← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 125

Sashe 121

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce a takaice, Shiru Zahra ta yi duk sai taji bata ji daɗi ba, Ita yanzu bata da niyyar ganin wani abu mara kyau ya samu Nana dan haka ta numfasa ta ce

“Sai an jima.”

“Mu jima da yawa”

Ya ce yana ƙoƙarin rufe system ɗin. Tashi ya yi ya nufi saman shima, Kai tsaye daƙinta ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Tana zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take. Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ƙarasa ciki, A gefen gadon ya zauna yana kallon ta still bai ce komai ba, Can dai ya numfasa ya ce

“Nana!”

Bata amsa ba haka kuma bata ɗago kanta ba, Ko kaɗan bata son jin muryarsa, Baƙin ciki isarta yake, Ji take kamar ta mutu ta huta da zama dashi. Ya jawo hannunta a sanyaye ya ce

“Me akayi miki kuma?”

Ya yi maganar yana ƙoƙarin matso da ita jikinsa, Janye jikinta ta yi ta sauka daga kan gadon ta shige toilet ba tare da ta yarda sun haɗa ido dashi ba, Ya yi shiru yana kallon ƙofar bayin, Can kuma ya tashi ya fice kawai.

****
Yola, Nigeria.

Zahra ta dinga kallon Umma jiki a sanyaye, Can dai ta ce

“Umma Ya Bashir kuma?”

Gyaɗa mata kai Umma ta yi kafin ta ce

“Eh Zahra'u, Bashir, Yana son ki ya ce. Kuma zai aure ki, Dan haka kawai ki bashi dama, Da zarar iddar ki ta ƙare sai a ɗaura muku aure.”

Shiru ta yi tana sauraren Ummar, Ita gaba ɗaya sai taji jikinta ya mata sanyi, Bashir ɗin da bata yi tunani ba shi ne zai zama mijinta na biyu, Shi ɗin ɗan yayar Umma ne, A Kaduna suke, Yana aiki a Saudiyya. Tun tana ƴar ƙarama ya taɓa cewa yana sonta, amma bayan tafiyarsa sai ta gamu da Abdusammad ta kuma ce shi take so, Har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba, Gashi ƙaddara na neman sake hada su a matsayin mata da miji.

“Zahra'u”

Umma ta kira sunanta a nutse, Ɗaga kanta ta yi ta kalleta a sanyaye ta ce

“Na'am Umma...”

“Kin yarda? Bana son nayi miki abin da ba zai miki daɗi ba, Idan kin ce bakya son sa shikenan domin a yanzu kina da damar zaɓar mijin da ki ke so. Amma ki sani ba zan ji daɗi ba idan ki zama kamar yanda Khadijah ta zama, Kin ga dai yanzu halin data saka kanta”

Zahra da hawaye ya fara sakkowa kan fuskarta ta ce

“Ba zan sake ƙin biyayya ba Umma. Na yarda zan aure shi, Na yarda wallahi”

Ajiyar zuciya Umma ta sauke dan daman ta san halin Zahra ba zata bata matsala ba, Ta dafata fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce

“Allah ya yi miki albarka, In sha Allah Alkhairi zaki gani a rayuwar ki Zahra'u, In sha Allah ba zaki sake samun matsala ba. Ki dinga yawan addu'a kin ji, Allah ya tabbatar mana da Alkhairinsa.”

Jiki a sanyaye Zahra ta ce

“Amin Umma, Na gode sosai."

Murmushi kawai ta yi, Ta miƙe tana ƙoƙarin barin ɗakin ta tuna, dan haka ta tsaya ta ce

“Na manta, Ki samu ki je ki duba Khadijah, Ina son ki manta da komai dan Allah.”

Ba zata iya yiwa Umma musu ba, Duk da daman ita bata riƙe ta ba, Ta kalleta ta ce

“To Umma zan je in sha Allahu.”

“Allah ya yarda”

Cewar Umma, Sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana jin wani iri a ranta, Kaddara ta rabata da mijinta, Ta kuma rabata da ƴarta, sannan take shirin haɗata da wani sabon mutumin a matsayin abokin rayuwa. Tabbas Allah abun tsoro ne, Komai nasa akwai hikima da dalilin faruwa.

Bayan sallar la'asar ta shirya suka je gidan Anty Khadijah ita da Safeena da Amal. Sanda suka je tana zaune a ɗaki ta zuba uban tagumi, Gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Ta yi wata irin rama ta tashin hankali, Babu abin da ka ke gani a jikinta sai ƙashi da idanu, Ga wata irin yamushewa da fatarta ta yi. Sai kace wadda take fama da cutar ƙanjamau, Tun ranar data faɗi a soro bata sake takawa ba, Gaba ɗaya kafafun sun nannaɗe sannan Malam Garba ya hana akai ta asibiti ballantana a san abin da ke damunta. Sai ƙarewa take a banza, Babu ci babu sha, Sai kuka kawai, Babu abin da ke ɓata mata rai sama da abin da Kaddu ta yi mata, Ashe ƙawar da take ɗauka fiye da kowa nata ita ce take cutar da ita, Tabbas duk wanda ya bar Allah sai Allah ya bar shi, Kuma duk harkar da babu Allah kana zaune zata wargatse aji kunya. Zahra da ke zaune gefen gado ta kalleta ta ce

“Sannu Anty, Allah ya baki lafiya”

Anty Khadijah bata iya cewa komai ba sai hawaye dake zubowa kan yamusasshen fuskarta, Safeena da ke hawaye ita ma ta ce

“Kin gani ko Anty? Abin da nake ta faɗa miki kenan amma ki ka ƙi ji, Yanzu kalli halin da ki ke ciki. Kin zama abar tausayi, Kin raba mata da mijinta, Kin yi silar mutuwar ƴarta, Ina zaki je da wannan haƙƙin?”

