Sashe 8
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana ta faɗa tana janyo wayar Hameeda dake ƙasan pillow. Hoton Sultan ne akan screen ɗinta, yana sanye da kayan likitoci a airport ya yi murmushi, iyaka haɗuwa da kyau hoton ya haɗu. Nana ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, Maimoon ce ta lura ta taɓa ta tana cewa "what are you looking ne?" saurin ɗauke kanta tayi tana ɗan murmushi ta ce"hoton masoyin naki ki ka saka a screen?" Ta ƙare maganar tana kallon Hameeda.
Fizge wayarta ta yi tana harararta ta ce"ina ruwanki da wayata?" dariya Nana ta yi tana kallonta ta ce"haba dai daga naga hoto? Maimoon ki faɗawa Yaya Sultan wallahi Hameeda na ƙaunarsa"
Maimoon ta yi murmushi tana leƙa wayar Hameedan kafin ta ce"ikon Allah wayyo love! Nana kin ga wata ƙauna" tuntsirewa suka yi da dariya, Hameeda ta yi shiru tana kallonsu fuskarta a haɗe kamar ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru, ita dai ta ci gaba da buɗe wayar Nana duk da yanda take jin wani iri a ranta. Da kanta ta haɗa mata komai dan har da sim card a ciki, ta sai ta mata icloud sannan ta tura mata duk pictures da videos nasu, sai wajen 9:20pm sannan suka bar gidan kowa ya nufi hanyar gidansu. Koda taje gida bata ga kowa a parlon ba, dan haka ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar, ajiye wayar ta yi a gaban drawer sannan ta shige toilet. Tana fitowa daga wanka ta shirya a gurguje sannan ta nufi kan gado ta kwanta tana riƙe da wayarta, kalle-kallen hotunan ta dinga yi har wajen goma saura, sannan ta shiga WhatsApp ɗin da Hameeda ta buɗe mata. Hira ta ɗan yi da few friends nata ana ta yaushe rabo, sun daɗe suna magana da Khadijah kafin ta fara jin bacci dan ta saba da wuri take kwanciya. Dan haka suka yi sallama ta kashe datar ta ajiye wayar gefen side drawer sannan ta kwanta abin ta..
Washegari ya kasance juma'a ce dan haka bata tashi da wuri ba, around 9 na safe ta fito parlon hannunta riƙe da wayarta tana dannawa tana murmushi. Abba ne zaune a parlon sai Sultan da shigowarsa kenan bayan kiran da Abban ya yi masa, sam bata lura dasu ba, dan hankalinta gaba ɗaya na kan wayarta saboda hirar da suke da Khadijah. Amma ta fito daga kitchen hannunta riƙe da ɗan madaidaicin tray me ɗauke da kayan tea, kallonta ta dinga yi har ta ajiye tray ɗin sannan ta kalleta ta ce"Nana!"
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli Amman sai kuma ta ce"morning Amma"
"Baki da kayan kasawa ne?"
Amma ta yi tambayar, kallon kayan jikinta ta yi wata armless vest ce a jikinta sai wando wanda bai shige gwuiwarta ba, masu kala ɗaya, kanta ko ɗankwali babu dogayen kitson kalbar ya sakko kan kafaɗunta.
"Tambayarki nake"
Murya a ɗan shaƙe ta ce"a..ai daman yanzu zan sauya kaya"
Harararta Amma ta yi sannan ta nufi hanyar kitchen abinta, tura baki ta yi tana shirin komawa ɗakin Abba ya kira sunanta, dawowa ta yi ta ƙarasa parlon tana kallonsa ta ce"morning Abbana" murmushi ya sakar mata yana jan hannunta ya ce"morning daughter kin tashi lpy?" Sai da ta zauna a kusada shi sannan ta ce"Alhamdulillah, jiya kwana nayi ina tunanin wayata Abba" ya girgiza kansa jin zata fara shirmen ya ce"baki ga yayanki ba?" Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalleshi, zaune yake kan sofa sanye da sport wear, ta ɗan tura baki murya can ƙasa ta ce"morning Ya Sultan" babu yabo babu fallasa ya ce"morning ykk?"
"Alhamdulillah"
Ta faɗa tana mai da Idanunta kan Abba ta ce"Abba dan Allah zan je gidan Aunty Ramlah an jima" shiru Abba ya yi yana kallonta can kuma ya ce"har kin ji sauƙi ne?" saurin gyaɗa masa kai ta yi ta ce"Eh naji sauƙi Alhamdulillah" numfasawa ya yi kana ya ce"shikenan Allah ya kaimu" murmushi ta yi tana kallonsa ta ce"Amin thank you Abba" murmushin shima ya yi sannan ya ce"ki shirya idan Sultan zai fita sai ya yi dropping ɗinki" da sauri ta kalleshi lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, murya a sanyaye ta ce"Abba ba kai zaka kai ni ba?" jan kumatunta ya yi ya ce"i have alot to do Nana, kuma kin ga next week zan je Abuja dole nayi covering abubuwan da ke gabana" langwaɓar da kai ta yi ta ce"ayyah to Abba kawai sai na hau napep, na hutar da Yaya" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a Sultan zai tafi dake"
Tura baki ta yi ta ce"amma Abba..."
"Nana!"
