← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 125

Sashe 92

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba zaka taɓa cewa da ita yake ba, dan ko buɗe idanunta bata yi ba. Sai shessheƙar kuka da take a hankali, Murmushi ya yi sai kuma ya sanya hannunsa ɗaya ya ɗagota. Kamar jira take ta fashe da kuka tana ƙoƙarin janye hannunsa, sai dai rashin gwarin jikinta ya sanya ta gagara yin hakan. Ya zaunar da ita akan cinyarsa yana kallon ta ya ce

“ina miki magana kina share ni?”

Ɗauke kanta ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikinsa, Ya riƙe gam ya ɗago fuskarta ya ce“me aka miki?” bata san sanda ta sake fashewa da kuka ba, Ta fara dukansa tana cewa

“Ni ka rabu dani, ni bana so kana taɓa ni. Wallahi sai na faɗawa Ammata, ni gidanmu zan tafi...”

Ban da murmushi babu abin da yake, Ya riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa ya ce

“Yaushe zaki tafi gidan?”

Kallon sa ta yi, ganin yanda yake murmushi ya sanyata ɗauke kanta tana sake rushewa da wani kukan, Janyo fuskarta ya sake yi ya rungumeta ya ce

“Shikenan ya isa haka. Ki yi shiru kin ji”

“ka mayar dani gida”

Ta ce tana kuka, Shafa kanta kawai ya yi ya ce“tom zan mai da ke. Zo ki ci abinci”

“A'a ni ba zan ci ba ɗin.”

Ɗago fuskarta ya yi ya ce“tashi nace, je ki wanke bakinki ki zo ki ci abinci” sake maƙale kafaɗa ta yi tana shirin yin magana taji ya daka mata tsawa, Da sauri ta sauka daga jikinsa ta nufi toilet ɗin tana kuka. Sai da ta tsaya a banɗakin ta gama kukanta sannan ta wanko bakin ta fito,Ta zauna a gefe ta sunkuyar da kanta. Mug ɗin tea ɗin ya miƙo mata ya ce

“ki shanye tas kar ki rage min ko kaɗan.”

Kallon tea ɗin ta dinga yi fuska a yatsine, can dai ta kai shayin bakinta ta yi saurin ɗaukewa tana yarfe hannu ta ce

“zafi fa uncle.”

Kallon ta ya yi, sai kuma ya miƙa mata hannu, ta bashi shayin tana kallon sa. Doke hannunta ya yi ya jawota jikinsa ya karbi mug ɗin, bakinsa ya sa ya ɗan hura mata shayin sai kuma ya miƙa mata bakinta ya ce

“Haaa.”

Buɗe bakin ta yi ya fara bata, ko rabi bata sha ba ta ɗauke kanta ta ce“ni Allah na ƙoshi.”

“shanye ko na mareki”

Kamar zata yi kuka ta ce“na ƙoshi wallahi.” Ya ajiye mug ɗin akan tray ɗin sannan ya janyo plate ɗin soyayyen dankalin, Da kansa ya dinga bata shi ma har ta kusa cinyewa sannan ta ce“na ƙoshi.” bai ce komai ba ya ajiye plate ɗin yana kallonta ya ce“zo ki kwanta to.”

Kamar jira take ta rarrafa kan gadon ta yi kwanciyarta tana lumshe idanu. Ya ɗan kalleta sai kuma ya tashi ya fita hannunsa riƙe da tray ɗin, after 2mins ya dawo hannunsa riƙe da syringe, Ya zauna gefenta bayan ya ɓoye syringe ɗin a bayansa ya ce“dawo nan ki kwanta.” ya yi maganar yana nuna mata cinyarsa, Son jiki irin nata ya sanya ta taso ta ɗora kanta akan ƙirjinsa ta zagaye hannunta a bayansa ta rufe idanunta. Shiru ya yi yana kallon ta, sai da yaga ta fara bacci sannan ya zaro syringe ɗin, Ya sauke wandon jikinta ya saita allurar ya tsira mata. Wata irin ƙandarewa ta yi tana sakin kuka, Ta gasa masa cizo a ƙirji tana kuka. Murmushi kawai ya yi ya ɗauke syringe ɗin yana shafa kanta ya ce

“Sorry yi baccin ki.”

Bata ce komai ba, sai kukanta da take ƙasa-ƙasa dalilin baccin daya fara ɗaukanta, Shima ya yi shiru idanunsa a lumshe har bacci ya ɗauketa. Saukar numfashinta daya fara ji ya sanya ya ɗan kalleta, bacci take hannunta ɗaya a baki ta kwaɓe fuska, Ya girgiza kansa ya janyeta ya kwantar kan gadon sannan ya tashi ya rufeta da duvet. Ganin tana motsi ya sanya ya koma ya zauna, ta yi juyi sannan ta ci gaba da baccinta. Sauke numfashi ya yi sannan ya rage gudun ac ya juya ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana zuwa ya yi kwanciyarsa dan shima baccin yake ji.

****
It's been a months da zuwansu New York, gaba ɗaya aiki yayi masa yawa. Kusan kullum baya shigowa gidan sai dare sosai, shiyasa basa wani ganinsa idan ba asuba ce ta yi ba. Ɓangaren Zahra abun nata kullum gaba yake, yau a zauna lafiya gobe ta tada balli. Shi dai baya biye mata, dan bama shi da lokacin tsayawa faɗa da ita. Nana ce kawai ki biye mata idan ta dawo daga makaranta baya nan su yi ta tashin hankali, Yau ma kamar kullum tana zaune a main parlourn tana chatting, Abdusammad ya sauko daga ƙasa yana kallon ta ya ce“baki shirya ba?” miƙewa ta yi tana kallon sa ta ce“kai nake jira fa.” Ya kalli Noor dake zaune kusa da ita ta yi shiru ya ce“zo” ta shi ta yi ta koma wajensa ta tsaya ya ɗauketa ya ce“me ki ke so?”

