← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 125

Sashe 72

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Kuma dai Anty? Ni fa na gaji” harararta ta yi tana shan kwana ta ce“to ai sai ki yi ta gajiyar.” Tura baki Nana ta yi kafin ta koma ta jingina da kujerar motar idanunta ƙur akan titi tana kallon motocin da ke shigewa, Time to time take tuna maganganun Anty Ramlah, wani ta yi dariya wani kuma ta tura baki, murya can ƙasa ta ce

“Wai uncle ɗin tab!”

“Magana ki ka yi?”

Anty Ramlah ta tambayeta ba tare da ta kalleta ba, girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“A'a.” Bata sake ce mata komai ba har suka ƙarasa Gibson Jalo ɗin, Ta buɗe motar ta sauka tana kallonta ta ce“ki jirani ina zuwa” gyaɗa mata kai ta yi, Ta juya ta nufi gidan da yake kallon su. Tun Nana na jure zaman motar har sai da ta gaji, ga yunwa da take ji, ga kuma gajiya. Kanta har wani ciwo yake mata, sai bayan kusan mintuna talatin sannan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da wata jaka mai ɗan fadi, Ta buɗe back seat ta ajiye sannan ta dawo driver seat ɗin ta tada motar suka bar wajen. Har suka ƙarasa gida babu wanda ya ce komai a cikin su, Tana gama parking Nana ta fito ta nufi balcony ɗinsu da sauri, Sai dai kafin ta kai ga ƙarasawa taji an kira sunanta. Cak ta tsaya tana zumɓura baki a fili ta ce“Na shiga uku!"

Ta juya tana kallon Maimoon dake ƙarasowa wajen, Kamar zata yi kuka ta ce“mene ne dan wallahi nagaji” hararara ta zabga mata sannan ta ce“To Atta ke kiranki” haɗe rai ta sake yi sannan ta ce“to ni wallahi ba zan je ba!” daga haka ta juya ta nufi cikin gidan su da sauri. Da idanu kawai Maimoon ta bita dai-dai nan Anty Ramlah ta ƙaraso wajen, Ta gaisar da ita cike da girmamawa, Amsawa ta yi kana ta ce

“Maimoon ya jikin?”

Sunkuyar da kai ta yi sannan ta ce“Alhamdulilah Anty”

“Sannu Allah ya raba lafiya.”

Anty Ramlah ta yi maganar tana kallonta, Da amin ta amsa sannan ta ce“Anty kawo na riƙe miki kayan” waro idanu ta yi lokaci ɗaya kuma ta girgiza kanta ta ce“haba dai rufa min asiri, na wahalar da ke. Shiga ciki kawai”

Ɗan murmushi ta yi dan daman ba wani daɗin jikinta take ji ba kawai dan Atta ta takura mata ne ya sanya ta fito. Ganin tana ƙoƙarin yin gaba yasa ta ce“Aaa Anty dan Allah idan kin shiga ki saka Nana ta zo, Atta ke kiranta kuma ta ce wai ba zata je ba.” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi ta ce“Allah ya shiryi Nana, tam zan turota” okay kawai ta ce sannan ta juya ta bar wajen, ita kuma ta nufi cikin gidan.

Kwance ta sameta a parlon kan cinyar Amma, ta ajiye jakar hannunta ta zauna ta ce“wash!”

“Sannu sai yanzu?”

Amma ta tambaya tana kallonta. Jinjina mata kai ta yi kafin ta ce“wallahi Yaya, kin san sai da suka mata gyaran jiki sannan aka mata Henna da saloon. Kuma na biya gidan matar can na amso magungunan da turaren”

Amma ta ce“Shiyasa ku ka daɗe, Yanzu ku fara cin abinci sai ki ƙarasa.” zare mayafin jikinta ta yi sannan ta ce“a'a ni a ƙoshe nake wlh, Nana tashi muje” kamar zata yi kuka ta ce“Ina kuma? Ni Allah fa nagaji sosai, kaina ciwo yake.”

Harararta Amma ta yi ta ce“ɗagani ni. So ki ke kakarki ta zo ta fara azazzalata ko me? Tashi mana.” dakyar ta miƙe zaune har da yan hawayenta ta ɗauki hijabinta ta shige ciki, Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta ɗauke kanta ta ce“Allah ya shiryeki.” Miƙewa Anty Ramlah ta yi ta ɗauki jakar da ta shigo da ita sannan ta bi bayanta.

****
Ana idar da sallar isha'i Atta na shigowa parlon, Ta dinga ƙarewa ko wace kusurwa kallo kafin ta taɓe baki ta shiga kiran sunan Amma. Amma da ke kitchen ta fito hannunta riƙe da spoon da bata san ta ɗauko ba saboda kiran Attan. Ganin ita ce tsaye a tsakiyar parlon ya sanyata sakin murmushi kafin ta ce“Atta ke ce da daren nan?”

