← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 125

Sashe 13

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya Aliyu" Amrah ta bata amsa, shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi, ji tayi ta gaji da tsaiwar dan haka kawai ta zauna cikin ciyayin da ke wajen. Hawayen da bata san dalilin su bane suka dinga zuba kan fuskarta, kallonta duk suka dinga yi kafin Maimoon ta yi karfin halin cewa

"Me ki ke yiwa kuka Nana?"

"Yaya Sultan!"

Maganar ta suɓuce mata ba tare da ta yi aune ba.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

https://chat.whatsapp.com/Hbf1rpqVyiZCko3JyHNMcG?mode=ems_copy_c

Page 8...

Hamida ta durƙusa gabanta tana kallonta da mamaki ta ce"me ki ka ce Nana?" girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce"nothing" daga haka ta miƙe ta bar wajen ba tare da ta sake kallonsu ba. Kai tsaye apartment ɗin su Hamida ta nufa kamar yanda Amma ta ce mata, koda ta shiga bata samu Mama a parlon ba dan haka ta nufi daƙinta kanta tsaye, bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Mama na zaune ƙasan gado tana karatun Alqur'ani, ta ɗago kanta tana kallonta ta ce"wa'alaiki assalam Khadijah shigo" jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ta zauna kusa da ita sannan ta ce"Mama ina kwana?"

"Lafiya kalau Nana"

Sunkuyar da kanta ta yi tana jan fingers ɗinta ta ce"daman Amma ta ce wai na zo" jinjina kai Mama ta yi, ta rufe Alkur'anin hannunta ta ajiye kan drawer sannan ta gyara zamanta cikin nutsuwa ta ce"eh ni na ce ki zo, daman zan yi wata magana da ke ne" sosai Nana ta ji jikinta ya yi sanyin barin yanda taga Mama na mata magana cikin kulawa. Mama ta numfasa sannan ta ce"Nana wane wanda ki ke so?" Da sauri ta ɗago kanta ta kalleta, kenan Amma ta faɗa mata abin da ya faru? ta tambayi kanta, Mama ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba ya sa ta ce"ina jin ki faɗa min" cikin shessheƙar kuka Nana ta fara cewa"malamin mu ne a Aun, Amma kuma ta ce kar na sake kulashi" Mama ta jinjina kanta cike da gamsuwa sannan ta ce"meyasa ki ka fara son sa bayan kin san tsarin gidanku Nana? baki ganin za'a ga rashin kunyarki? duk cikin yan uwanki babu wanda ya yi miki sai a waje? Uhm. Ko kina son ki ɓata mana zumunci ne?" Da sauri ta shiga girgiza kanta tana jan numfashi ta ce"a'a wallahi Mama, bani da niyyar tarwatsa zumuncin da aka gida tun iyaye da kakanni, nima zan yi farin ciki idan har nabi wannan dokar, amma kuma..."

Ta sunkuyar da kanta kuka na kwace mata, Hannunta Mama ta kama ta riƙe cikin nata ta ɗago fuskarta tana kallonta ta ce"amma kuma me? ba zaki iya sadaukar da soyyayarki ba saboda danginki? ba zaki zo farin cikin mahaifinki ba? Na faɗa miki wani abu?; sanda aka ce za'a min aure ban yi shekarunki ba, I'm just a 17yrs old, aka aura min babansu Hamida, ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba sai a ranar da aka kawoni gidansa. And kamar ku muma boarding school aka kai mu tun daga Junior har candy. Saboda haka bamu saba da wasu mutane ba daga gida sai makaranta, a lokacin da muka dawo gida bayan mun kammala makaranta marigayi da kansa yake ɗaukanmu ya kai mu unguwa, duk inda ake shaƙawata sai da ya kai mu, har Umrah muka je. A sannan kuma na gamu da wanda nake so, sunansa Sagir, na so shi kamar ba zan daina ba, har cikin estate ɗin nan yake zuwa, time ɗin duk ba'a yi wadannan gine-ginen ba. Ya zo ba tare da kowa ya sani ba, kin san me aka yi? Rana ɗaya na dawo daga islamiyya aka ce an ajiye min kaya a ɗaki naje na saka, ban yi tunanin komai ba naje na shirya cikin leshin mai kyau da tsada, sai da na fito sannan Baba ya sa aka kirani ɗakinsa ya faɗa min an ɗaura min aure da babansu Hamida, ban ce komai ba a sannan duk da yanda na dinga ji a zuciyata, haka na haƙura nace to, aka ɗaukeni aka kawo ni gidan nan. Sai da dare ya yi sannan ya shigo na gansa, a lokacin bana son sa har cikin raina, amma ba zan iya ce masa ba, kuma ban isa na faɗawa wani ba, dan haka na riƙe abun a raina har zuwa sanda kyautatawarsa tasa na fara jin ƙaunarsa. Naji zan iya rayuwa dashi, rayuwa mai ɗorewa, na manta da cewa shi zaɓin iyayena ne, muka ci gaba da rayuwarmu cikin farin ciki da son juna"

