← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 125

Sashe 52

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Nana kuwa kasa bacci ta yi, haka kawai taji zuciyarta na karyewa, taji kamar wani mummunan abu na shirik faruwa da ita. Dan haka ta tashi ta shige toilet ɗin Amma ta ɗauro alwala sannan ta fito ta sanya hijabi ta fara gabatar da sallolin nafila. Bayan ta idar ta zauna ta dinga addu'o'i kala da kala har kusan 3 na dare. A ɗakin Abba kuwa Amma ce zaune ƙasan gado hannunta riƙe da cazbaha tana ja dan sam ta kasa bacci, idan ta tuna gobe za'a ɗaura auren Nana ta yi nesa da ita sai taji duk jikinta ya sake sanyi, kamar yau ta haifeta aka dinga zuwa kallonta amma ace har ta yi girman da za'a aurar da ita, itama ta zama matar gida. Wannan tunanin shi ne abin da ya hanata bacci, ga kuma tausayin Nana sanin ba son auren take ba, babu yanda bata yi da Abba ba amma sam yaƙi fahimta, ya kuma kafe akan dole sai Nana ta auri Safwan. Dan haka ta rabu dashi bata sake cewa komai ba, shi ma bai sake yi mata magana ba sai sabgoginsa yake a ɗakin, ya dinga waya da mutanensa na ƙasar waje wadanda zasu halarci ɗaurin auren da za'a yi gobe, a zahiri idan ka ganshi zaka iya rantsewa akan babu abin da ke damunsa, amma cikin zuciyarsa fal take da ƙunci da kuma damuwa. Ji yake kamar kada gobe ta yi domin bai shiryawa jin kukan tilon ƴar tasa ba, duk da bai san dalilinta na ƙin auren ba, amma yaji shima baya son auren. Sai dai ba zai taɓa iya yarda ya ce haka ba saboda gudun lalacewar zumunci. Dan haka ya dinga ƙoƙarin riƙe kansa da kawar da komai daga ransa, wanda haka yasa Amma ta dinga tunanin ko dai bai damu da Nanar bane.

Kiran Sallar asubahin farko mutane suka fara tashi, masu ɗora tuwon ɗaurin aure suka fara aikinsu haka ma masu yin sauran girke-girke. Wajejen ƙarfe 6 na safe kuwa sai mutum ya ɗauka 12 ce ta yi saboda yanda ake shige da fice a cikin estate ɗin, dangi da abokan arziki sai kai kawo suke. Burin kowa ya gama abin da yake gabansa domin ɗaurin auren karfe 10:30 na safe ne.

Ƙarfe 7 saura Hamida ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Nana na zaune gefen gado ta zuba uban tagumi dan bata san ma ta shigo ɗin ba, Hamida ta girgiza kanta tana mamakin yanda Nana ta fi kowa damuwa akan auren, a hankali ta taɓata ta ce

“Nana”

A ɗan firgice Nana ta kalleta sai kuma ta sauke numfashi ta ce“na'am”

“ki zo in ji Mama”

To kawai Nana ta ce sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa, ta zura hijabin da ta yi sallah sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin Hamida na biye da ita. Gaisar da mutanen dake parlon suka yi sannan suka fice, Hamida sai hira take mata ita kuwa ta kasa cewa komai sai uhm da uhm'uhm, a haka har suka ƙarasa apartment ɗin su Hamidan.

Koda suka shiga ciki Nana turus ta yi ganin su Amrah, Maimoon da kuma Haule. Kowannensu zaune sun yi shiru suna jiran su ji abin da Mama zata ce, zama Nana ta yi gefen Maimoon sannan ta gaida Mama, Mama ta amsa fuska a sake sannan ta gyara zamanta tana kallonsu duka ta ce

“Nasan kun san abin da ake nufi da aure, ba sai na yi wani dogon jawabi ba. Kawai dai zan ɗan tunasar daku ne na kuma ƙara muku haske akan wasu abubuwan wanda na san ba lallai bane kun san su” shiru duka suka yi suna saurarenta. Mama ta sauke numfashi sannan ta fara masu nasiha cikin salo na yanda zasu gane me take nufi, duk wani abu mai muhimmanci sai da ta tabbata ta sanar dasu, sannan ta sanya suka yi addu'a a tare kafin ta sallami kowa ya tafi don shiryawa lokacin wajejen ƙarfe 8:00 na safe.

