← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 125

Sashe 102

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafa kanta ya yi ya ce“Don't worry kin ji.” Sun daɗe a haka kafin ya miƙawa wata maid ita ya nufi wajen, Zaune ya tarar da Zahra gefen motar tana kuka har sannan. Ya ɗan yi jim sai kuma ya ƙarasa yana kallon ta ya ce

“Tashi daga nan”

“Ba zan tashin ba! Ina ruwan ka dani ma? Mene ruwanka da zamana?”

Zahra ta yi maganar a fusace. Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya dauke kansa yana kallon fountain ɗin dake zubar da ruwa as usual ya ce

“Kada ki ɓata min rai. Ki tashi ki koma ciki nace!”

Miƙewa ta yi tana kallon sa rai ɓace ta ce“au tunanin ka zan yi abin da ka ke so ne? Bayan ka mayar dani banza shara a gidanka? Bayan kana nuna rashin adalci a fili? To wallahi ba zan yi ba! Kuma ka sani wannan abun da ka yi tamkar ka buɗe wani sabon shafi ne na bala'i da tashin hankali a cikin gidan nan, ba zan taɓa bari a zauna lafiya ba! Ita kuma yarinyar za tayi dana sanin shigowa cikin gidan nan!”

Zahra na gama faɗin hakan ta nufi cikin gidan kamar zata tashi sama, hannunta sai ɗigar jini yake amma ko damuwa bata yi ba, da idanu kawai Abdusammad ya bita sai kuma ya sauke numfashi. Ya dinga kallon yanda ta wulaƙanta tsaddajiyar motar, gaba ɗaya ta farfashe glasses ɗin ta. Girgiza kansa ya yi yana sake jin jina al'amarin mata, Kafin daga bisani ya yiwa wasu securities umarni dasu gyara wajen a ɗauke motar. Shi kuma ya koma cikin gidan.

Nana na zaune gefen gadonta sai kuka take, idan ta tuna yanda Zahra ta farfashe mata glass ɗin sabuwar motarta sai taji ranta na ɓaci. Kasa jurewa ta yi ta janyo wayarta dake can ƙarshen gadon ta yi dialing numbern Hajiya Babba. Sai da ta kusa katsewa sannan Hajiya ta ɗauka, Daga ɓangarenta ta ce

“Nana yau kuma kin tuna dani?”

Fashewa da wani sabon kukan Nana ta yi, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ce

“Mene ne? Kukan me ki ke takwara?”

Cikin shessheƙar kuka ta ce

“Hajiya Anty Zahra ce!”

Da mamaki Hajiya Babba ta ce

“Me ta yi miki ita Zahra?”

Nana na goge hawayenta ta ce

“Dukana ta yi Hajiya, saboda kawai nayi magana shi ne ta mareni. Kuma ta fasa min motar da uncle ya siya min...”

Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Hajiya Babba da ranta ya gama ɓaci sakamakon maganar dukan da taji ta ce

“Shi Abdusammad ɗin yana gani ta mareki?” gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce

“Eh mana. Kuma Hajiya ta fasa min motar da ya bani...”

Shiru Hajiya Babba ta yi can ta ce“shikenan yi shiru bari zan kira shi ya kai mata wayar naji dalilin da zata dake ki.”

Nana ta gyaɗa kanta ta ce“To Hajiya na gode.”

“Ki daina kuka”

Hajiya Babba ta yi maganar a tausashe, To Nana ta ce sannan ta kashe wayar, Ta kwanta gefen gadon ta yi shiru tana tunani.

Zahra na zaune tsakiyar gadonta tana waya da Anty Khadijah ya shigo ɗakin, Tana ganinsa ta sauke wayar daga kunnenta ba tare da ta kashe ba, Ya ƙaraso gaban gadon ya zauna yana kallon ta fuska a ɗaure ya mika mata wayar dake hannunsa. Kallon wayar ta yi sai kuma ta kalle shi, Ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta amsa ta saka wayar a kunne. Hajiya Babba dake zaune kan sofa ta ce

“Zahra'u”

Cike da girmamawa ta ce

“Barka da rana Hajiya, Ina yini?”

“Alhamdulillah. Daman naji wani batu ne wanda bai min daɗi ba, na ce bari na miki magana. Akan me kina da hankalin ki zaki dinga biye wa yarinya ƙarama? Akan me zaki daketa? Kin san yanda muka ɗauketa? Kin san matsayinta a wajen mijin ki shi kansa? Akan me haka?”

Hajiya Babba ta yi maganar a faɗace, Shi dai Abdusammad shiru ya yi dan duk abin da take faɗa yana ji saboda a handsfree wayar take. Zahra da hawaye ya sake cika idanunta ta girgiza kanta ta ce

“Wallahi Hajiya ba laifina bane. Yarinyar ce bata da kunya, Har ni Nana zata dinga yiwa kallon kishiya tana faɗawa magana? Kasa jurewa nake wallahi!”

“Shi ne ki ke dukanta? Idan mahaifinta yaji zai ji daɗi ne? Kin san son da yake wa ƴarsa? Bana son sake jin irin haka ta faru. Kada ki sake cewa zaki kai hannu ki daketa, idan ta yi miki laifi ai ga mijinku nan ki sanar masa, amma kada ki sake cewa zaki ɗauki hukunci da kan ki.”

Zahra ta haɗiye wani miyau mai ɗaci kafin ta gyaɗa kanta ta ce“In sha Allah Hajiya ba zan sake ba.”

