Sashe 46
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru Nana ta yi tana kallonta idanunta cike taɓ da hawaye. Ganin bata ce komai ba ya sanya Maimoon gyaɗa kanta ta ce“Alright tun da ba zaki yi magana ba bari na kira Amma sai ita ki faɗa mata” daga haka ta juya tana shirin ficewa daga ɗakin. Tashi Nana ta yi ta riƙota da sauri a lokacin hawayen dake cikin idanunta suka samu damar zubowa kan kuncinta, ta riƙe gefen hijabin Maimoon tana hawaye a hankali. Haɗe rai Maimoon ta yi tana ƙoƙarin janye hannunta daga jikinta ta ce“Ni sakeni. Wallahi idan har baki faɗa min ba ba zan fasa kiranta ba”
Sauke numfashi Nana ta yi cikin kuka ta ce“shikenan zan faɗa miki ki dawo ki zauna dan Allah” yanda ta yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya sake bawa Maimoon mamaki, dan sam ba haka Nana take ba. Ta ɗan kalleta sai kuma ta nufi ciki ta zauna gefen gadon tana kallonta ta ce“Ina jin ki”
Nana ta sanya gefen hannunta ta share hawayen dake zubowa kan fuskarta sannan ta fara bata labarin duk abin da ya faru, tun daga sanda suka rabu dashi a supermarket da kuma sanda ya zo gida ya kawo mata wannan hotunan. Da kuma yanda suka yi da Zahra. Nana ta sauke ajiyar zuciya cikin shessheƙar kuka ta ce
“Ban san ya zan yi ba Maimoon. Bana son Junaid ko kuma Aunty Zahra su fitar da hotuna na, idan Abba ya gani ban san wane hali zai shiga ba, sannan kuma bana son na ce ba zan auri Yaya Safwan ba. Maimoon ji nake dama na mutu, daman ban zo duniyar ba, zuciyata zafi take min wallahi”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Maimoon da ke zaune tana kallonta fuskarta ta yi caɓa caɓa da hawaye ta taso jiki a sanyaye ta rike Nana cikin kuka ta ce“Nana shi ne baki faɗawa kowa ba? Shi ne ki ka bar abin a ranki?” girgiza kanta ta yi ta ce“wa zan faɗawa Maimoon? Kowa tunani yake saboda bana son auren nan yasa nake damuwa. Babu wanda ya zauna dani ya tambayeni abin da ya dameni, To taya zan iya fadawa wani?”
Maimoon ta sanya hannunta dake rawa ta share mata hawayenta sannan ta ce“shikenan ki daina kuka, ki zauna mu ga ta inda zamu ɓullowa al'amarin”
Jinjina mata kai kawai Nana ta yi, Ta kama hannunta suka ƙarasa gaban gadon suka zauna sannan ta ce“Yanzu ina ga abin da yafi shi ne a sanarwa da manya. Maganar Aunty Zahra ina ganin uncle ya kamata mu faɗawa, shi ya san yanda zai yi da ita”
Zaro idanu Nana ta yi sai kuma ta shiga girgiza kanta murya a sanyaye ta ce“a'a bana son kowa ya sani, bana son su sani dan Allah”
Maimoon ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce“to Nana idan bashi ba wane ki ke ganin zai fahimceki? Wane ki ke ganin faɗa masa zai kawo sauƙi a lamarin?”
Ta yi maganar cike da damuwa. Cikin kuka Nana ta ce“nima ban sani ba, kuma bana tunanin faɗawa kowa. Amma ya zan yi? Junaid ya ce muddin nayi auren nan sai ya fitar da hotunan, sannan ita Aunty Zahra ta ce in dai na auri Yaya Safwan sai ta fitar dasu. Kenan duk basu son na aure shi ne. Dan haka mafita ɗaya kawai nake nema”
Maimoon ta dinga kallonta can kuma ta ce“wace mafita kenan Nana? Idan baki auri Yaya Safwan ba to hakan na nufin zaki bijirewa maganar gidan nan, kuma hakan na nufin lalata al'amarin”
Nana ta rasa abin cewa sai kawai ta fashe da kuka ta ɗora kanta a cinyar Maimoon. Ita kanta Maimoon kasa daina hawaye ta yi, dan ta san dole sai wani abu mara daɗi ya faru. Ƙaddara ta riga da ta faɗawa Nana, mai fitar da ita sai dai Allah. Bayan mintuna biyar ta ɗago kanta tana kallon Maimoon ta ce
“Maimoon na tambayeki”
“Ina ji”
Ta ce tana gyara zamanta. Nana ta ɗan numfasa sai kuma ta ce“ashe daman ana barazana a soyyaya? Ashe daman mai sonka zai iya abin da zai cutar da kai? Da gaske sir Junaid yana sona kamar yanda nake son shi?”
Ba ƙaramin tausayi ta bawa Maimoon ba, amma ta dake ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“a'a Nana, babu yanda za'a yi wanda yake sonki ya yi ƙoƙarin yi miki barazana. Mai son ki tsakani da Allah ba zai taɓa tunanin samunki ta kowace irin hanya ba. Ba zai tunanin cutar da ke ba, Nana na faɗa miki wani abu.?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta numfasa ta ce“Wallahi sir Junaid ba sonki yake ba! Ke ce ki ke son shi fiye da yadda ya dace, amma shi akwai wani abu a ransa”
Nana ta yi shiru tana kallonta, can cikin zuciyarta kuma tana tunanin irin dadewar da suka yi da Junaid. Yanda ya dinga kulawa da ita, ya bata duk taimakon da take buƙata, ya sota ya ƙaunaceta, to ya za'a yi ace ba sonta yake ba? To idan ba sonta yake ba me yake?.
