← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 125

Sashe 71

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Eh mana Anty. Yanzu dan Allah kamar Yaya Sultan, ai kin ga bai min girma ba sosai, to amma ji fa uncle, ƙato ne shi fa. Kawai sai a dinga yimin dariya, Kuma har ƴa ce dashi, wallahi tsoho ne, ni saurayi nake so na aura”

Ta sake komawa kan cinyar Ramlah tana kukanta. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi dariya na son kwace mata ta ce

“To ai duk wannan abun dana lissafo shi uncle ɗin naki zai dinga miki. Ba zai bari ki dinga kuka ba, zai kula dake sosai kin ji”

Ɗago kanta ta yi ta ce“To bayan ma har mata ce dashi, kuma ni wallahi bana son kishiya.”

Haɗe rai Aunty Ramlah ta yi ta ce“to ke ina ruwanki da matarsa? Babu abin da ya shafeki da rayuwarta.”

Tura baki ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce“ni Allah bana son zama da kishiya, wallahi sai dai ya saketa!”

Kallon kin zama mahaukaciya Ramlah ta yi mata kafin ta ce“to don't ever, kar ki sake koda wasa ki fadi wannan maganar a gaban wani kin ji abin da nace.?”

Gyaɗa mata kai ta yi, Aunty Ramlah ta sauke numfashi ta ce“ki daina wannan shirmen ki saurari abin da zan faɗa miki kin ji.”

Shiru ta yi kamar gaske, Aunty Ramlah ta kama hannunta na dama cike da kulawa ta ce

“Nana ki daina wannan kukan haka. Kin san dai tun da an riga da an ɗaura auren na babu wanda ya isa ya sa a kwance shi, saboda haka ki kwantar da hankalinki. Babu wata matsala dan ance Abdusammad ne mijin ki, me ake buƙata ne a aure ba zaman lafiya ba? Da soyyayar juna. Na tabbata Abdusammad ba zai ce baya son ki ba, saboda ke ɗin mace ce irin wadda kowane banki ke fatan samu, kina da kyau kina da tarbiyya. Sannan bugu da ƙari kina da ɗabi'u irin wanda maza ke so, Idan har kin kwantar da hankalin ki, to babu yanda za'a yi ya zama na wata. Dole ke zaki kwace shi, musamman daya kasance ke ɗin ƴar uwarsa ce, saɓanin waccan da kawai a wani wajen ya ganta ya aureta. Dole kina da alfarma a wajensa, Sannan idan har bai ji zai iya zama dake ba ba zai taɓa yarda ya aureki ba, kina dai gani babu irin macen da ba'a nuna masa ba a cikin gidan nan a lokacin da zai aure amma sam ya ce babu wadda ta yi masa, babu yanda ba'a yi dashi ba. Amma ke babu wanda ya yi masa dole, shi da kansa ya ce a ɗaura muku aure, ya biya sadaki mai yawa kina ganin ba zaki iya kwace shi daga hannunta ba.?”

Aunty Ramlah ta yi shiru tana kallonta, ganin yanda ta ƙura mata idanu wanda ke nuna tana fahimtar abin da take cewa yasa ta ci gaba da faɗin“Idan har zaki bi abin da zan faɗa miki to tabbas uncle ɗin zai zama naki. Zaki mulki gidan fiye da yanda ki ke tunani, duk da kasancewarsa tsayayyen namiji zaki iya cin galaba a kansa, dan haka ki buɗe kunnunwanki ki ji abin da zan ce miki.”

Ganin bata ce komai ba ya sa Anty Ramlah ta haɗe ranta ta ce“ba magana nake miki ba.?”

A sanyaye ta ce“Ina ji”

Anty Ramlah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yauwa kina ji...”

Around 11am Amma ta shigo ɗakin, zaune ta sameta, Nana na kan cinyarta ta yi shiru. Amma ta ce“Ramlah babu abin da zaku yi lokaci fa na tafiya?”

Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“a'a zamu yi, Nana tashi muje.”

Tura baki ta yi sannan ta tashi zaune tana haɗe-haɗen rai. Anty Ramlah ta sauka daga kan gadon tana kallonta ta ce“taso nace.” kamar zata yi kuka ta ce“to bari nayi wanka.”

Girgiza kai Anty Ramlah ta yi tana jan hannunta ta ce“a'a idan mun je can kya yi” da ɗan mamaki ta ce“Anty to ina zamu je?”

Harararta Anty Ramlah ta yi ta ce“kin tashi ko isata zaki yi da magana?”

Zumɓura baki ta yi sannan ta tashi a hankali, Hijabin dake ajiye kan drawer ɗinta ta ɗauka ko gama zurawa bata yi ba Anty Ramlah taja hannunta suka yi waje. A parlon suka tsaya Amma ta ce“dan Allah Ramlah kar ku dade a zo a isheni.”

Murmushi Ta yi ta ce“To idan ba'a gama ba ai ba zamu dawo ba Yaya.”

Shiru Amma ta yi, can kuma ta sauke numfashi ta ce“to Allah ya tsare hanya.” da Amin ta amsa sannan suka yi waje, suna ƙoƙarin shiga mota, suka ƙaraso compound ɗin, Da idanu Nana ta dinga bin su ganin sun zo inda take yasa ta ɗaga mata hannu. Ita ma Amrahn daga mata hannu tayi tana murmushin, ganin ya kalli inda take yasa ta ɗan sunkuya a sanyaye ta ce

“Ina kwana Yaya.”

Fuska a sake ya amsa mata sannan ya gaisar da aunty Ramlah ta amsa ta ce“Sultan ya gida ya iyalin?” murmushi ya yi ya ce“Alhamdulilah Anty ya kids?”