Ya kirata a ɗan tsawace, sunkuyar da kanta ta yi sanin halinsa ta ce"I'm sorry" fuska a haɗe kamar ba shi ba ya ce"tashi ki tafi" bata sake cewa komai ba gudun kada ya hanata ta tashi ta nufi ɗakinta a sanyaye..sai da ta bar wajen sannan ya kalli Sultan ya ce"dan Allah kar ka bari ta tafi ita kaɗai" murmushi ya yi ya ce"in sha Allah Abba" okay Abba ya ce sannan Sultan ya mike dai-dai nan Amma ta fito daga kitchen riƙe da wani tray, ganin yana shirin tafiya ya sanya ta ce"a'a kai what do you mean?" Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi y ce"tafiya zan yi Amma" harararsa ta yi ta ce" zauna ka yi breakfast my friend!" Ganin yanda ta haɗe rai babu alamar wasa ya sanya ya koma ya zauna ba dan yaso ba, ta yi serving ɗin su shi da Abba suka yi breakfast ɗin..
Tun da ta koma ɗaki take kwance tana yan matan hawaye, koda wasa bata son bin sa, to amma kuma tana son taje gidan Aunty Ramlah ko dan alƙawarin da ta yiwa Junaid, haka ta dinga tunane-tunanenta har wajen ƙarfe 11 na safe, sannan ta tashi ta nufi toilet, wanka ta yi ta shirya cikin wata atampa glitter mai coffee and pink, ɗinkin t-boubou da straight skirt, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya wanda ya yi mata kyau sosai atampar ta haskata sosai. Kallon kanta ta yi a madubi sai kuma ta dauki eye pencil ta yi zagayen baki dashi, sannan ta saka a idonta ta shafa lip gloss nan take ta zama wata babbar mace mai aji da kyau, pink ɗin dan kunne da sarka ta saka sannan ta yafa coffee ɗin mayafi, ta dauki handbag coffee da takalmi golden ta saka. Sosai ta yi kyau abin ta kamar sabuwar amarya, ta ɗauki wayarta sannan ta fito parlon lokacin 12 na rana ta kawo kai, zaune ta sami Amma tana karatun Alkur'ani, tana ganinta ta rufe qur'anin kana ta ce"tun yanzu zaki tafi?" gyada mata kai ta yi ta ce"Eh haka Abba ya ce da wuri zai yi dropping ɗina, idan ya dawo sai ya biya ya ɗaukoni" Amma ta ce"to ki gaisheda Ramlam kuma kar ki kai dare" to kawai ta ce sannan ta nufi waje da sauri.
A compound ɗin ta iske Maimoon tana watering flowers tana ganinta ta ajiye butar tana murmushi ta ce"Hajiya Nana duniyar ƙawa, ina kuma zaki je haka?" She just roll her eyes sai kuma ta ce"gidan Aunty Ramlah zan je" Maimoon ta dinga kallonta sai kuma ta ce a hankali "wajen sir Junaid zaki je?" gyaɗa mata kai ta yi cikin raɗa ta ce"Eh zai zo can sai mu haɗu" Maimoon ta girgiza kanta ta ce"Nana baki tsoron abin da zai je ya dawo?" Taɓe baki ta yi ta ce"ni babu abin da nake tsoro in dai zan haɗu da sir Junaid ai shikenan" ƙarar buɗe ƙofar da suka ji shi ya hanata magana, a tare suka juya suna kallon wajen, Sultan ne ya fito, yana sanye da wani yadi mai shara-shara ɗinkin riga da wando, ya ɗora hula akansa idanunsa maƙale cikin shade glasses. Daga ganshi kaga rich and classic guy, ya ƙaraso wajen cikin takunsa na isa. Nana ta kalli Maimoon sai kuma ta ce"sai na dawo"
"Dashi zaku tafi?" Ta gyada mata kai. Fuska a haɗe kamar koda yaushe ya ce"sai nace ki zo mu tafi?" tura baki ta yi sannan ta yi gaba, ya bita da harara sai kuma ya yi gaba shima yana amsa addu'ar Maimoon..
Har suka fita daga cikin estate ɗin babu wanda ya ce uffan, ganin ya ɗauki hanya ya sanya ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa, murya a sanyaye ta ce"Yaya ina motar to? Nifa nagaji"
Hannunta ya riƙe cikin nasa ba tare da ya kalleta ba ya ce"mota, wace motar? Ai a ƙafa zamu tafi!”
08106608363
Nanameera..*🌹 NAANAH 🌹*
Page 6...
Cak ta tsaya tana kallonsa da mamaki, shi kuwa ya haɗe ransa ya ce"mene haka?" kwantar da murya ta yi ta ce"Haba Ya Sultan sai ƙafata ta yi ciwo ai, dan Allah ka ɗauko motar ka ko ta tsaida mana napep" Sultan ya zare glasses ɗin idanunsa yana kallonta fuska a haɗe ya ce"ni nace ki lalata min mota da ƙazanta? To ba'a kawon daga car wash ba, saboda haka let's go malama!" Muryarta na rawa ta ce"amma Yaya..."
"Shhhhhh!"
Sultan ya faɗa bayan ya ɗora hannunsa bisa bakinsa, kasa cewa komai ta yi amma tuni idanunta suka sauya kala, ya riƙe hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka zo babban titi bai ce komai ba, ita dai binsa kawai take duk da yanda take jin ƙafafunta kamar zasu ɓalle. Ganin suna shirin tsallaka titi ya sanya ta rikeshi da ɗaya hannun nata, juyowa ya yi yana kallonta sai kuma ya ce"lafiya dai?"