Sashe 104
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Lafiya dai?”
“A.aaliyu ke kiran ka”
Wayarsa dake hannunta ya kalla sai kuma ya karɓa ya kai kunne, Abdusammad ya yi shiru jin Aliyu bai ce komai ba yasa ya ce
“Buddy kana jina?”
Jan numfashi ya yi yana ƙoƙarin ɓoye kukansa ya ce
“Eh ina ji.”
Wata irin faɗuwar gaba yaji ta ziyarce shi, domin duk abin da ya saka Aliyu kuka to ba ƙaramin abu bane. Hankali a tashe Abdusammad ya ce
“Lafiya? Kukan me ka ke?”
Aliyu Ya girgiza kansa kukan na ƙoƙarin cin ƙarfinsa, Ya kasa koda magana. Tsaki Abdusammad ya yi a ɗan tsawace ya ce
“Malam idan ba zaka faɗa min abin da ya faru ba na kashe wayata”
Maimoon dake gefensa tana kuka ce ta karbi wayar muryarsa na rawa ta ce
“Uncl... uncle Yaya Safwan!”
Wata irin bugawa yaji zuciyarsa ta yi, Da ƙarfi ya ce
“Me ya same shi! Ina Safwan ɗin yake? Jikin nasa ne?”
Maimoon ta girgiza kanta cikin kuka ta ce
“We lost him,Ya mutu Uncle!”
08106608363
Nanameera.
Page 61.
Wani irin abu yaji ya tokare masa a ƙirji, Ya sauke wayar ƙasa har sannan Maimoon bata daina kuka ba. Kallon sa suka dinga yi ganin yan da ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, Nana ta taso ta ƙaraso wajen tana kallon sa.
“Uncle mene ne?”
Ta tambaye shi tana jan hannunsa, Ɗago idanun sa wanda suka rine ya yi ya kalleta lokaci ɗaya hawaye ya kawo kurmin idanun sa, Ya girgiza mata kai murya a sanyaye ya ce“Ya rasu!”
Da sauri Nana ta saki hannunsa, Zahra dake kusa da shi ta ɗago kanta tana kallon sa cike da tashin hankali ta ce“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una! Ya mutu kuma?” Gyaɗa mata kai kawai Ya yi, Nana ta yi dinga kallon sa can kuma ta fara ƙoƙarin barin wajen sai ganinta suka yi a ƙasa Sumammiya.
****
Yola/Nigeria.
Safiyar ranar Alhamis suka sauka a garin, wajejen ƙarfe 8:00 na safe suka ƙaraso cikin estate ɗin. Nana ta dinga kallon compound ɗin wanda yake cike da al'umma, Abdusammad bai sake kallon su ba ya yi gaba abin sa. Zahra kuwa kallon Nana ta dinga yi ganin ita ma ta yi gaba abin ta, Rashin sanin wajen wanda zata ya sanya ta ja hannun Noor suka nufi apartment ɗin su, Nana na shiga ta tarar da Haule zaune kan kujera tana sanye da hijabi sai kuka take kamar ranta zai fita. Maimoon da su Hamida na zaune gefen ta suna kukan suma, A sanyaye Nana ta ƙarasa dan ita har ta yi kukan ta gaji, Ta zauna a ƙasa ba tare da ta cewa kowa komai ba. Suma da idanu kawai suka dinga kallon ta can dai Maimoon ta ce“Nana kun zo?”
“Da gaske ya mutu? Da gaske Yaya Safwan ya rasu? Dan Allah Maimoon ki faɗa min!”
Nana ta yi tambayar hawaye na zubowa akan fuskarta, Maimoon ta rufe fuskarta da Hijabin jikinta tana kuka tana girgiza mata kai, Nana ta kalle ta sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka. Haka suka dinga kuka a wajen babu mai rarrashi dan suma su Amma kukan suke mutuwar Safwan ta girgiza kowa.
Abdusammad kuwa tun da ya zauna kusa da Abba bai ce komai ba, Bai kuma kalli kowa ba, Haka kuma ba kuka yake ba. Sai dai idanun sa sun kaɗa sun yi jajur kamar garwashi. Jijiyoyin kansa duk sun tashi, Ba lallai bane ka ga tashin hankalin da yake ciki. Domin babu alamar hakan akan fuskarsa, Cazbahar dake hannun sa kawai yaje ja a hankali yana motsa bakinsa. Cikin ransa kuwa shi kaɗai ya san abin da yake ji, Duk yanda yake da Safwan ko gawarsa bai samu damar gani ba, Ballantana ya yi masa kallon ƙarshe, rabon ba zasu haɗu ya sanya ya ƙi zuwa duk da yanda ya dinga takura masan.
****
Babu wanda mutuwar Safwan bata daka ba a gidan, Kowa jikinsa ya yi sanyi. Musamman Haule wadda ta kasa dawowa daidai duk da sati biyun da aka ɗauka, Kullum yini take cikin ɗakin Amma tana kuka, wani lokacin Nana ta dinga taya ta, wani lokacin kuma ta rarrasheta. Ta kasa mantawa dashi a ranta, Sam bata yi tunanin rabuwa dashi ba, bata yi tunanin Safwan zai mutu yanzu ba. Ɓangaren Siyama kuwa ita gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta, Babu wanda yake zuwa wajenta, Ko gaisuwa ba'a wani zuwar mata, Sai ɗaiɗaikun mutane idan sun zo suke cewa a kai su wajen matarsa. Ta zama wata abar tausayi da ita, Ta rame ta yi baƙi, Ita kanta bata yi tunanin mutuwa Safwan zai yi ba, Duk da ta san bashi da lafiya sosai daurewa kawai yake amma bata yi tunanin abun zai zamar masa haka ba. Idan ta tuna ita ce wadda ta shafa masa cutar sai taji ta ƙara tsanar kanta, Ko kaɗan ta kasa sukuni, ko abinci bata ci, babu mai rarrashinta. Anty Khadijah ce kawai ke zuwa gidan ta zauna da ita, wani lokacin kuma Amal da Safeena su zo. Zahra kuwa idan ta shigo da safe ta ganta bata sake komawa, Gaba ɗaya ma ba shiga harkar jama'ar gidan take ba. A haka har Sati uku suka shige, Ranar wani Alhamis misalin ƙarfe 4:00 na yamma Anty Khadijah ta buɗe ƙofar parlourn ta shigo, Zahra na zaune kan sofa ta yi yin game a wayarta. Ta kalleta sai kuma ta ajiye wayar a gefe tana cewa
“Au Anty, Ke ce a gidan?”