Hajiya Babba ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce“Yauwa to, Allah ya yi albarka.” Da Amin ta amsa sannan ta miƙa masa wayar, Ya karɓa ya tashi ya fice bayan ya saka wayar a kunnensa. Zahra ta runtse idanunta wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta, Anty Khadijah da ke kan layi har sannan ta taɓe baki ta ce

“Zahra! Zahra! Zahra! Kina zaune a inda ba'a ganin darajarki? Kina zaune a inda ba'a ganin ki da ƙima? Ya ma za'a yi uwar mijin ki ta dinga faɗa miki irin wadannan maganganun? Taɓ!”

Zahra da taji kamar ta fama inda ke mata kaikayi ta fashe da kuka tana cewa“Anty kin gani ko? Basa sona! Ba sa ƙaunata, basu damu dani ba. Kamar ba sirikar gidan ba, Daman Hajiya Babba ba son auren mu take ba kawai ta yi shiru ne. Yanzu kuma ya auri wadda take so dole ta nuna mana banbanci, wallahi ji nake kamar na gudu na bar gidan nan, kamar na yi tafiyata na bar su!...”

Ta sake fashewa da wani kukan. Girgiza kai Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“ba za'a yi haka ba, dole a san abin yi. Babu yanda za'a yi na bar ki cikin wannan masifar Zahra! Yanzu ni babu kudi a hannuna. Duk na bawa Garba, idan kina da wasu kuɗaɗe ki samu ki turo ko ki karɓa a hannun mijin ki, na san abin da zan yi miki. Wallahi babu wadda ta isa ta fitar dake daga cikin gidan nan, Kuma ko kallon banza babu wadda ta isa ta yi miki har da uwar tasa.” Shiru Zahra ta yi kamar me tunani sai kuma ta ce“Ina da kuɗi zan turo miki Anty.” Anty Khadijah ta gyada kanta ta ce“Toh shikenan. Ki daina kuka amma” Share hawayenta ta yi ta ce“In sha Allah Anty.”

“Ki saki ran ki, kada ki nuna ran ki ya ɓaci, Ku tashi ki je ɗakinsa. Kada ki ce zaki yi fushi yanzu, ki kwantar da kan ki” Toh kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar. Ta tashi kamar yanda Anty Khadijah ta ce mata ta shige toilet, wanka ta yi ta fito ta ɗauki kayan baccinta ta saka sannan ta fito daga nata apartment ɗin ta nufi nasa.

Koda ta shiga zaune ta same shi tsakiyar gado ya yi shiru da alama wani abun yake tunani, ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon tana kallon sa ta ce

“Doctor!”

Tamkar a mafarki haka yaji muryar tata, Ya ɗago ya kalleta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, Ya ɗan yi jim kafin ya ce

“Zahra lafiya? Ko nan ɗin ma zuwa ki ka yi ki tadan hankali?”

Saurin girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“A'a wallahi, dama zuwa nayi na baka haƙuri. Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, ba zan sake ba, wallahi kasa jurewa nake doctor, kai kan ka ka san ina sonka. A duk sanda naga Nana ta raɓeka ji nake kamar zuciyata zata fito, sai naji ba zan iya barinta ba. Dan Allah dan Annabi doctor ka fahimceni, koda zaka nuna mata soyyaya kada ka yi a gabana. Wallahi ba zan jure ba, Ita tana da kowa, tana da danginta wanda suke sonta. Tana da dangin miji wanda suke goya mata baya, sannan kuma tana da kai. Ni kuma bani da su, kai kaɗai nake da! Da kai na dogara. Idan ka gujeni bani da kowa....” Zahra ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye na zubowa kan fuskarta. Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, Ya sani Nana ta fita gata. Nana na da gatan iyaye, tana da na yayye sannan kuma ga gatan miji. Saɓanin ita da shi kaɗai ne gatanta sai kuma Allah, Tashi ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna gefenta ya kama hannunta murya a sanyaye ya ce

“Na sani Zahra, kuma kema kin san bani da niyyar wulaƙanta ki, ban aure ki saboda na cutar dake ba. Na aure ki ne saboda ina son ki, saboda na shirya zama dake, kuma zan kare mutuncin ki da martabarki. But why ki ke son ɓata kan ki? Akan me ki ka sauya? Ba haka ki ke ba da Zahra. Wannan ba ɗabi'un ki bane, Kin zama mara haƙuri, kin zama mara kunya, kin koyi rashin mutunci kala-kala. Faɗa min wane yake son gurɓata tunanin ki?”

Ya yi maganar cikin tausasa harshe, Zahra dake kuka ƙasa-ƙasa ta ɗago kanta ta kalle shi sai kuma ta girgiza kanta ta ce

“Dan Allah ka yi haƙuri, ba zan ƙara ba.”

Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce“Ba komai ni ban riƙe ki ba. Kuma idan sabon mota ki ke so ba sai kin fasa nata ba, sai ki faɗa min na sauya miki. Naga kina da cars har biyu kuma ba hawa ki ke ba, that's why yasa ban sa an kawo dake ba. But za'a kawo miki kema” Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a wallahi, ka bar shi.” Bai ce komai ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, Zahra ta saki ajiyar zuciya tana jin duk wata damuwar na narkewa.

Washegari da safe ya shiga apartment ɗin Nana, tana kwance akan gado tana kallo, Ya ƙarasa ciki ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce

“Madam ko gaisheni ba zaki yi ba?”

Ko kallon sa bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi. Ya ɗan yi murmushi yana shafa kansa kafin ya ce
Chapter 102 · 0% Book details