Koda suka fito Maimoon ce ta ja Nana gefe tana kallonta ta ce“ya ake ciki?” Nana ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce“nima ban sani ba Maimoon. Abba ba zai taɓa bari a fasa auren nan ba, kawai yanzu ina tsoron abin da sir Junaid zai yi ne, domin jiya Aunty Zahra ta ce min komai ya shige ita”

“komai ya shige ta ce?”

Nana ta gyaɗa kanta. Shiru Maimoon ta yi tana mamaki can kuma ta ce“to ta baki hotunan?” girgiza kai Nana ta yi ta ce“a'a suna hannunta, so nake idan komai ya lafa sai naje na amsa na hada dana wajena na ƙona”

Maimoon ta buɗe baki zata yi magana kenan ta hangi su Aunty Khadijah suna tawowa, Siyama ce ke biye da ita sai Safeena da Amal, kowaccen su ta ci uwar kwalliya kamar bikin gidansu ake. Ta gaban su Nana suka zo suka shige, Maimoon ta taɓe baki sannan ta ce

“gayyar tsiya”

Ɗan murmushi Nana ta yi ta ce“ke ina ruwanki dasu?”

“to banda neman magana uban me ya kawosu gidan mu? Har su ci wata kwalliya”

Nana ta girgiza kanta tana kawar da zancen ta ce“ke ni ƙirjina ciwo yake bari na tafi na kwanta kafin karfe 9 ta yi, Khadijah ta ce min da wuri zata tawo”

“Zuwa zata yi?”

Gyaɗa mata kai Nana ta yi, Maimoon ta ce“Khadijah bala'i ta zo mu sha dariya”

Nana ta ɗan yi shiru tana ƙarewa compound ɗin gidan kallo can kuma ta ce“sai an jima”

“ok. Duk yanda ake ciki ki faɗa min ko a waya ne”

Toh kawai Nana ta ce sannan ta saketa ta nufi hanyar apartment ɗinsu, Itama Maimoon juyawa ta yi ta nufi nasu apartment ɗin. Safwan ya sauke wani zazzafan numfashi sannan ya juya ya bar wajen bayan ya gama kallonsu. Koda ya shiga gida sama ya shige ya zauna a gefen gadonsa yana tunanin mafita. Tabbas idan ya ce ya fasa auren Nana a yau to komai zai zo masa da sauki, kuma zai samu damar auren Siyama. to amma ta ina zai fara fitar da wadannan hotunan nata? Ya girgiza kansa a fili ya ce

“No i can't! Ba zan iya ba wallahi”

Ya ƙare maganar yana kawar da tunanin daga ransa.

****
Around 9am Zahra ta shiga sakkowa daga saman hannunta riƙe da Noor wadda aka mata kwalliya da wata doguwar riga ta atampa Holland ɗinkin t-boubou wanda yasha aiki, ɗinkin ya mugun yi maga mata kyau kamar ba ƙaramar yarinya ba. Zahra kuwa sanye take da wani ubansu lace ash colour ɗinkin doguwar riga yaji stones sai kyalli yake, ta yi yar simple make-up a fuskarta wadda ta ƙara mata kyau. Safeena na murmushi ta ce“woww Aunty wallahi kin yi kyau kamar kece amaryar”

Murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta zauna kan sofa tana cewa“ban san sharri Safeena”

“Ai ba sharri ta miki ba wallahi kin yi kyau”