Maimoon ta dinga kallonta ganin ta yi shiru yasa ta ce“ki bar wannan tunanin mu tashi mu yi abin da yake gabanmu”
Girgiza kanta ta yi ta ce“ni ƙirjina ciwo yake ba zan iya yawo ba” Maimoon ta mike tana cewa“a'a ki taso mu je, Atta tun ɗazu ta ce ina ki ke”
Kamar zata yi kuka ta ce“to ni sai an jima zan fita” tana gama faɗin haka ta koma ta kwanta tana juya mata baya. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta tashi ta fice daga ɗakin dan ta san tunda tace hakan ba tashin zata yi ba..
Amma na tsaye jikin drawer tan haɗe wasu takardu na Abba da ya zube, yayinda shi kuma yake zaune gefen gado idanunsa maƙale da glasses yana duba system a hankali. Sai da ta haɗe takardun ta zuba a envelope sannan ta ajiye su gefe guda, ta ɗaga car key ɗinsa zata ɗauke taga wata takarda kamar receipt. Ɗauka ta yi a hankali ta ware ta, ta dinga kallon takardar sai kuma ta kalleshi daga inda take tsayen. Numfasawa ta yi a hankali ta ce
“Yallabai”
“Uhm”
Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba. Amma na sake karanta rubutun takardar karo na uku ta ce“amma sai naga kamar wannan kuɗin is too much” sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya kalli takardar hannunta. In a very calm voice ya ce“too much for what?”
“Sun yi yawa kuɗin, 10.5m kawai na furniture?”
Kafeta Abba ya yi da idanu sai kuma ya ce“hala akwai wata yar da zan aurar bayan Nana right?”
Amma ta ɗan kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a ba wai haka ba, amma koma ita kaɗai ce ai wannan kayan sun yi tsada” taɓe baki ya yi kafin ya ce“to ni basu min tsada ba. Kuma da a ce ta zaɓi wanda suka fi haka kuɗi ni mai siya mata ne. Sanin kan ki ne bayan Nana bani da wata yar ko ɗan da zan aurar har na masa hidima, ita kaɗai Allah ya min kyautarta. Dan haka idan ba zaki tayani ba, ki yi shiru da bakin ki”
Amma ta yi shiru sanin halinsa yasa yasa ta mayar da receipt ɗin ta ajiye sannan ta ce“to Allah ya ƙara arziki da wadata”
“Amin. Idan kuma kin shirya haihuwar wata yar ne sai ki faɗa min na rage”
Murmushi ne ya kubuce mata, ta kalle shi ta ce“a'a to ni na hana kai na haihuwa ne?” ta ƙare maganar tana zama kusa da shi. Rufe system ɗin gabansa ya yi ya juyo yana kallonta ya ce“to laifin wane? Ni dai kin san jarumi ne ba?” Amma ta ɗauke kanta tana murmushi, Ya tashi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce“bari na zo zan nuna miki” tashi itama ta yi ta ce“Allah ya huci zuciyarka. Ni breakfast ma na ɗora” daga haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi murmushi ya juya ya shige toilet.
****
Karfe 4:00 na yamma aka fara henna's party ɗin, gaba dayansu suna apartment ɗin Hajiya Babba dan duk yafi ko ina girma. A compound ɗin gidan aka kira masu decorations suka tsara wajen, kai ka ɗauka wani event ɗin aka je. Gaba ɗaya dangi na kusa dana nesa sun zo gidan, dan haka wajen ya cika da jama'a. Amaren suna sanye da dogayen riguna na saki maroon colour, kasancewar su farare yasa ya yi musu kyau sosai. Fuskarsu fresh dan basu yi kwalliya ba, sai powder da lip gloss da suka shafa. Kowacce sai harkokinta take da ƙawayenta dan duk an gama masu ƙunshin, Nana kuwa na gefe ɗaya ta zauna kusa da Aunty Mariya da suka zo daga Abuja. Ta yi shiru tana kallon fararen hannunta wanda suka yi kyau da lallen da aka yi musu, sai dai zuciyarta a dagule take da tunane-tunane kala-kala. Sai kusan magriba sannan aka tashi, Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa tana zuwa ta shige ɗakinta tun kafin mutanen gidan su taru.
A gefen gadonta ta zauna tana wani irin numfarfashi dan tun ɗazu take jin ƙirjinta na mata wani irin zafi, Ta kwanta a hankali tana lumshe idanunta, a hankali kuma ta fara jin azabar na ƙaruwa, numfashinta ya fara ɗaukewa dakyar take iya jawo shi. Tana nan kwance har bayan mintuna ashirin sannan wani wahalallen bacci ya ɗauketa, Cikin baccinta taji kamar a mafarki ana kiran sunanta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana ware su a ɗakin. Babu kowa a ciki dan haka ta tashi zaune tana dafe saitin zuciyarta wanda ya ci gaba da bugawa da sauri, Ta lumshe idanunta sannan ta tashi ta shige toilet. Wanke fuskarta ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta zura hijabinta ta gabatar da sallar magriba sannan ta zare hijabin, tana ƙoƙarin tashi daga wajen Amma ta turo ƙofar tana kallonta ta ce
“Nana ki zo inji Abbanki”