← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 125

Sashe 82

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko saurarensa bata yi ba ta ci gaba da kukanta, Ya kalli ɗan ƙaramin bakin nata wanda ya sha lip gloss sai sheƙi yake. Haka kawai yaji tsigar jikinsa na tashi, Koda wasa bai son yaga mace ta saka lip gloss musamman idan yana da alaƙa da ita, Yanzu zai yi jikinsa na neman sauyawa. Ya fara ƙoƙarin kai hannunsa domin ya goge mata, danƙon da yaji yasa ya tabbatar da ba kaɗan ta shafa ba, kuma ba lallai ya fitan a hakan ba, Dan haka ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya. A hankali kuma ya durƙusar da kansa daidai fuskarta, Lokaci ɗaya kuma ya ɗora bakin nasa akan nata ya fara tsotsa a hankali. Wata irin zabura Nana ta yi, Ta ƙamkameshi tana jin wani irin fitsari na tawo mata, sai da ya suɗe kaf man leɓan bakin nata sannan ya sanya ɗayan hannunsa ya buɗe bakin nata, Cikin hanzari kuma ya zura bakin cikin nata. Kusan sumewa Nana ta yi jin yanda yake sauke mata wasu azababbun kisses, nan da nan jikinta ya saki ta gagara koda motsa ɗan yatsanta ne. Jin hannunsa akan ƙirjinta ya sanya sakin wani marayan kuka, Cikin ikon Allah ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi, Kasancewar jikinsa a sake yake ya sanya ya yi baya, Ta tashi da gudu ta shige toilet ta rufe ƙofar gam. Tashi ya yi ya biyo bayanta ya tsaya a bakin ƙofar muryarsa a ɗan shaƙe ya ce

“Kee! Nana! Nana!”

Ban da kuka babu abin da take, Ta sulale a ƙasan bayin tana kukanta, Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan ƙofar kamar ba zai magana sai kuma ya ce

“Ki ka ce na shirya cin amarci na siyo miki kaza. To gashi na kawo miki ai”

Girgiza kanta ta dinga yi cikin kuka ta ce“a'a uncle ni bana son kazar, wallahi bana so! Bana son kazar amarcin, ka ɗauki kazar ka tafi da ita.”

Sauke zazzafan numfashi ya yi jikinsa har wani rawa yake ya ce

“Ai baki isa ba! Tun da ki ka yarda na kawo kaza dole ki fito naci amarcin!”

08106608363
Nanameera.
*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 50.

Sake rushewa ta yi da wani sabon kukan ba tare da ta ce komai ba, Ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata kafin ya sake cewa“Idan ki ka bari na buɗe ƙofar nan da kai na sai na baki mamaki!” Sake cure jikinta ta yi waje ɗaya ta sanya hannunta ta rufe bakinta tana ci gaba da kukanta a hankali. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya ya bar ɗakin, Tana jin ƙarar rufe ƙofa amma sam taƙi tashi ta fito, Dan tunaninta ba tafiyar ya yi ba. Tana nan zaune har kusan ƙarfe 11:00 na dare, Bacci ya fara ɗaukanta a zaunen, Gajiya ta yi dan kanta ta tashi ta buɗe ƙofar toilet ɗin a hankali tana leƙa ɗakin. Ganin da gaske babu kowa a ciki ya sanya ta fito, Kai tsyae kuma wajen ƙofa ta nufa ta murɗa key kuma ta bar shi a jiki, Sannan ta koma ta cire kayanta ta ɗauki na bacci ta saka ta hau kan gadon, Ko ta kan ledar kazar dake wajen bata yi ba. Ta duƙunƙune jikinta da duvet sannan ta rufe idanunta, Sai dai kuma sam baccin yaƙi zuwar mata gani take idan ta rufe idanunta Abdusammad zai dawo ɗakin ne. Dan haka ta fara kuka a hankali, A haka har bacci ɓarawo ya saceta.

Washegari around 9am ya tsaya jikin ƙofar, Kamar ya tafi sai kuma ya fara knocking a hankali. Nana dake zaune ƙasan gado ta jingina kanta da jikin gadon ta ɗago kanta a firgice, Kallon ƙofar ta dinga yi jiki a sanyaye. Ya ci gaba da knocking dan duk tunaninsa bacci take yi, Ganin bata da niyyar buɗewa ya sanya ya ce

“Nana! Nana! Nana!”

Kasa amsawa ta yi, Nan da nan jikinta ya fara rawa. Dan ita har ga Allah yanzu tsoronsa take, Ta miƙe ta koma can ƙarshen gado ta zauna tana ci gaba da kallon ƙofar. Gajiya ya yi da bugun ya ce“Idan ki ka bari na ɗauko maƙulli na bude ƙofar sai ranki ya ɓaci!.”

Tura baki gaba ta yi ta sunkuyar da kanta, Ya bar jikin ƙofar, Shirun da taji an yi ya sanya ta miƙe a hankali ta ƙarasa gaban ƙofar. Ta kasa kunnenta a jikin ƙofar amma bata ji alamar yana nan ba, Dan haka ta zare key ɗin ta buɗe ƙofar ta leƙa a hankali. Cikin rashin sa'a taji ya turo ƙofar da ƙarfi, Ta yi baya ta faɗi cikin ɗakin. Tsayawa ya yi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, Ta miƙe da gudu ta nufi hanyar toilet, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa ya sanya ƙafa ya taɗeta, ta yi baya zata faɗi ya riƙota ta faɗa jikinsa. Wata irin zabura Nana ta yi tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya haɗe fuska babu alamar wasa ya ce

“Kin nutsu ko saina mareki?”

