← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 125

Sashe 16

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka ƙaraso apartment ɗin Aliyu babu wanda ya ce komai a cikinsu, ya samu Aliyu zaune cikin garden dashi da Maimoon, tana ganinsa ta miƙe muryarta na ɗan rawa ta ce"barka da yamma uncle" ba tare da ya kalleta ba ya ce"Barka" ta bi ta gefensu ta bar wajen da sauri. Zama ya yi kan farar kujera yana kallon Aliyu babu yabo babu fallasa ya ce"and what's this? mene zaka kira yarinya apartment ɗinka? kome zaka tattauna da ita ba kai ya kamata kaje gidansu ba?" Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce"to malam naji ba zan sake ba" harararsa Abdusammad ya yi ya ce"kana ɗaukan maganata wasa ba? kai a matsayinka da shekarunka kana ganin ya dace ka dinga keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba?" Dafe kansa ya yi ya ce"oh my god, naji ba zan sake ba, shikenan?" taɓe baki ya yi ya ce"idan ma ka sake mene nawa a ciki?" Daga haka ya kalli Nana da ke tsaye a wajen kamar statue ya ce"tafi gida" bata ce komai ba ta juya ta bar wajen da sauri. Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya mai da idanunsa kan Abdusammad ya ce"wannan yarinyar ko kai ne ka haifeta sai haka" kwalin dabinon da ke wajen ya farka ya ɗauka guda ɗaya ya sanya bakinsa bayan ya yi bismillah sannan ya ce"to ai ni ɗin na haifeta, kuma ma da ace nayi auren wuri ai da na haifi kamarta, she's 16 fa yanzu"

"Bata ma cika ba"

Aliyu ya yi maganar yana dariya. Shiru ya yi kamar me tunani sai kuma can ya ce"ni ko na tambayeka mana" Aliyu ya gyara zamansa ya ce"ina ji"

"Yaushe aka yi maganar auren yaran nan?"

Kallonsa ya yi sai kuma ya ce"wani abun ya faru ne?"

Haɗe rai ya yi ya ce"amsa zaka bani malam"

Murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce"ba'a fi 3days ba, nan da 1 month za'a ɗaura auren idan Allah ya kai mu" jin jina kai Abdusammad ya yi kafin ya sake cewa"da wa da wane za'a musu auren?"

Murmushi kawai Aliyu ya yi sannan ya ce"dukansu mana, Maimuna, Hamida, Amrah sai kuma Nana"

"Nana dai?"

Gyaɗa masa kai ya yi, ya zare kwallon dabinon daga bakinsa kana ya ce"wannan yarinyar? Ba sun girmeta ba?" Aliyu ya ce"eh ita ce ƙarama a cikinsu, sa'ar Juwaira ce fa, kawai dai tana da garin jiki ne shiyasa ta shiga cikinsu, kuma ita ma ta kammala karatun secondary" taɓe baki ya yi ya ce"and saboda haka yasa za'a aurar da ita yanzun? Wane ya bada wannan shawarar?"

Aliyu ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce"masu bada shawarar aurar da ya'yan gida mana, su Uncle ne da Hajiya" tashi ya yi yana gyara zaman rigar jikinsa kafin ya ce"I'll talk to them in sha Allah, ya kamata a ɗan bar irin wannan auren haka nan"

Tashi shima Aliyun ya yi a ɗan dame ya ce"haba Buddy, me ya sa koda yaushe ka ke Ƙoƙarin creating problems ne? haka fa ka yi akan aurenka, ka je ka auri Zahra duk da ka san ba'a irin wannan auren, ba ka yi shawara da kowa ba, ka yanke hukunci sannan yanzu ma ka ce zaka yi magana akan auren yara?"

Ɗauke kansa ya yi ba tare da ya ɗauki maganar Aliyun da muhimmanci ba ya ce"eh na auri Zahra saboda ita nakeso, and na yaba da hankalinta da kuma tarbiyyarta, saboda haka yasa na aureta duk da bata kasance ƴar cikin wannan dangin ba. Ba wai ina son tayar da hankalin dangi bane, a'a ina so ne naga sun yi abin da ba za'a tauyewa wani ko wata haƙƙi ba! yanda ban yarda da auren zumunci ba haka ba zan bari a tilastawa yara auren zumunci ba! Idan ma za'a yi to a zauna a yi zube ban kwarya kowacce ta faɗi wanda take so kafin sannan a aura mata shi, idan kuma ba haka ba sai dai a haƙura da auren wlh!"

Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, sai kuma ya bar wajen, Da idanu kawai Aliyu ya bi shi yana tunanin maganganunsa, Allah ya kiyaye dai kada ya tada tarzoma irin ta wancan lokacin, Aliyu ya yi maganar a ransa yana sauke numfashi sai kuma ya juya shima ya bar wajen.

Kai tsaye apartment ɗinsa ya koma, sanda ya shiga zaune ya tarar da Noor jikin Zahra tana danna wayarta, tana ganinsa ta sakko daga jikinta da gudu ta zo ta riƙe ƙafafunsa cikin muryarta ta yarinta ta ce"welcome Abbiey" hannunsa ya sanya ya ɗauketa ya ɗagata sama ya yi juyi da ita, ta dinga sheƙa dariya wadda ta fito da asalin kyanta da kuma kamarta dashi, kafin daga bisani ya mai da ta kafaɗarsa yana murmushi ya ce"thank you my baby girl, yau kin yini wajen su Hajiya Babba ko?" gyaɗa masa kai ta yi tana kwanciya a kafaɗar tasa ta ce"ina can wajen Hajiya da su Aunty Juwaira, muna ta wasa" sauketa yayi yana faɗin"yarinyar ƴar gata, je ki wajen Ummi" da gudu ta tafi shi kuma ya nufi hanyar upstairs da sauri. Da idanu kawai Zahra ta bishi sai kuma ta sauke numfashi ta kalli Noor ta ce"baby zo nan ki kwanta" hawa jikinta ta yi ta kwanta kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa. Zahra ta dinga shafa kanta har baccin nata ya yi nisa sannan ta ɗauketa ta haura sama da ita. A bedroom ɗinta ta kwantar da ita, ta rufa mata duvet saboda sanyin yamman daya buso, sannan ya fita daga ɗakin kai tsaye kuma nasa bedroom ɗin ta nufa.

