Sashe 41
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Zahra ta kalleta fuskarta da wani irin mamaki, Atta ta jinjina kanta tana watsa mata wani kallo ta ce“eh!. Haka na ce, kuma dole ya bi umarnina. Dan babu wanda ya isa ya bijirewa abin da nake so kaf dangin Shuwa wallahi, Saboda haka ba zai yiwu ya ci gaba da zama da wadda bata danganci danginsa ba, dan ni ban ji daɗin haihuwar da ku ka yi dashi ba! So nayi ya haihu da jininsa wadda zamu yi alfahari da ita!”
Zahra ta dinga kallon Atta ganin yanda take gasa mata magana hankali kwance, ta mike tana shirin barin ɗakin Abdusammad ya shigo, faɗawa ta yi jikinsa tana fashewa da kuka, Ya ɗora hannunsa ɗaya a bayanta yana kallonta da mamaki ya ce
“Mene ne?”
Kasa cewa komai ta yi sai sake ɗora kanta da ita a ƙirjinsa tana ƙara sautin kukan nata.
Atta ta miƙe tana harararta ta ce“to da ki ke kukan dukana zai yi? Kuma aurene babu fashi muddin ina raye sai ya yi wani aure wallahi kuma sai ya auri Nana?”
Da sauri Abdusammad ya kalleta rai ɓace ya ce“Atta!”
Wani mugun kallo ta yi masa kafin ta ce“zaka dakeni ne? Na ce zaka dakeni ne? Wallahi sai ka auri Nana muddin ina numfashi a duniyar nan”
Janye Zahra ya yi daga jikinsa yana kallonta cikin ɓacin rai ya ce
“Atta wai maganar me ki ke yi haka ne? Wace Nana? Ko zan auri kowa a duniya me zan yi da Nana? Yarinyar dana raina da hannuna kuma ita ki ke son na aura?. And beside ma Nanar da ki ke magana har da ita a wanda za'a ma auren next week, Safwan zata aura, dan haka dan Allah ki daina wannan maganar kina zubar min da mutuncin gaban mutane. Sannan Zahra matata ce, na aureta saboda ina sonta ki daina zaginta dan Allah! Dan Allah Atta”
Atta ta yi mitsi-mitsi da idanunta cike da masifa ta ce
“To ina ruwana da matarka ce? Kai ta dama bamu ba, abin da muka sani shi ne sai ka ƙara aure. Sannan da ke maganar wai za'a yiwa Nana aure, ai ba auren aka yi ba, to wallahi bari kaji ko auren aka yi sai ya saketa ka aureta! Kai nake so ka aureta ba wani ba, kuma babu wanda ya isa ya hanani zartar da wannan hukunci!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 26...
Zahra dake tsaye tana kallon Atta ta fashe da kuka ta juya ta gudu ta bar ɗakin tana rufe bakinta da hannunta, Bai kalleta ba haka kuma bai yi yunƙurin bin bayanta ba. Sai ma takowa daya fara yi ya zo gaban Atta, ganin yanda ta haɗe ranta sai huci take ya sanya ya ɗan sassauta nasa fushin babu yabo babu fallasa ya ce“Atta dan Allah abar wannan maganar, ki daina sako Nana cikin maganar nan, aure fa za'a mata” wani irin kallon sheƙeke Atta ta yi masa a zafafe ta ce“to ba zan barta ba. Idan ka ji na bar maganar nan to an yi abin da nake so ne” Abdusammad ya dinga kallonta dan ya rasa abin da zai ce mata kuma, Ya girgiza kansa sai kuma ya juya ya bar ɗakin. Da harara ta bishi sannan ta ce“to zan ji tsoronka ne? Wallahi sai an yi abin da nake so idan ba haka ba hankalin kowa ba zai kwanta ba!” Atta ta ƙare maganar tana nufar ɗakinta..
Yana tura ƙofar ɗakin ya fara jin shessheƙar kukanta, Ya ƙarasa shiga ciki yana kallonta tana haɗe yan kayan da ta zo dasu a ƙaramar trolley ɗin gabanta, Sakin ƙofar ya yi sai kuma ya ja ya tsaya a wajen ya naɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu. Zahra ta kammala haɗe kayan nata tana kuka ta zura hijabi har ƙasa sannan ta juyo da shirin fita ta ganshi tsaye jikin ƙofa. Kallonsa ta ɗan yi sai kuma ta ɗauke kanta tana sake nufo ƙofar da shirin fita, murya a sanyaye kamar babu abin da ke damunsa ya ce
“Fateemarh!”
Yanda ya yi maganar cike da nutsuwa ya sanyata dakatawa, ta tsaya cak inda take har sannan tana shessheƙar kuka. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya baro jikin ƙofar ya shiga takowa har gabanta, ƙamshin turarensa daya cika mata hanci da kuma kaifin idanunsa ya sanya ta sunkuyar da kanta lokaci ɗaya taji tsigar jikinta na tashi. Kallonta ya dinga yi kafin a hankali ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago haɓarta yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ce
“Mene ne?”