“Suna nan kalau” ta ce a sake. Jinjina kansa ya yi ya ce“Tam a gaishe min dasu pls” zasu ji ta ce sannan suka yi gaba ita kuma ta buɗe motar ta shiga, a sanyaye Nana ta shiga motar lokaci ɗaya taji ranta ya sake ɓaci. Aunty Ramlah bata ko kalleta ba ta yiwa motar key suka bar Estate.

****
Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Maimoon ta shigo parlon bakinta ɗauke da sallama. Bata samu kowa a ciki ba, kamar ta juya ta fita sai kuma taja ta tsaya tana jiran taga ta inda zata fito, bayan mintinan da basu shige biyar ba Zahra ta fito daga kitchen Saboda kiran wayarta da taji, sai dai ganin Maimoon ya sanyata tsayawa ta ce“Laaa Maimoon ke ce a gidan yau?” babu yabo babu fallasa ta ce“Eh ina yini?”

“Lafiya kalau ya gida?”

Zahra ta amsa mata da fara'arta. Taɓe baki Maimoon ta yi dan ba abin da ya kawota ba kenan ta ce“Daman Atta ke kiranki.” shiru Zahra ta yi da mamaki ta ce“Atta kuma? Meya faru” girgiza kai Maimoon ta yi cike da rainin hankali ta ce“A'a ni ban sani ba gaskiya sai dai idan kin je kya ji. amma kuma kamar akan maganar tariyar amaryar da za'a yi an jima ne.” Maimoon ta ƙare maganar tana sakin wani kyakkyawan murmushi na zallar rainin hankali, Kallonta kawai Zahra ke yi can kuma ta danne zuciyarta ta ce“Tom gani nan in sha Allah.”

“Yauwa da yafi dai.”

Ta ce tana juyawa, sai da taga ta fice daga ɗakin sannan ta zauna kan sofa hawayen da take ta maƙalewa suka gangaro kan fuskarta. Wani irin zafi take ji a zuciyarta, kenan tun kafin ta shigo sun fara nuna mata irin abin da zasu yi, kenan zata zama shara a cikin gidan, Ta ɗora kanta bisa cinyarta tana fashewa da kuka. Ta dade a wajen tana kukan ganin ba zai kai mata ba ya sanya ta ɗago kanta ta ɗauki wayarta da ke kan table ta danna numbern Aunty Khadijah. Sai da kusa katsewa sannan ta ɗaga. Zahra ta kasa cewa komai sai kuka da take a hankali, Aunty Khadijah da ke zaune gaban motar wani Alhaji ta ce

“Lafiya dai Zahra?”

Cikin kuka ta ce“Aunty basa sona. Mutuwa zan yi wallahi, ƙirjina zafi yake min” cike da rashin fahimta ta ce“ban gane ba Zahra, me ya faru? Su wane basa sonki”

“Yan gidan nan mana, basa son zama dani. Wai an jima zata tare, ya zan yi Anty?”

Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“ba dai bakya jin shawara ba Zahra? Yanzu kin ga Siyama na samun matsala dasu tun da taje? To ya ma za'a yi ta samu matsala bayan mun yi maganin matsalar, amma ke sam kin ƙi yarda, kin biyewa Umma da bata san me duniya ke ciki ba. Dan haka kuka yanzu ki ka fara shi wallahi, nan gaba ma sai sun koro ki daga cikin gidan baki ɗaya.”

Zahra ta girgiza kanta tana kuka ta ce“A'a wallahi, in sha Allah ba zan bar gidan nan ba. Ba zan rabu da mijina ba, ki faɗa min me zan yi Anty? Wallahi zan yi koma mene ne muddin zan zauna lafiya a cikin gidan nan, dan Allah ki faɗa min me zan yi.?”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 44.

Jinjina kai Aunty Khadijah ta yi sannan ta ce“alright we should talk later.” daga haka ta katse wayar saboda mutumin da yake gabanta. Zahra ta sauke numfashi ta sanya hannunta ta goge idanunta sannan ta tashi ta haye sama, Mayafi kawai ta dauko sannan ta dawo ƙasan, ta fito daga parlon jiki a sanyaye ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba.

****
Anty Ramlah ce tsaye gabanta. Ta kai mata duka tana cewa“ke Nana tashi mu tafi!” a ɗan firgice ta buɗe idanunta sai kuma ta tura baki, Ta sanya hannunta wanda yaji red henna gaba da baya. Ya yi wani irin kyau kamar a fatar hannun aka halicce shi. Ta murza idanunta a shagwaɓe ta ce“To Anty yanzu zamu tafi?” Gyaɗa mata kai ta yi ta ce“to ba an gama komai ba?” Sai a sannan ta kai hannunta kanta, jin yanda ya yi wani irin santsi ya sanya ta miƙe tsaye tana kallon console mirror ɗin da ke wajen. Juyowa ta yi tana washe baki ta ce“Anty ji kaina ya yi kyau.” murmushi Anty Ramlah ta yi kafin ta ce“Eh mana gashinan kinyi kyau abin ki, da an ganki an ga amarya.” sunkuyar da kanta ta yi tana sosa kai, Anty Ramlah ta sake murmushi sannan ta ce“oyaa zo mu tafi Amma ta fara kira.”

To kawai ta ce sannan ta ɗauki hijabinta ta zura, Anty Ramlah ta ƙarasa cashier ɗin wajen ta biya kudaden sannan suka fita daga shagon. Bayan sun shiga mota sun fara tafiya Anty Ramlah ta ce“Nana zamu je na amso saƙo nan Jalo”
Chapter 71 · 0% Book details