanin mai tunani. Koda wasa baya son abin da zai ɓata ranta, ballantana har yaji kukanta, shiyasa a tsawon rayuwarsu tare zai iya ƙirga sanda ranta ya ɓaci a dalilinsa. Sun ɗauki lokaci mai tsawo a haka har sai da ta fara rage sautin kukan nata don kanta. Ya ɗagota daga jikin nasa ya fara goge mata hawayen nata da hannunsa, ita kuwa sai ƙara narkewa take dan ta samu abin da ta ke so. Kuma sosai taji zuciyarta ta mata sanyi sakamakon kukan da ta yi, Sai da yaga ta yi shiru gaba ɗaya sai shessheƙar kuka kawai take sannan ya ce
“Yanzu kin haƙura?”
Gyaɗa masa kai ta yi a hankali, Ya yi murmushi sannan ya ce“Yauwa Allah ya yi miki albarka, Ya baki zaman lafiya a gidan mijinki. Ya...”
“Abba da gaske uncle zan aura? Da gaske ni matarsa ce?”
Ta katse shi da sauri jin ya yi maganar gidan mijin. Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce
“Eh Nana, da gaske ne, Abdusammad shi ne mijinki. Kuma ina fatan ki yi masa biyayya, ki rufe sirrin mijinki, ki zauna dashi lafiya. Ki kula da dukiyarsa, ki zama mata tagari a cikin gidansa. Koda wasa kada ki bari mijinki ya yi kuka dake, kada ki bari ya kawo ƙararki. Ki zama yarinyar kirki kin ji Khadijatou.”
Samun kanta ta yi da sake fashewa da wani sabon kukan, ta sake rungumeshi tana kukan ta ce“Abba uncle fa? Uncle ɗina ne, daman ana auran uncle? Ustaz ɗin mu ya ce mana ba'a aure da uncle. Me yasa ni zai aureni?”
Murmushi irin na manya uncle ya yi sannan ya ɗago kanta ya gyara mata zama yanda zata fahimce shi sosai ya ce“Haka ne, ba'a aure da uncle. Amma ba irin naki uncle ɗin ba”
Da ɗan mamaki ta kalleshi, ya jinjina mata kai ya ce“Abdusammad ɗan Yayana ne, hakan na nufin shi ɗin cousin ɗinki ne. Kuna ce masa uncle ne dalilin kallon mahaifin da ku ke masa, ba wai dan shi ɗin ƙanina bane. Abdusammad ɗana ne kamar yanda ki ke ƴata, dan haka aure a tsakaninku halattaccan abu ne, aure ne na raya sunnar ma'aiki, dan haka idan kina kallon babu aure tsakaninku ina son ki daina daga yau kin ji.”