Amal ta yi maganar itama tana murmushi, kallonsu Zahra ta yi sai kuma ta gyaɗa kanta irin ta jin nan ta ce“tofa ai shikenan” daga haka ta kalli Aunty Khadijah ta ce“har na fara tunanin kiran ki” Aunty Khadijah na taunar cew gum wanda ya zame mata dabi'a ta ce

“wallahi mun biya ta wajen Kaddu ne na amshi saƙo shiyasa ki ka ga mun daɗe. Hope dai komai na tafiya dai dai?” jinjina kai Zahra ta yi tana kallon Noor ta ce“eh in sha Allah komai zai tafi kamar yanda muka tsara”

“Ummi zan tafi wajen Hajiya”

Noor ta yi maganar tana wasa da ɗankwalin dake hannunta, Zahra taja hancinta ta ce“ba zaki jira mu tafi tare ba?” maƙale kafaɗa ta yi, ta ce“to je ki Allah ya tsare” tsalle Noor ta yi sannan ta fice daga parlon da gudu.

Miƙewa Siyama ta yi tana danna wayar hannunta ta ce“ina zuwa”

“Ina zaki je Siyama?”

Aunty Khadijah ta tambayeta. Juyowa ta yi tana kallonta ta ce“Safwan ke kirana yana waje”

Jawo hannunta Aunty Khadijah ta yi ta zaunar da ita sannan ta buɗe jakar hannunta tana ƙoƙarin zaro abu ta ce

“ke wace irin banza ce ne? Ba sai ki faɗa min ba, ko kin manta?”

Ta ƙare maganar tana fito da kwallin ta miƙo mata, amsa Siyama ta yi sannan ta buɗe tana ƙoƙarin sakawa ta ce“to bana manta ba, kin san...” maganar ta maƙale saboda waya irin azaba da taji ta ziyarci ƙwaƙwalwarta, ta saki kwallin sannan ta miƙe tsaye tana fashewa da ihu ta ce

“wayoooo Allah na na shiga ukuna Mommy, idona na shiga uku” tashi Aunty Khadijah ta yi ta riƙeta tana faɗin “meya samu idanun”

“barkono, wallahi barkono ne a ciki wayyo idona, na shiga uku na makance Mom”

Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, sai murza idanun take da duka hannayenta biyu. Gaba ɗaya rikicewa suka yi, suka dinga yi mata sannu ana zuba mata ruwa, Safeena ce kawai zaune tana dariya ƙasa-ƙasa dan ita daɗi taji da hakan ta kasance. Kusan mintuna 15 kafin ta iya buɗe idanun, amma sun kumbura sun ji jajur dasu. Ta miƙe kamar me cutar makanta tana dafa gefen kujera ta ce“wallahi Mom bana gani”

Ta ƙare maganar tana sake gwale idanun nata, Zahra ce ta riƙe hannunta ta ce“wai duk bakya ganinmu?” sai dai ta gwalalo idanun sannan ta ce“ina ganinki kaɗan-kaɗan” dariya ce ta kusa kama Zahra amma ta dake ta ce“to za ki iya zuwa wajen Safwan ɗin?” kamar ƙaramar yarinya ta gyaɗa kanta ta ce“eh zan iya, Mom ara min glasses ɗin ki” tsaki Aunty Khadijah ta yi tana nuna ta da hannu ta ce

“Ji banza, to uban me zai gani idan idanun na cikin glasses?”

Siyama ta yi shiru sai kuma ta juya ta nufi hanyar waje jin wayar na ringing.

A can wani garden na bayan estate ɗin ta samu Safwan tsaye yana jiranta, sanye yake da jallabiya baka a jikinsa, ya dinga kallonta har ta ƙaraso wajen. Murmushi Siyama ta sakar masa sannan ta ce

“Ina kwana?”

Kasa dauke idanunsa ya yi daga cikin nata sai murmushi da ya yi ya ce“lafiya kalau my love kin zo ashe?”

Tana wasa da fingers ɗinta ta ce“Eh ba dole na zo aurenka ba”

Haɗe rai Safwan ya yi ya ce“aurena kuma?”
Chapter 52 · 0% Book details