← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 125

Sashe 3

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tafiya ta dinga yi tana yan waƙoƙinta na turanci, kowane gida a rufe yake, kai tsaye kuma gidan Hajiya Babba ta nufa. Babban duplex ne dan yafi kowane gida girma a cikin estate ɗin, ta dinga kallon gidan fuskarta ɗauke da annuri dan rabonta da Hajiya Babba wata shida kenan, ta ƙarasa da sauri ta murɗa handle ɗin ƙofar, karo suka ci, ta yi baya tana dafe goshinta. Tsayawa ya yi a jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta. Ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki, hannunsa ya sanya kamar zai taɓa ta, ta sake ja da baya. Harararta ya yi kana ya ce"gashi zan cire miki" hannunta ta shafa a gefen fuskarta taji gashinta a waje, da sauri ta mayar dashi cikin ɗankwalin ba tare da ta kalleshi ba ta ce"zan shige" ɗan murmushi Sultan ya yi sannan ya ce"to shige malama" daga haka ya koma ciki. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi sannan ta shiga cikin parlon.

Wani irin ihu ta saki data hango Hajiya Babba zaune kan sofa, ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana dariya ta ce"Hajiya Babba, nayi missing ɗinki" murmushi Hajiya Khadijah ta yi ta ce"takwara so ki ke sai kin ƙarasani?" Ɗagata Nana ta yi ta zauna gefenta tana cewa"Ni na isa Hajiya Babbarmu mai Makkah da Madina" Hajiya Babba ta dinga kallonta tana murmushi ta ce"shikenan an gama makarantar" Nana ta gyaɗa kanta tana kwance ɗankwalin kanta ta ce"Eh mana, mun zama manya" Dariya irin ta manya Hajiya Babba ta yi sannan ta ce"ai yanzu yan'uwan naki suka shiga ciki"

"Su Maimoon?"

Nana ta tambaya tana miƙewa tsaye, jinjina mata kai Hajiya Babba ta yi ta ce"eh su mana, kitchen suka shiga" bata sake cewa komai ba ta nufi hanyar kitchen ɗin da sauri. Tsaye ta samesu suna magana ƙasa-ƙasa, ta dinga kallonsu sai kuma ta ce"ashe kuna nan" Amrah ce ta ce"da mun yi niyyar mu zo apartment ɗinku idan muka bar nan ashe zaki zo kema" ɗan taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce"to hirar me kuke?" Maimoon ce ta ƙarasa ta jawota murya can ƙasa ta ce"hirar Yaya Sultan muke, Hameeda ce tace wai tana mugun son shi, shi ne muke addu'a Allah yasa Hajiya Babba ta ce ya aureta, tun da daman duk ta girmemu kuma ta fimu hankali" Nana ta dinga kallonsu amma bata ce komai ba, Hameeda da ke tsaye tun ɗazu bata ce komai ba ta ƙaraso gabanta, hannunta ta kama cikin sanyin murya ta ce"Nana ina son Yaya Sultan tun ba yau ba, duk da naga shi bai fuskanci hakan ba, amma wallahi duk sanda na ganshi ji nake zuciya kamar zata fito. Ina son shi, shi nake burin na aura" ita dai Nana kallonta kawai take tana ayyana wawta irin tata, Ganin bata ce komai ba ya sanya Hameeda ta sauke ajiyar zuciya ta ce"ba zaki taimakeni bane Nana?" Numfasawa Nana ta yi still looking at her ta ce"amma kin yi ganganci Hameeda, akan me zaki fara jin kina sonsa bayan kina da tabbacin ba lallai bane ki same shi? Kin san a gidan nan babu ruwansu da wanda ki ke so, wanda ya dace dake kawai za'a baki. Akan me ki ka fara son yaya Sultan?"

Hameeda ta dinga kallonta sai kuma ta juya ta fara tafiya toward direction ɗin window muryarta na rawa ta fara faɗin"kaddara! Kaddara ce Nana, ita soyyaya babu ruwanta da wanda ya dace, ina son yaya Sultan tun bansan kaina ba, wallahi ina jin idan bashi na aura ba bazan taɓa iya biyayyar aure ba. Nana inason Yaya Sultan fiye da yanda ki ke son Sir Junaid!"

With so much surprised Nana ke kallonta, Ba ita kaɗai ba har da sauran dake tsaye. Ji tayi ƙafafunta suna neman gagara ɗaukanta, ta dinga kallon bayan Hameeda zuciyarta na ɗagawa. Bata ce komai ba ta juya ta fice daga kitchen ɗin gaba ɗaya.

A parlon ta samu Hajiya Babba tana ganinta ta ce"Allah dai yasa ba ɓarna ku kemin a kitchen ba" ko amsa Nana bata samu damar bata ba ta fice daga parlon da sauri kamar zata tashi sama, Hajiya ta dinga bin ta da kallo sai kuma ta taɓe baki sanin halinta ta ce"abun ne ya motsa kenan".