Kamar jira take ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin kuka, ta ƙanƙameshi kamar zata ɓara ƙirjinsa gida biyu. Abdusammad ya ɗan yi murmushi sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya zagayeta a jikinsa, a hankali kuma cike da nutsuwa ya dinga shafa bayanta ba tare da ya ce komai ba. Bayan mintunan da basu shige biyar ba ta fara rage sautin kukan nata. Ya yi shiru yana lumshe idanunsa har ta yi tsit gaba ɗaya sai shessheƙar kukan da bata daina ba. Sai a sannan ya ɗago kansa daga bayanta yana kallonta ya ce“kukan na mene?”
Girgiza kanta ta yi tana shirin fashewa da wani sabon kukan ya ɗora hannunsa a baki cikin wata irin murya ya ce
“shiiiii!”
Haɗiye kukan nata ta yi, Ya ja kumatunta sannan ya ce“ just tell me kukan me ki ke?” Zahra ta dinga kallonsa da runannun idanunta, kenan bai ma san kukan me take ba? Bai san abin da aka yi mata ba? Sai kawai ta sake jin wani sabon kukan na kwace mata.
Abdusammad kallonta ya dinga yi sai kuma ya girgiza kansa wannan karan fuskarsa a haɗe ya ce“Idan baki min shiru ba zan ɓata miki rai kuma!”
Sanin babu wasa acikin lamarinsa ya sanya ta yi shiru tana murza idanunta, ya taɓe baki yana ƙarewa trolley ɗin hannunta kallo ya ce“get ready nan da 1hr zamu tafi”
Tamkar ta zuba ruwa a ƙasa tasha haka taji saboda daɗi da farin ciki, dan kwata-kwata bata ji daɗin garin ba, kuma ba kowane sanadi ba illa Atta, wadda tun zuwansu bata barta ta huta da jarabarta ba. Sai da ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce“Doctor tafiya zamu yi?” gyaɗa mata kai kawai ya yi yana nufar toilet. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zare hijabin jikinta ta koma ta zauna gefen gadon.
****
Sultan ya dinga kallon Safwan rai ɓace ya ce“amma baka cikin hayyacin ka ko? Baka san me ka ke cewa ba ko?” Safwan dake tsaye yana rufe agogon hannunsa ya ɗan yi gajeran murmushi sai kuma ya ce“Ya Sultan na san me nake mana, kaga maganata ta yi maka kama da ta wanda bai san me yake ba?” a fusace Sultan ya mike tsaye yana masa wani irin kallo ya ce“amma idan haka ne baka da hankali wallahi! Wace irin rayuwa ce wannan Safwan?”
“Me nayi kuma? Dan na sanar da ita gaskiya?. Wallahi Yaya ban taɓa jin son wata yarinya cikin raina sama da Siyama ba, Ni ita zuciyata ke so, amma nasan banida ikon aurenta a yanzu. Dan haka ba zan zafafa na ce dole sai ita ba, zan karbi Nana hannu bibbiyu. Amma dole ne na sanar da ita cewa ina da wadda nake so, kuma nake da burin aure. Saboda haka kar ta saki jikinta tayi tunanin da ita ɗaya zan zauna”.
Jinjina kai Sultan ya yi yana kallonsa sai kuma ya ce“okay kayi duk yanda ka ke ganin shi ne dai dai, ba zan hanaka ba, amma ina son ka sani idan har ka cutar da yarinyar nan wallahi tallahi Allah ba zai bar ka ba, idan har ka yi amfani da aurenka wajen zaluntarta Allah sai ya saka mata!” Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin fuu ba tare da ya jira ta bakin Safwan ba. Taɓe baki Safwan ya yi ya bi shi da idanu sai kuma ya ci gaba da abin da yake.
****
Ƙarfe 5:10 na yamma suka fito ƙofar gidan, Atta dake riƙe da hannun Nana ta kalli Abdusammad daya haɗe ransa kamar ba shi ba ta ce“to da ka ke haɗe rai shi ne zai hanani abin da naga dama?” kallonta kawai ya yi amma bai ce mata komai ba, ta taɓe baki ta ce“aaa to kaje da baƙin halinka, Ni kada ka tafi dani a baki, baƙonka Annabinka” duk yanda ta bashi dariya dakewa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“Sai kun zo Atta”
To kawai ta ce masa dan sam bai bata fuskar da zata sake wata maganar ba, ya shige motarsa dan daman tuni Zahra ta shiga. Da kyar su Maimoon suka rabu da Atta dan magiya suka dinga mata akan ta zo su tafi tare amma sam taƙi yarda ta ce sai ana i gobe ɗaurin aure zata zo. Babu yanda suka iya da ita haka suka haƙura suka shiga mota, ta sake sallama dasu Aliyu sannan ta kalli Nana fuskarta ɗauke da damuwa ta ce
“Ai da bake za'a yi aure ba ai zaman ki zaki yi anan ma tafi tare” murmushi kawai Nana ta yi dan ita ma taji daɗin zama da ita, Muryarta a sanyaye ta ce“to Atta ki zo mu tafi tare mana” girgiza kai ta yi ta ce“a'a ku dai je ina nan tawowa”
Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“to sai kin zo” daga haka ta nufi motar Safwan tana daga mata hannu. Sai da motocinsu suka bar ƙofar gidan sannan Atta da sauran jama'ar suka koma ciki cike da begensu.