“Abbie chocolate zan ɗauko nida Afeefa da Sumshi”

Ya ɗan ware idanunsa yana murmushi ya ce“iyye iya su kaɗai zaki ɗaukowa?” ta gyaɗa masa kai tana kwanciya a jikinsa. Bai sake ce mata komai ba ya kalli Nana wadda ke sakkowa daga sama hannunta rike da jakarta. Ƙarasowa ta yi ta tsaya tana rike da wayarta ta ce

“uncle na gama.”

Okay ya ce sannan ya kalli Zahra ya ce“Madam muje.” Fuskarta a haɗe ta ce“ita kuma ina zata je?” ta yi maganar tana nuna Nana, Ɗauke kai Nana ta yi dan bata da lokacinta. Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“ina zamu je dai zaki ce”

“To ai naga dai yau ba kwananta bane ballantana ta bika unguwa. Dan Allah wallahi ba zata je ba!”

Zahra ta yi maganar tana zabgawa Nana harara. Kafin ya yi magana Nana ta ce“to ai sai ki hanani zuwan, wallahi sai naje”

Kallon su ya dinga yi ganin zasu fara halin nasu ya ce“kun ga ni babu wadda zata ɗaga min hankali. Naji ba kwananta bane, kenan idan ba kwananta bane ba zata bi ni wani waje ba?” gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce

“Eh wallahi ba zata raka ka ba. Idan tana so aje da ita shopping ko wani waje sai ta bari sai ranar da ka ke daƙinta ku je, amma yau ranata ce nida ƴata Allah ba zata bimu ba.”

Taɓe baki Nana ta yi tana kallon sa taji me zai ce. Ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“shikenan tunda abun haka ne, duk ku zauna an fasa zuwa. Da Noor kawai zan je”

“Ohho sai dai a fasa ɗin amma muddin dani wlh ba zata ba!”

Zahra ta yi maganar tana zama akan sofa, Nana ta kalleshi cike da masifa itama ta ce“to ai idan ka je da Noor kamar ka je da ita ne. Sai ka tafi kai kaɗai” Girgiza kansa ya yi ya ce“wannan ne kuma baku isa ba.!”

Daga haka ya nufi waje hannunsa riƙe Noor, Zahra ta mike tana kallon ta ta ce“kin ga ko? Ai ke baki isa ki na hana abu kuma ayi ba. Kuma wallahi kamr yanda na faɗa miki sai kin san kin auri mijina, sai kin yi dana sanin aurensa, wallahi duk wani abu dana san zai ƙuntata miki sai na saka shi ya yi sa, sai kin gwammace ace baki yi aure ba!”

Dakewa Nana ta yi duk da kukan dake neman kwace mata, ta zabga mata harara ta ce

“To idan kin fasa. Na auri mijin naki, na aure shin, kuma babu abin da ki ka isa ki yi min. Wallahi baki isa ba! Idan ma akwai wadda zata yi dana sani to ke ce bani ba, ke bare wadda ya auro ki daga waje. Wadda ta aure shi saboda kwadayin abun hannunsa, ke ce zaki fita ki bar ni a gidan nan. amma ni dai ƙarya ne na bar gidan nan saboda ke!”

Zahra ta dinga kallon ta ganin yanda take gasa mata magana, can ta yi kwafa tana matsowa kusa da ita ta ce

“Ai ko zan nuna miki ke baki isa ba, ni da ya auro ni a wajen na fiki ƙima da mutunci a wajensa. Ke da aka yi masa auren cushe? Ko an faɗa miki bamu san yanda aka yi bane? Ko kin manta? Ballagazar yarinya wadda ta gama zubar da mutuncinta a waje. Shashasha mai bin maza kawai! Wadda iyayenta basu bata tarbiyyar data kamata ba! Lalatacciyar yarinya wadda lalatattun iyaye suka haifeta!”

Tuni Nana ta fara hawaye, ta cakumi wuyan rigarta tana kallon ta ta ce“Ke kin isa ki zagar min iyaye! Wallahi ƙarya ki ke! Sai dai idan kece latattun iyaye suka haifeki! Ubanki da uwarki ki ke zagi ba dai nawa ba, Banza...”

Wasu zafafan maruka taji an sauke mata a both checks ɗinta, Ta haɗiye ragowar maganar ta dafe kuncinta tana jan numfashi. Tsananin azaba ya hanata koda kuka, ya fizgota daga jikin Zahran yana mata wani irin kallo fuskarsa a haɗe ya ce

“abin da ki ke yi kenan? Abokiyar wasanki ce ita? Sa'arki ce da ki ke yi mata haka? Zagi? Zagi Nana!?”

Zahra ta fara sharar hawaye tana kallon sa ta ce“gara da Allah yasa ka dawo ka gani yau a gabanka. Idan na faɗa maka ai nasan ba yarda zaka yi ba, kullum haka take min, kullum idan har baka nan ta dawo daga makaranta haka take zama tana zagina, ya za'a yi na jure? Nana fa? Ya za'a yi a ce Nana ke zagina! Ni fa...” .

Zahra ta fashe da kuka, Fuskarsa a haɗe take, idanunsa sun sauya kala, ko ba'a faɗa ba ka san ransa ya yi matuƙar ɓaci. Ya hankaɗeta yana kallon Zahran ya ce

“Muje!”
Chapter 92 · 0% Book details