Girgiza kai Zahra ta yi muryarta a sanyaye ta ce

“Ki bar cewa haka Safeena, Ni wallahi na yafe mata, Na yafe har abada. Duk da naji zafinta a da amma yanzu ya huce, Na gane kuma ƙaddara ce ta sanya hakan ta faru, Dan haka ni na yafe kome ta yi min, Ina mata fatan Allah ya yafe mata.”

Wani irin raunataccen kuka ne ya kwacewa Anty Khadijah, Ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana rera shi, Tabbas ta yi dana sani, Ta ji kunya, Ta yi nadama. Nadamar da baza ta amfanar da ita komai ba, Domin komai ya ƙare mata. Tashi Zahra ta yi ta koma gefenta ta ɗagota ta fara share hawayenta ta ce

“Ki yi haƙuri Anty, Dan Allah ki daina kuka kada wata cutar ta same ki bayan wadda ki ke ciki”

Gyaɗa mata kai Anty Khadijah ta yi sai a sannan ta ce

“Na gode Zahra.”

Zahra ta yi shiru hawaye na zubowa kan fuskarta, Ɗan uwa rabin jiki, Sai taji ina ma ita ce ciwon ya sameta ba Anty Khadijahn ba. Suna nan zaune har kusan magriba sannan suka tafi gida, Ko awa biyu basu yi da zuwa gida ba aka kira wayar Umma, Bayan ta ɗaga matar gidan ta sanar da ita halin da Anty Khadijahn ke ciki, Umma da ta gama ruɗewa ta faɗawa su Zahra haka suka sake ɗungumar jiki suka koma gidan, Koda suka je basu sameta ba, Dan an yi asibiti da ita. Dan haka suka wuce can, A asibitin suke samun labarin irin dukan da Malam Garba ya yi mata bayan tafiyar su Zahra, Ya kuma ce ya saketa, Akan ta tambaye shi gwala-gwalanta da ke hannun sa. Umma ta jingina da jikin bango hawaye na zubowa kan fuskarta. Su kansu su Zahra kuka suke, Duk da basu san halin da take ciki ba, Suka bugawa Siyama waya suka sanar da ita. Kasancewar gobe zata gama takaba yasa ta ce goben tana hanya zata zo, Suna nan zaune har kusan ƙarfe 10 na dare kafin likita ya fito, Da sauri suka ƙarasa inda yake, Zahra ce ta yi ƙarfin halin cewa

“Doctor ya jikin nata?"

“Ki sameni a office!"

Shi ne kawai abin da ya ce sannan ya yi gaba, Zahra ta sauke numfashi ta bi bayansa. Koda ta shiga office ɗin a tsaye ta same shi, Ya yi alama data zauna ta zauna sannan shi ma ya zauna, Zare glasses ɗin idanunsa ya yi yana kallon ta ya ce

“Ke ƴar uwarta ce?”

Gyaɗa masa kai Zahra ta yi ta ce

“Eh Yayata ce uwar mu ɗaya uban mu ɗaya”

Shiru likitan ya yi can kuma ya ce“Me yasa baku kawota asibiti ba tun wuri? Sannan wa take aure? Ina yake?”

Sosai gaban Zahra ya fadi, Ta ce“Tana gidan mijinta ne kuma malami ne baya bari ta fita”

Da mamaki ya ce

“Malamin ya yi mata wannan illar? I'm sorry to say ya gaba lalata mata jiki, Na ɗaya ba zata sake haihuwa ba, Na biyu tana da cutar Hiv. Na uku ƙafafunta ba lallai bane su sake takawa, Sakamakon faɗuwar da ta yi!”

Zahra bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba, HIV? Kenan ita ta shafawa Siyama? Siyama kuma ta shafawa Safwan? Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una. Shi ne abin da kawai take iya maimaitawa cikin ranta, A fili kuwa ban da kuka babu abin da take. Tashi likitan ya yi ya fice daga ɗakin baki ɗaya.

****
Washegari da safe Nana na tashi ta yi wanka, Ta fito parlour, Kitchen ta shiga ta haɗa breakfast sannan ta fito ta zauna anan kan sofa, Bayan ta gama ci ta tashi ta koma ɗakin da niyyar ɗaukan maganin da Amani ta bata, Dan ta san yanzu duk inda yake to ya gama shirin fita. Sai dai me? Duk irin duban da ta yi wa jakar bata ga maganin ba, Babu shi babu dalilinsa. Sai da ta zazzage gaba ɗaya takarcen da ke ciki duk da ta san a pocket ɗin jakar ta ajiye, amma aka ce idan raƙumin ka ya ɓata to har kafar allura ga duba. Tana cikin dube-dube aka buɗe ƙofar ɗakin, A ɗan zabure ta juya tana kallon sa, Sanye yake da suit black colour da alama fita zai yi. Hannayensa zube cikin aljihun trousern dake jikinsa, Kallon kallo suka dinga yi, Can dai ta ɗauke nata idanun tana ƙoƙarin kwashe kayan data zubar

“What are you looking for Nana?”

Ta tsinkayi muryarsa a sama, Girgiza kanta ta yi a ɗan rarrabe ta ce

“Babb...Nothing”

“Are you sure?”

Ya sake tambayarta. Juyawa ta yi ta kalle shi, Ta ga ya sakar mata murmushi. Ya zaro tablet ɗin daga hannunsa ya daga shi yana faɗin

“Ko dai wannan ki ke nema? Are you looking for ur abortion pill ko?”
Chapter 121 · 0% Book details