Mama ta sauke nannauyan numfashi sannan ta ci gaba da faɗin"kin san me yasa na baki wannan labarin?" Nana ta girgiza kanta hawaye na sake zubowa kan kuncinta, Mama ta ce"saboda ki san ba komai ka ke so kake samu ba, a lokacin dana bijire na ce sai na auri Sagir da ban san me zai sameni ba. Ban san wace rayuwa zan yi dashi ba, amma biyayyar da nayi ya sanya Allah ya dubeni ya haɗani da wanda yake sona yake kuma tausayina. Ba dole sai kin auri wanda ki ke so ba, amma dole ne ki auri wanda yake ganin girmanki dana iyayenki, wanda ki ke da tabbacin ba zai cuceki ba a iya zamanki dashi. Kuma wannan shi ne irin mijin da muke fatan kowaccen ku ta samu, duk wadda ki ka ga an haɗata da wani, to an duba an ga wannan shi ne zai dace da rayuwarta ne, saboda haka ki zama mai biyayya Nana ba mai son zuciya ba. Ki sani wannan abun da ki ke shirin yi ba ƙaramin yaƙi bane, faɗa ne tsakanin zuciya da kuma al'ada, dan haka ba abu bane mai yiwuwa ki yi nasara a kai. Dan haka ina mai baki shawarar ki yi haƙuri da abin da aka tsara, ki ɗauka wannan shi ne Alkhairin rayuwarki"

Nana ta dinga gyaɗa kanta tana kuka, jikinta ya yi sanyi sosai kuma maganganun Mama sun shigeta, ita ma ta san ba lallai bane ta yi nasara akan abin da take so. Mama ta sanya hannunta ta share mata hawayen dake zuba sannan ta ce"ki daina kukan kin ji" sake jinjina kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce"To Mama, ni daman na haƙura dashi amma dan Allah ki ce kada su aurar dani yanzu, tsoro nake ji mama, tsoro nake ji..."

Sosai ta bawa Mama tausayi dan akwai ƙalubale ba ƙarami ba a cikin auran yarinta, amma ta ɗan yi murmushi ta ce"mene ne abin tsoro Nana? Yayanki zaki aura fa, kuma kin san ba zai cuceki ba" girgiza kanta tayi ta ce"ni bana son aure yanzu Mama, ni karatu nakeson nayi, kuma ban san wa zan aura ba ma"

"Ba'a faɗa miki ba?"

Da sauri ta gyaɗa kanta, Mama ta ce"Safwan zaki aura Nana" sake fashewa ta yi da kukan da bata san dalilinsa ba, Mama ta ce"mene ne hakan?" kasa cewa komai ta yi, sai kuka take rusawa. Tashi Mama ta yi ta ce"ai shikenan" daga haka ta fice daga ɗakin, kwanciya ta yi a wajen ta ci gaba da rera kukanta kamar an kunna radiyo.

****
Ƙarfe 2:12 na rana baƙaƙen motocin suka fara shigowa cikin estate ɗin, nan da nan hayaniyar convey ta cika ko ina, a bakin apartment ɗin Hajiya Babba suka yi parking,black ride ne guda bakwai a jere, suna gama parking aka fara buɗe murfin kowace mota, sojoji ne suka dinga fitowa, kowannesu sanye da uniform da kuma bindiga. Suka jere a gaban motar da ke tsakiya wadda har sannan babu wanda ya fito, ƙofar da ke left side aka buɗe Aliyu ya fito daga ciki, sannan ya zagaya da kansa zuwa ɗaya side ɗin dai dai nan wani soja ya buɗe murfin, ƙafarsa ta dama ya fara sakowa wajen motar mai sanye da takalmin Gucci black colour sai sheƙi yake, sannan ya dafa murfin motar ya fito. Wani babban mutum ne mai cikar kamala da sura, wanda a ƙiyasi ba zai shiga 37-38yrs ba, fari ne tas kuma asalin kyakkyawa, kai tsaye ba za'a iya cewa bature bane haka kuma ba za'a ce bafulatani bane, fatarsa har wani ja take saboda tsananin fari. Yana sanye da wasu Tom ford suit black colour wanda suka tsaya a jikinsa kamar dan shi aka yi su, hannunsa maƙale da agogon Richard mille sai kyalli yake, idanunsa maƙale suke da Dita sunglasses, gashin kansa akwance har gaban kansa ya yi luf irin na larabawa, murmushi ya yi wanda ya sanya farare kuma rabbabun haƙoransa suka bayyana, kowane haƙori shi kaɗai yake ba tare da ya jingina da ɗan uwansa ba, sai kuma ƙatuwar wushirya a tsakiya. Yana da ƙasumba mai yawa kuma wadda tasha gyara sai kyalli take, iya ka haɗuwa da kuma tsafta wannan mutumin ya cikata. Kana ganinsa kaga babban mutum wanda ke ji da kansa, Aliyu ne yayi murmushi ganin yanda yake bin gidajen da kallo ya ce"Buddy muje mana" bai ce masa komai ba sai gaba da ya yi ya fara takawa cikin izza da taƙama.

Parlon Hajiya Babba a cike yake da mutanen gidan, su Papa, Abba, Daddynsu Hamida, Safwan, Hamid,Sultan, Mama, Amma, Ummi, Mami, da ma sauransu duk suna zazzaune suna jiran shigowarsa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, ya tsaya daga gefe yana bin kowa da kallo, kafin a hankali ya zare glasses ɗin idonsa. Manyan idanunsa suka bayyana ya dinga kallon kowa fuskarsa ɗauke da murmushi, da sauri kuma ya ƙarasa ciki yana zuwa ya shige wajen Abba yana rungumeshi.. Murmushi shi ma Abban ya yi yana shafa kansa ya ce"Yaron kirki" langwaɓar da kansa ya yi yana jin wata irin nutsuwa na saukar masa, ya daɗe jikin Abba kafin ya tashi ya ƙarasa wajen Papa, haka ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya yana gaishe dasu kafin ya ƙarasa wajen Hajiya Babba. Ya shige jikin mahaifiyar tasa yana lumshe idanunsa, kasa ɓoye farin cikinta ta yi ta dinga taɓa jikinsa tana murmushi. Above 5mins kafin ya tashi ya zauna gefenta yana kallon sauran ƙannen nasa, cike da girmamawa suka dinga gaishe dashi, yana amsawa cikin sakin fuska.
Chapter 13 · 0% Book details