← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 125

Sashe 81

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta tawo ta hangeshi tsaye gaban motarsa, da alama dawowarsa kenan. Dan haka ta ƙara saurin da take dan ba son magana take dashi ba, Cikin rashin sa'a idanunsa ya kalli inda take, Kasancewar da wadataccen haske a wajen kuma gari bai gama duhu ba ya sanya ya ganeta, Gaba ta yi ba tare da ta kalli ko inda yake ba. Safwan ya biyo bayanta da sauri yana kiran sunanta, Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Ya karasa gaban nata yana haki saboda saurin da ya yi kasancewar ba lafiya gare shi ba. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen henna har sannan, Safwan ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ce

“Nana na san na aikata kuskure, na karya alƙawarin da nayi miki. Amma dan Allah ina neman afuwarki, ki yafe min, wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni. Na kasa samun abin da nake so, koda yaushe tunanin ki nake, ina tunanin abin da nayi miki. Dan Allah dan Annabi Nana ki yafe min.”

Ya ƙare maganar cikin wani irin sanyin murya. Sosai taji jikinta ya yi sanyi, Duk da riko ta kasance ɗabi'arta amma taji zata iya yafewa Yaya Safwan ɗin, dan haka ta sauke numfashi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce

“Ni na riga da na yafe maka Ya Safwan. Na san duk abin da ya faru ƙaddara ce, kuma ban isa na guje mata ba, dan haka ka daina damuwa akan wannan abun, Ya riga da ya shige har abada.”

Ajiyar zuciya Safwan ya sauke yana jin wani abu na faɗa masa wanda da ya tokare masa a ƙirji, Ya jinjina kansa kafin ya ce“Allah sarki, nagode sosai Nana, Allah ya baku zaman lafiya da Yaya, Ya kaɗe fitina a cikin auren ku. Ya baku zuri'a ta gari.”

“Amin na gode Yaya.”

Ta amsa cikin wani irin yanayi, Ita kanta ta gaza gane abin da hakan ke nufi. Zuciyarta sai bugawa take, sun ɗauki a ƙalla mintina biyu babu wanda ya ce da wani ƙala, can dai Safwan ɗin ya ce“Tom sai da safe Nana, Allah ya bamu alkhairi.”

Kamar jira take ta ce“Amin ya rabbi.”

Daga haka ya matsa mata ta yi gaba.

“Nana!”

Safwan ya sake kiran sunanta, Juyowa ta yi ta kalleshi. Ya tako har gabanta ya ce

“Mantawa nayi zan faɗa miki ki dinga addu'a Nana. Ki riƙe addu'a kin ji” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta ce“Tom in sha Allah Yaya” Murmushi kawai ya yi, Ta dinga kallonsa ganin yanda kamarsa da Uncle Abdusammad ta fito. Ya ce“tom jeki” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta juya ta ci gaba da tafiya, Shima ya koma inda ya bar key ɗin motarsa ya dauka sannan ya nufi cikin gidansa.

****
Gajiya ta yi da jiransa ta yi kwanciyarta akan sofa, nan da nan kuma wani bacci ya ɗauketa. Sai kusan ƙarfe 10:30 na dare ya shigo gidan, Kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa, Ya watsa ruwa ya fito ya koma ƙasa. Kasancewar Zahra ke girki ya sanya ya zauna a ƙasan, Ta kawo masa abinci, fuskarsa a sake suka ci tare. Bayan sun gama wani guard ya shigo hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, A gabansa ya ajiye sannan ya juya ya fice. Abdusammad ya tura mata ɗaya daga cikin ledojin, Karɓa ta yi ta buɗe gasasshiyar kaza ce a ciki guda biyu, Sai ice-cream na roba manya guda biyu. Ta yi murmushi ta ce“to an gode Allah ya ƙara arziki.” da Amin ya amsa sannan ta tashi ta kwashe kaf kayan da suka yi amfani dasu ta kai Kitchen, Koda ta sake dawowa a tsaye ga ganshi ya kalleta ya ce“sai da safe ko.”

Murmushi ta yi duk da yanda take jin babu dad'i ƙasan ranta haka ta daure ta ce“tom Allah ya tashe mu lafiya.” Amin kawai ya ce sannan ya nufi upstairs hannunsa riƙe da ɗaya ledar. Sai da ya yi jim a bakin ƙofar kafin ya murɗa handle ɗin a hankali, Kwance ya hangeta kan sofa ta rufe fuskarta da hannayenta. Sam bai yi tunanin bacci take ba, Dan haka ya ƙarasa ciki ya ajiye ledar hannunsa akan table sannan ya taɓa ta ya ce

“Nana! Nana!”

Kasancewar bata da nauyin bacci ya sanyata buɗe idanunta, Ta tashi zaune tana murza idanun, lokaci ɗaya kuma ta zabura ta sauka daga kan kujerar. Bai ce mata komai ba ya gyara zamansa kan kujerar, Ta koma can nesa dashi ta zauna sannan ta ce“Sannu da zuwa”

“Yauwa!”

Ya ce ba tare da ya kalleta ba. Shiru wajen ya ɗauka, Ta dinga kallon sa ganin yanda ya yake danna wayarsa hankali kwance. Can dai ta miƙe tuna abin da Khadijah ta ce mata, Ta nufi dining area ɗin dake cikin parlon, ta gefen ido ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abin da yake. Ɗaya bayan ɗaya ta kwaso kayan tsaf ta jera akan dining, Bai san sanda ya ajiye wayar hannunsa ba ya dinga kallon ta da mugun mamaki. A gabansa ta tsuguna ta ɗan kalleshi sai kuma ta dauke kanta ta dauko plate ta ce

“Me zan zuba maka?”