Anty Khadijah ta ƙaraso ciki ta zauna kusa da ita ta ce“Eh wallahi Zahra ni ce. Daman cewa nayi bari na biyo na duba ki, naje wajen Siyama ne.” Zahra ta ce“Okay Bari na kawo miki ruwa”
Ta miƙe ta shige kitchen, Anty Khadijah ta bita da idanu, After some minutes ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da kayan drinks. Ta ajiye mata a kan table sannan ta koma ta zauna, Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ɗauki ruwa tana ƙoƙarin buɗewa ta ce
“Wai ke ya zaman naku?”
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“Wallahi gashi nan Anty, Babu wani daɗi. Ni dama jira nake komai ya lafa na miki magana, Ya ake ciki da kuɗin da ki ka sa na bayar?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta buɗe jakarta ta zaro wani ƙullin magani a baƙar leda ta miƙo mata tana cewa
“Kin ga wannan shi ne maganin, wallahi idan ki ka yi aiki dashi yanda zan faɗa miki to nan bada jimawa ba sai ya saketa!”
Ɗan zaro idanu Zahra ta yi ta dafe ƙirji ta ce“Saki kuma Anty? Na faɗa miki ba asiri ba kama shi zai yi ba. Wallahi shi ma ba'a zaune yake ba” Tsaki Anty Khadijah ta yi ta ce“Kaji banza, To wane ya ce miki shi za'a yi wa?” Zahra ta yi shiru kamar mai tunani, Can kuma ta ce“To wa za'a yi wa?” Wani murmushi Anty Khadijah ta yi tana juya ledar hannunta ta ce
“Mahaifiyarsa za'a bawa!”
Miƙewa tsaye Zahra ta yi tana kallon ta ta ce“Wai wa ki ke nufi? Hajiya Babba? So ki ke ya sakeni ni?” Wata uwar harara Anty Khadijah ta maka mata kafin ta ce“Ke daɗina dake bakya cin ribar zance, to wane ya ce miki zai sake ki? Ai ke da fita a gidan nan sai dai a mafarki, muddin ki ka yi amfanin da wannan, to wallahi ko a mafarkin ma ba zaki bar gidan nan ba.” Zahra ta dinga kallon ta jiki a sanyaye, Anty Khadijah ta miƙa mata ledar tana cewa“Ba fa wani abun zaki yi ba, kawai a abinci zaki zuba mata, Da zarar ta cinye shikenan! Sai yanda ki ka yi dasu duka” Zahra ta ɗan kalleta sai kuma ta amsa ledar tana kallon ta. Anty Khadijah ta gyara zamanta ta ce“Idan har kin yi yanda na ce to babu wanda ya isa ya raba ki da mijin ki, Ita kanta sai yanda ki ka yi da ita! Kawai a abinci zaki zuba. Ki duba girkin da tafi so ki yi mata, Idan ba haka ba ki ci gaba da zama ran ki na ɓaci a banza” Zahra ta sauke numfashi ta ce“Toh Anty. In sha Allah zan yi, ai abinci ne kawai, zan kai mata” Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Anty Khadijah ta sauke kafin ta ce“To shikenan, Allah ya bada nasara. Ni bari ki ga na je” Ta ƙare maganar tana tashi tsaye. Itama Zahran miƙewa ta yi har sannan maganin na hannunta ta ce“Da wuri haka, da kin bari na gama abincin dare” Girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“A'a ba zan bari ba wallahi. Sauri nake, Wai ina yarinyar ne?”
Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“ai kin san tun da muka zo gidan nan tana apartment ɗin su, bata taɓa kwana anan ba, daga mu sai shi.” Jin jina kai Anty Khadijah ta yi cike da fahimta ta ce“To kin ga idan kin yi komai yanda ya dace sai dai ta yi ta zama a can!” Murmushi Zahra ta yi a sanyaye ta ce“Kai Anty, da wuri haka?”
“Kina ɗauka wasa ne Zahra?”
Girgiza kai ta yi har sannan tana murmushi, Anty Khadijah ta ce“To ki gwada ki ga, wallahi zaki yi mamaki”
“In sha Allah Anty zan yi, gobe goben nan ma”
Zahra ta yi maganar tana kallon ta. Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“To Allah ya kai mu, Sai mun yi waya” Sallama suka sake yi sannan ta fice daga parlon, Zahra ta koma ta zauna tana sauke numfashi.
****
Nana na zaune kusa da Haule wadda ta yi shiru ta yi nisa a cikin tunani aka buɗe ƙofar ɗakin, Atta ce ta shigo hannunta riƙe da wata warmer. Nana ta dinga kallon ta ba tare da ta ce komai ba, A gaban gadon ta zauna tana kallon Haule ta ce
“Zo nan maza ga abinci na kawo miki, Yarinya ki dinga zama a haka? Sai wani abu ya samu ɗan cikin ki? To da me zamu ji? Da rashin uban sa ko kuwa da ke?”