Sashe 27
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daren ranar haka ta ƙarasa shi cike da damuwa, ta kasa bacci sai juye-juye ta dinga yi, har aka fara kiran sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallah, addu'a ta zauna ta dinga yiwa Junaid tana nema masa sauƙi har gari ya fara haske sannan ta tashi ta koma ta kwanta. Ƙarfe 9:20 na safe ta farka, ta tashi zaune tana mitsitsika idanunta, wayarta ta ɗauka ta kalli screen ɗin taga missed calls har uku da numbern Junaid, ji ta yi gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta danna call back ƙirjinta na bugu da ƙarfi, ringing ɗaya ya ɗauka a sanyaye ya ce“Assalamu alaikum”
“ya jikin nasa? Yana iya magana? Me likitan ya ce”
Ta jera masa tambayoyin muryarta na rawa, numfasawa Al-ameen ya yi ya ce“da sauƙi Alhamdulillah, yanzu zan fita naje asibitin na gan shi”
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta runtse idanunta hawaye ya dinga zirarowa ta gefen idanun, jin ta yi shiru ya sanya Al-ameen ya ce“Nana”
“shikenan nima zan zo asibitin, ka faɗa min address ɗin”
Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“bari zan turo miki da text message ɗin, private asibiti ne nan gefen Jalo” toh kawai ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar, ji ta yi jikinta ya ƙara yin sanyi, me zai faru idan wani abun ya samu Junaid ta dalilinta? Ya za'a yi ta yarda? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ta dinga rerashi har bayan mintuna ashirin. Jiki babu kwari ta tashi ta shige toilet ta yi wanka ta fito, a gurguje ta shirya cikin wata umbrella pattern Abaya black colour, ko rolling mayafin ba ta yi kawai ta yafa shi loosely, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta da atm card ɗinta sannan ta juya ta fita.
Koda ta fito parlon bata samu kowa ba, dan babu alamar ma sun fito daga ɗaki, dan haka kawai ta yi waje without second thought. Tafiya ta dinga yi da sauri da sauri har ta fice daga cikin estate ɗin, ta ƙarasa gefen titi, ta ɗauki a ƙalla 10mins a wajen kafin ta samu wani napep ya kawo mutane, ta tsaida shi ta shiga sannan suka bar wajen.
****
Barraks road.
Siyama ce zaune kan sofa idanunta zube kan wayarta ƙirar iphone 13pro max tana dannawa a hankali, Aunty Khadijah ta fito daga bedroom tana gyara zaman mayafin jikinta ta kalleta ta ce“zan fita idan Umma ta dawo sai ki faɗa mata” sai da ta ajiye wayar sannan ta ɗago ta kalleta, sanye take da wata embroidery Atampa ja mai adon baki, ɗinkin t-boubou wadda ta sha stones sai kyalli take, wuyanta da hannunta sanye da kayan ado na ƙarfe sai wal-wal take, Siyama ta ɗan yi murmushi kafin ta ce“Mom kin yi kyau sosai wallahi” murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi ta ce“nima nasani, kina ji idan na fita zan biya ta gidan Hajiya Baturiya sai muga yanda za'a yi” cikin farin ciki Siyama ta ce“yauwa Mom dan wallahi tun jiya hankalina ya kasa kwanciya, idan na rufe idona fuskarsa nake gani, ji nake kamar na shirya na koma gidan yau wallahi”
“A'a kar ki je, ba yanzu ba, ki bari na dawo sai mu ƙarasa maganar” to kawai ta ce sannan ta mata Allah ya tsare ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice, ita kuma ta ci gaba da danna wayarta.
****
Misalin ƙarfe 10:30 na safe ta ƙaraso Jabo road, dan haka ta sauka daga napep ɗin ta tsaya tana tunanin yanda za'a yi ta bashi kudi dan babu ko biyar cash a hannunta, ganin yana jiranta ya sanya ta ce“yauwa ko zan maka transfer ne na manta ina sauri ban dauko cash ɗin kuɗi ba” kallonta mai napep ɗin ya dinga yi sai kuma ya ce“to shikenan yimin” numfasawa ta yi kafin ta buɗe wayarta ta shiga Opay ɗinta ya dinga karanto mata lambobin har ta gama ta tura masa sannan ya bar wajen, kalle-kalle ta dinga yi ganin titin babu wasu mutane sosai sai ɗaiɗaikun motoci dake shigewa, ta yi dialing numbern Junaid har ta katse ba'a ɗaga ba, ɗan tsaki ta yi ta sake dialing ta kai kunne, sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga da sauri ta ce
“yauwa gani a bakin titin”
“Nana!”