Bayan fitar ta Maimoon ta ƙarasa gaban Hameeda ta dafata cike da damuwa ta ce"meyasa zaki ce mata haka? kin san batasan ana dawo da maganar sir Junaid ko?" Juyowa ta yi tana goge hawayen fuskarta ta ce"shine zata gane halin da nake ciki, kamar yanda Nana ke son Junaid kuma take da yaƙinin ba zata sameshi ba haka nima nakeson yayanki Maimoon, Dan Allah idan har kina da dama ki taimakeni na aureshi" ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Rungumeta Maimoon ta yi cikin shessheƙar kuka itama ta ce"zan so ace ina da wannan damar wallahi da tuni na saka kin aureshi, amma ban isa nace ga abin da zai faru ba, Allah ne kawai yasan ƙaddarar kowane ɗayanmu, kuma ba zamu iya guje mata ba, kawai ki yi addu'a" Hameeda ta dinga gyaɗa mata kai ba dan ta gamsu da maganganun nata ba.

****Koda ta shiga parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta wuce ɗakinta da sauri ta rufe ƙofar, jingina ta yi da jikin ƙofar ta shiga sauke numfashi da sauri da sauri, kafin daga bisani ta fashe da wani irin kuka ta sulale ƙasa kan tiles ta shiga rera kukanta. She wish zata iya ci gaba da zuwa AUN, she wish a ce ita bata kasance ƴa a cikin dangin M-Shuwa ba, da tabbata Sir Junaid shi ne wanda zai zamo miji a gareta, mutumin daya nuna mata ƙauna tun bata san kanta ba, mutumin daya sota saboda Allah ba dan wani abu ko halitta nata ba. Mutumin da take jin bazata iya haƙura da soyyayarsa ba, sai dai ƙaddara ba zata bata ikon rayuwa dashi ba, bata isa ta ce ga wanda take so a cikin gidansu ba, ba za'a taɓa yarda ba! Ba zasu yarda ba!. Nana ta sauke dogon numfashi sannan ta miƙe daya inda take ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali kamar me tsoron wani abu, haka ta dinga tunawa da masoyinta Junaid gami da kewarsa, ta dinga jin kamar ta tashi ta koma AUN suyi rayuwarsu cikin farin ciki. Tana nan kwance tana yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya saceta.

Ƙarfe 7:20pm ya shigo cikin gidan, kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, zaune take kan sallaya tana jan cazbahar hannunta, ya ƙarasa ya zauna bayan ya yi sallama ya yi shiru yana jiranta. Sai da ta kammala laziminta sannan ta juyo tana kallonsa ta ce"Aliyu sai yanzu?" jinjina mata kai ya ce fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce"wallahi Hajiya, na ɗan tsaya ne da wani former friend ɗina" Hajiya Babba ta ce"to bari a kawo maka abinci" girgiza kansa ya yi ya ce"a'a yanzu na dawo sai nayi wanka na shirya nagaji sosai" Hajiya Babba ta gyaɗa kanta kana ta ce"to shikenan nima isha'i zan yi na kwanta yau yaran nan duk sun gaji dani"

"Su Juwaira sun shigo miki ne?"

"Ai yau ba yaran bane yan matan gidan ne suka dawo daga makaranta"

Aliyu ya ce"to ai ni shaf na manta wallahi su Nana danger an dawo gida kenan" Hajiya ta yi murmushi ta ce"ai har ma ta fara halin nata, daga zuwa ɗazu ta yi baƙar zuciya. Ai jira nake gobe ta yi idan Allah ya ara mana rai na kira su Kabiru azo a yi maganar aurensu kowa ya huta!"

Aliyu ya ɗan yi murmushi ya ce"Daga dawowarsu Hajiya da an bari sun ɗan huta ai" Wani kallon sheƙeke ta masa kafin ta ce"hutun me zasu yi Allah na tuba? Kowacce ta huta a gidan mijinta aurar dasu zan yi!"

08106608363
Nanameera✌️*🌹 NAANAH 🌹*

Page 3...

Shiru ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, Hajiya ta ci gaba da fad'in "In sha Allah zuwa gobe zan yiwa su Kabiru magana, azo a san yanda za'a yi, dan bana son akai watan gobe ba'a san matsayar aurensu ba" Aliyu ya jinjina kansa ya ce"To Hajiya Allah ya kaimu" Ta amsa da Amin sannan ta ci gaba da laziminta. Tashi ya yi bai ce mata komai ba ya nufi sama, ta bishi da kallo sai kuma ta taɓe baki.

Ƙarfe 8:20 na dare Amma ta dinga knocking ƙofar, ganin har sannan bata buɗe ba ya sanya taja tsaki da ɗan ƙarfi ta ce"Nana! Nana!"

Sai da ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta saita nutsuwarta a sanyaye ta ce"na'am Amma"

"Ki fito ina jiranki"

To kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta zare hijabin jikinta. Sai da ta ƙarasa gaban mirror ta kalli fuskarta ta tabbatar babu alamun kuka, duk da idanunta sun ɗan kumbura. Ta gyara ɗaurin kanta sannan ta nufi ƙofa ta fita.
Chapter 3 · 0% Book details