Abdusammad da mamaki ya kusa daskarar dashi ya girgiza kansa a sanyaye ya ce“Girki ki ka yi Nana? Wane ya saka ki girki?” Ya jera mata tambayoyin har sannan idanunsa akan ta yana mamakin abun. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta kamar ba ita ba ta ce“Ni ce na dafa maka, ai kai mijina ne kuma ni zan dinga yi maka girki yanzu.” ta yi maganar a shagwaɓe. Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce

“To naji nagode Nana, amma ni yanzu na ƙoshi naci abinci.”

Da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya annurin dake man fuskarta ya ɓace, Ta yi sak tana kallon sa. Kamar ba zata yi magana sai kuma ta ce“Shi ne kaci abincin? To a ina kaci abincin?”

“To ay ban san kin yi girki ba Nana. Zahra ce ta dafa naci a ƙasa”

Da wani irin mamaki take kallon sa, nan da nan hawaye ya cika fuskarta, Ta tashi daga wajen ta koma can ƙarshen parlourn ta silale a ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka. Abdusammad ya dinga kallonta lokaci ɗaya kuma ya tuna abin da ya ce, Ya kai hannunsa ya rufe bakinsa ya ce

“Na jangwalo masifa.”

Ya miƙe yana shirin zuwa wajen da take, Tana ganin haka ta mike tsaye tana wani irin kuka kamar zararriya ta ce

“Ni kada ka zo kusa dani! Kada ka zo inda nake! Tun da ita kake so, Ai daman ita ce matarka. Ni kuma baka sona, Saboda ni ba irin wadda ka ke so ba ce, Shi ne kaje ka ci abincinta bayan kuma kwana na ne, Shi ne kaje ka ci abincinta tun da ita ka ke so...”

Ta kasa ci gaba da maganar saboda kukan da yaci ƙarfinta, Girgiza kansa ya yi yana tsaye a inda yake ya ce“Ba haka bane Nana, ban san kin dafa abinci ba ai, dana sani ba zan ci a wajenta ba. Ke kuma ki ka ce min baki iya girki ba ko..”

“Ai daman saboda haka kaje ka ci a wajenta, saboda ni ƙazanta zan yi maka. Daman ai ita ka ke so, Kuma ita ka ke fara zuwa ka gani, ni kuma babu ruwanka dani. Wallahi ba zan yarda ba!”

Ta ƙare maganar cikin gunjin kuka, Sake yo gaba ya yi a ƙoƙarinsa na son zuwa inda take, Ta daka uban tsalle ta bar wajen da gudu. Bedroom ɗinta ta shige ta garƙame ƙofar da maƙulli, Ya dafe kansa sai kuma ya nufi wajen gudun tashin hankali yasa ya taya a bakin ƙofar muryarsa a sanyaye ya ce

“Look Nana, ba nace miki ban sani ba, Ki buɗe ƙofar ki ji. Ki daina kukan”

Tana tsaye jikin ƙofar sai kukanta take, Jin bata ce komai ba ya sanya shi sake cewa “To shikenan ki buɗe ƙofar zan baki abin daɗi, har kaza na siyo miki kin ji ki buɗe ƙofar”

A hankali ta tsagaita da kukan, Ta matsa daga jikin ƙofar har sannan tana shessheƙar kuka, Jin ta fara yin shiru ya sanya ya ce

“Yauwa buɗe kin ji Nanata, Yar ƙaramar matar uncle ɗinta. Buɗe kin ji”

“Ka miƙo min kazar kawai”

Ya tsinkayi muryarta. Shiru ya yi sai kuma ya ce“to ai kin ga babu window anan, ki buɗe ƙofar sai na miƙo miki na tafi.” Shiru ta yi tana jin kamar ta buɗe ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta ce“to ina kazar?”

“Bari na ɗauko”

Ya ce a hankali. Daga haka ya koma inda ya ajiye ledar kazar ya ɗauko ya dawo bakin ƙofar sannan ya ce

“Gata a hannuna, Buɗe sai ki karɓa.”

A hankali ta zare key ɗin dake jikin ƙofar, ta ɗan buɗe kaɗan ta zuro hannunta na dama ta ce“Bani ga hannuna.” yanda ta yi maganar ya kusa sanya shi tuntsirewa da dariya amma ya dake ya miƙa mata kazar, Tana ƙoƙarin ƙarba ne taji ya jawo hannun nata gaba ɗaya. Ta zunduma ihu jin ya buɗe ƙofar ɗakin duka, Ya shigo ciki har sannan yana rike da hannun nata da kuma ledar kazar, Ƙoƙarin janye nata hannun ta dinga yi, sai dai irin riƙon da ya yiwa Hannun bana wasa bane. Dan haka ta kasa, Da ɗaya hannun nasa ya ɗagata cak bai sauketa ko ina ba sai kan gadon, Ya saki hannunta yana ƙoƙarin zama, Juyawa ta yi tana shirin barin wajen taji ya jawota ta faɗo jikinsa. A hankali ya sanya duk hannayensa biyu ya rungumeta a faffaɗan ƙirjinsa, Nana ta fara ƙoƙarin janye jikinta tana kuka a hankali, Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce

“iyye! Ƴar yarinyar ƙarama zata min wayo. Kin san shekarun dana baki kuwa?”
Chapter 81 · 0% Book details