Girgiza kanta ta fara yi tana hawaye ta ce“Dan Allah uncle ka yi hakuri, Dan girman Allah wallahi ba zan sake ba. Ba zan ƙara ba, Ka sakeni!”

Ta ƙare maganar tana kuka. Bai ce mata komai ba ya jata har gaban gadon, ya zauna sannan ya zaunar da ita gefensa har sannan babu alamar walwala akan fuskarsa ya ce

“Ni abokin wasanki ne da zan dinga kiran ki kina ji ki min banza? am I play with you?”

Girgiza kanta ta yi a hankali tana sunkuyar da kanta, Ya yi kwafa sannan ya ce“Duk ranar da ki ka sake min irin haka sai na ɓata miki, Kinji abin da na ce.?”

Gyaɗa masa kai ta yi nan ma, Ya yi shiru yana kallon yanda take ta rawar jiki, Ɗauke kansa ya yi yana karewa ɗakin kallo. Lokaci ɗaya idanun sa ya sauka akan ledar kazar dake kan drawer, Miƙewa ya yi ya ƙarasa wajen ya ɗauko ledar ya dawo. Nana na ganin haka ta fara ja da baya, Buɗe ledar ya yi yaga babu abin da ta taɓa a ciki, Ya mayar ya ajiye a ƙasa sannan ya ce

“Kin ci kazar?”

Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce“A'a wallahi, Ban ci maka ba uncle. Ban ci ba wallahi!”

Ta ƙare maganar tana kuka, Sake haɗe rai ya yi kafin ya ce“Me yasa? Ba cewa nayi ki ci ba?”

“Na ƙoshi, Ni bana ci.”

Ta yi maganar a sanyaye. Taɓe baki ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“To ni yunwa nake ji, Tashi ki mana warming ɗinta sai ki kawon” Jikinta har rawa yake ta mike, ta ɗauki ledar sannan ta fice daga ɗakin. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi.

****
Zahra ta dinga kallon Anty Khadijah da mamaki can kuma ta ce“Lafiya Anty da safen nan?” haɗe rai Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Dallah magana na zo mu yi dake.” Zahra ta kalli hanyar sama sai kuma ta kalli Anty Khadijah ta ce“Doctor yana nan, muje waje.” Taɓe baki Anty Khadijah ta yi sai kuma ta juya ta fice daga parlourn tana taunar cew gum, Zahra ta sauke numfashi sannan tabi bayanta dan daman hijabi ne a jikinta.

A ƙasan wata bishiya suka zauna kan fararen kujeru, Zahra ta yi shiru tana jiran taji abin da Anty Khadijahn zata ce. Ita kuwa Aunty Khadijah Shiru ta yi tana kallon Zahra kamar yanda malamin ya ce mata, After some minutes Zahra ta ce

“Anty mene ne? Naji kin yi shiru.”

Numfasawa Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“Daman akan maganar auren nan naki ne, na ce wai kin haƙura zaki zauna da kishiya kenan?”

Shiru Zahra ta yi kamar mai tunani, Anty Khadijah ta yi murmushi sannan ta ce“Ki yi tunani Zahra. zamanku da ita ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba, Saboda kin san ita yar uwarsa ce, a gabanki zai dinga nuna mata tafi ki, kuma ma ban da abin ki ya za'a yi mutum ya zauna da yarinyar da ya raina. Har da ke fa aka yi rainonta, Ace kuma yanzu ta zo ta aure mijinki, Tana kwana ɗaki ɗaya dashi, Haba wannan abu har ina!”

Aunty Khadijah ta ƙare maganar tana kallon Zahra to see her reaction. Zahra da duk abin duniya ya dameta ta girgiza kanta jiki a sanyaye ta ce “To ya zan yi Anty? Dole nayi hakuri kamar yanda Umma ta ce min. Da badan na shiga na fita na saka Siyama ta auri Safwan ba da Nana bata auri mijina ba, kin ga ashe Allah ne ya mata sakayya, Dole na yi haƙuri.”

Taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“To kenan zaki ci gaba da zama a haka kamar wata mara yanci kenan?”

Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“A'a. Na san doctor ba zai taɓa fifita Nana akaina ba, saboda ya san me yake, Yana da ilimi kuma yana aiki da iliminsa. Har zuwa yanzu ban ga ya yi min wani abu da ke nuna rashin kyautatawa ba.!”

Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta gyaɗa kanta ta ce“Haka ne, To Allah ya ƙara haɗa kan ku.”

“Amin Aunty.”

Zahra ta yi maganar a sanyaye, Anty Khadijah ta ce“Amma duk da haka bai kamata ki zauna haka babu wani abun tsare jiki ba. Kin san ita kishiya muguwar aba ce, Shiyasa na karbo miki wani magani ki samu ki jiƙa da ruwan ɗimi ko shayi ki sha, Babu abin da zai sameki in sha Allah.” Ta ƙare maganar tana laluba jakarta, Zahra ta yi shiru tana kallon ta har ta dauƙo wani ƙullin magani karami. Zahra ta karɓa sannan ta ce“To Anty Nagode sosai Allah ya ƙara girma.” Da Amin ta amsa sannan ta ce“Yaushe zaku koma ne?” Zahra ta yi murmushi ta ce

“Gobe idan Allah ya kai mu.”

Zaro idanu Anty Khadijah ta yi ta ce“Da wuri haka? Amma shi ne baki zo gida ba?”
Chapter 82 · 0% Book details