Zaune ta sameshi kan sofa yana danna system ɗinsa, ya zare rigar jikinsa duk da sanyin da ake, faffaɗan ƙirjinsa ya bayyana mai ɗauke da zanen tato a jiki, wajen ya yi luf da kwantaccen gashi wanda ya ƙara masa kyau. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a ƙasansa ganin bai kalleta ba ya sanya ta ce"wane ya taba min kai ne?" ta ƙare maganar tana ƙoƙarin taɓa fuskarta, janye hannunta ya yi yana faɗin "babu komai" Zahra da ɗan murmusa kafin ta ce"kamar ban sanka ba? Dan Allah me aka yi maka?" Ɗago dara-daran idanunsa ya yi ya zuba mata, ta yi saurin sunkuyar da mata saboda kwarjinin da ya yi mata, hannunta ya kamo yana faɗin "har yau baki daina jin kunyata ba?" Murmushi ta dinga yi ƙasa-ƙasa, ya tashi yana riƙe hannunta ya ce"zo ki ji" miƙewa ta yi tabi bayansa kamar yanda ya umarceta.

****
Bayan sallar magriba tana zaune a parlon tana karatun wani novel mai taken “Wrong decision” wayarta dake gefenta ta fara ƙara, ta gefen ido ta kalli wayar ganin numbern ya sanya bata ɗauka ba, ta mai da Idanunta kan karatun duk da ba fahimta take ba. Amma na zaune opposite ɗin ta tana buɗe sabbin mayafan data siyo ɗazu taji wayar nata ringing, ɗan tsaki ta yi ba tare da ta kalleta ba ta ce

"ki ɗaga kiran ko kuma ki kashe wayar kin daman"

Toh kawai ta iya cewa sannan ta ɗago wayar ta saka ta a Flight mode ta mayar ta ajiye, after 5mins Amma ta tashi bayan ta gama haɗe veils ɗin ta diba ta nufi daƙinta, tana rufe ƙofar Nana ta tashi ta ɗauki wayarta da gudu ta fita daga cikin parlon. A jikin balcony ta tsaya ta leƙa compound ɗin bata ga kowa ba sannan ta kunna wayar ta danna numbern da aka yi kiran, buga ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren Junaid ya ce

"Why aren't picking my calls?"

Murya can ƙasa ta ce"an hanani ne a gida"

Junaid ya ɗan yi shiru kafin ya numfasa ya ce"kin faɗa musu abin da nace miki?" Gyaɗa kai ta yi kamar yana gabanta sannan ta ce"eh"

"Me suka ce?"

Ya faɗa a takaice.

"They refused!"

Ta yi maganar babu gwarin gwuiwa.

Furzar da iska ya yi daga bakinsa har taji a cikin wayar kafin ya ce"yanzu kenan ya za'a yi?"

Girgiza kanta ta yi ta ce"nima ban sani ba, ina ga kawai mu haƙura sir"

"Mu haƙura? Nana ko dai daman baki sona ne?"

Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce"A'a ina sonka mana, amma ba zan iya bijirewa gidanmu ba, koda na gwada ba zan yi nasara ba sai dai na ɓata kaina a wajen kowa, sannan Ammata ta ce kar na sake maganar idan har ta isa dani, kaga dole nayi shiru. Bana son abin da zai tada hankalin yan gidanmu, zan haƙura na auri wanda suka zaɓa min koda hakan na nufin rugujewar farin cikina!"

Junaid ta dinga kallon screen ɗin wayar baki buɗe, he can't believe a ce ta haƙura da sauri haka, jin an ɗauki lokacin bai ce komai ba ya sanya ta kalli wayar ko kiran ya katse, gani ta yi yana kan layi dan haka ta sake maidawa kunnenta a sanyaye ta ce

"Zan yi haka ba wai dan bana sonka ba, sai dan na kare mutuncin iyayena da kuma gidanmu gaba ɗaya"

Runtse idanunsa ya yi yana jin kalamanta kamar tana ɗiga masa dalma ne a cikin zuciya, koda wasa bai yi tunanin rabuwa da ita nan kusa ba, kuma ba zai taɓa barin hakan ta kasance ba. Ya saita nutsuwarsa kafin ya ce

"Shikenan Nana naji, amma ina son na ganki idan har babu damuwa"

Muryarta a ƙarye ta ce"again kuma sir?"

Gyaɗa kansa ya yi sannan ya ce"eh Nana, ina son magana da ke, koda hakan na nufin magana ta ƙarshe tsakaninmu, ki min wannan alfarmar Nana!"

Lumshe idanunta ta yi hawaye na zirarowa kan kuncinta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin ba zata iya rejecting ɗinsa ba ta ce

"Shikenan sir, I'll, a gidan Aunty Ramlah?"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"eh ko anan ɗin ma, zan faɗa miki sanda nakeson mu haɗun sai ki zo"

Ta numfasa sannan ta ce"okay sir"

"Thank you Nana"
Chapter 16 · 0% Book details