Junaid ya kirata muryarsa a ɗan shaƙe, dafe ƙirji ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ta ce“sir ya jikin naka? Kana lafiya dai?” jin jina kansa ya yi yana jingina da jikin gadon ya ce“da sauƙi Alhamdulillah Nana” ajiyar zuciya ta sauke ta ce“to gani a bakin titin ya sunan asibitin?” cikin sassanyar muryarsa ya ce“Al-ameen ya fito zai tawo dake kin ji, da baki wahalar da kan ki ba” Girgiza kanta ta shiga yi kafin ta ce“ba zan iya zama ban zo na ganka ba, ba zan iya ba!” ta ƙare maganar cike da rauni, Na hannunsa na dama ya sanya ya goge hawayen daya zubo masa ya ce“shikenan Nana sai kin zo” to kawai ta ce sannan ta kashe wayar, ta dinga tunanin halin da yake ciki, koda bata ganshi ba ta san jikinsa babu daɗi, domin ba haka ya saba maganarsa ba. Tana nan tsaye har wajen 11:00 na safen kafin su ƙaraso titin, kasancewar ana rana ya sanya ta ɗan ja mayafin Abayar jikinta ta rufe gefen fuskarta. A gabanta motar ta yi parking ya sauke glass ɗin yana kallonta ya ce“shigo muje” duk da bata san shi ba amma ta gane shi ne wanda ya zo ɗaukanta, dalilin muryarsa da taji, dan haka ta karasa ta buɗe passenger seat ɗin motar ta shiga sannan ta rufe, kallonta ya dinga yi a hankali kuma ya ce“sannu ko” yauwa kawai ta ce dan hankalinta gaba ɗaya yana wajen Junaid, shima bai sake cewa komai ba ya yi reverse ya bar wajen. Tafiya kusan 10mins ta kwo su bakin asibitin The Medicare, ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya zura hancin motar ciki, a parking space ɗin asibitin ya yi parking sannan ya sauka ita ma ta buɗe gefenta ta fito ta tsaya tana ƙarewa babban asibitin kallo,
“muje ko”
Maganar ta dawo da ita daga tunanin data tafi, ta jinjina kanta sannan ya yi gaba tana biye dashi, cikin vip suka shiga ita dai sai kallon wajen take har ya buɗe wani daki ya shiga, bin bayansa ta yi ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Junaid ne zaune tsakiyar gado ya jingina kansa da ƙarfen gadon idanunsa a lumshe, kallonsa ta dinga yi ganin yanda ya rame cikin kwanaki kaɗan, ya yi baƙi kamar ba shi ba, Alameen ya ƙarasa gabansa ya taɓa shi a hankali ya ce“Junaid gata” buɗe idanunsa ya yi a hankali kai tsaye kuma akanta ya sauke su, ya dinga kallonta ganin yanda ta yi kyau abin ta kamar babu abin da ke damunta, murmushin ƙarfin hali ya yi mata kafin a sanyaye ya ce“Nana”
Ƙarasowa wajen ta yi a hankali ta tsaya jikin gadon still looking at him ta ce“sir sannu, ya jikin naka?”
”Alhamdulilah Nana, naji sauƙi sosai” ya ce shima yana kallonta, shiru ta yi bata sake cewa komai ba, ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan fuskarta, girgiza kai Junaid ya yi ya ce“mene ne haka Nana? Stop crying mana” kamar jira take kawai ta fashe da kuka, ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, kasa hanata ya yi, ya dinga kallonta dakyar kuma ya iya cewa“Nana kina son wani ciwon na daban ya sameni?” girgiza masa kai ta yi ba tare da ta kalleshi ba, ya ce“to zauna ki daina kukan” Zama ta yi gefen gadon kamar babu laka a jikinta, ta kifa kanta bisa cinyarta ta ci gaba da kukanta a hankali. Juyawa Al-ameen ya yi ya bar dakin, Junaid ya numfasa sannan ya ce“Nana ɗago kan ki na ce” rage kukan ta fara yi a hankali sannan ta ɗago kan nata bayan ta goge hawayen ta kalleshi cikin shessheƙar kuka ta ce