“Yo ba dole ki ganni da daddare ba, kin ƙule ƴa a ɗaki kamar zaki mayar da ita ciki. Cewa nayi da la'asar za'a kaita amma gashi har ana sallar magriba babu ita babu labarinta, to zuwa nayi na tafi da ita.” Murmushi kawai Amma ta yi dan ba zata iya da halin Atta ba ta ce“ai tana ɗaki Nanan”

Bata sake kallon inda take ba ta nufi hanyar ɗakin Nanar tana gyara mayafinta da ke sakkowa kafaɗarta. Suna zaune a ɗakin, Ban da ƙamshi babu abin da ke tashi. Wani irin sassayan ƙamshin humra ne wanda ya hadu dana turaren kwalba haɗi dana kabbasa. Ita kanta Anty Ramlah da ba ita aka sakawa turaren ba ƙamshi take, Nana na zuane gefenta ta rufe fuskarta da wani golden ɗin mayafi mara kauri, sai shessheƙar kuka take a hankali. Atta ta shigo ɗakin babu ko sallama, Turus ta yi ganinsu zaune, ta ƙarasa ciki tana kallon su ta ce

“A'a wallahi kul Ramlah ki ke ko wa? Akan me zaki riƙe min ƴa anan? Yarinya za'a sadata da ɗakin mijinta kin zo kin wani sakata a maƙata ko me ki ke ce mata ohho?”

Murmusawa Anty Ramlah ta yi tana tashi daga wajen ta ce“Allah ya huci zuciyarki Atta. Gata anan ai mun gama”

”Ku ka gama me? Hala dai ba wani mugun abun ki ka kitsa mata ba.?”

Atta ta yi maganar tana ɗage lulluɓin dake kan Nanar, Kifa fuskarta ta yi a tsakanin cinyoyinta tana ƙara volume ɗin kukanta.

Ɗago kanta Atta ke son yi amma fur taki yarda, ta saketa tana yin baya ta ce“a'a wallahi ki je dan kan ki. Tashi ni muje a kai ki ɗakin mijinki”

Tamkar ta sake tura Nana haka ta sake rushewa da wani sabon kukan, Anty Ramlah ta koma ta riƙe hannunta dake cikin mayafin ta ce“Ba na ce miki ki daina wannan kukan ba? Taso maza.”

Sake kwace hannunta ta yi tana ci gaba da kukanta. Anty Ramlah ta yi tsaki ganin tana son bata musu rai ta ce

“Ran ki zai ɓaci kuma Nana tashi na ce miki!”

Ta ƙare maganar a tsawace, Harararta Atta ta yi cikin tsawa ita ma ta ce“A'a dakata! Ya yarinya ita kaɗai ubanta ya mallaka zaki dinga mata tsawa? Ƴar da za'a lallaɓata ko kin manta gidan miji za'a kaita?”

Ko saurarenta Anty Ramlah ba ta yi ba ta ja hannun Nana ta sakko da ita daga kan gadon. Lace ne a jikinta mai kyau da tsada golden mai ratsin coffee, ɗinkin doguwar riga wadda ta kama mata jiki. Anty Ramlah ta gyara riƙon da ta yi mata bayan ta sauke mata mayafin ta ja hannunta suka bar ɗakin, Da idanu Atta ta bi su can kuma ta biyo bayansu kamar zata faɗi saboda sauri. A parlon suka sami Mama wadda shigowarta kenan don tafiya da Nana, Anty Ramlah ta miƙa mata hannunta. Riƙewa Mama ta yi kamar jira Nana take ta sake fashewa da kuka, Amma da ke tsaye ta ƙarasa gabanta. Ɗaga mayafin ta yi tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce

“Haba Nanata ki daina kin ji. Yanzu kin zama babba fa” Sake fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikin Amma ta ƙanƙameta, ita kanta Ammar kasa bata haƙuri ta yi dan ita ma kukan take, koda wasa bata yi tunanin nan kusa zata kai Nana ɗakin miji ba. Sai gashi yau zata rabu da ita, duk da ba nisa zata yi ba sai taji kamar zasu rabu ne. Anty Ramlah ce ta ƙarasa wajen ta janye Nana daga jikinta cikin son kwantar mata da hankali ta ce“Yi haƙuri mana Yaya. Idan kina kuka to ita ta ina zata yi shiru?” Gyaɗa mata kai Amma ta yi tana goge hawayenta. Mama ta sake riƙe hannun Nana tana kallon su ta ce“to Ramlah ko zaki biyo mu ne?” Girgiza kai Anty Ramlah ta yi dan ta san sai sun fara kaita apartment ɗin Hajiya Babba ta ce“a'a kawai ku je, Allah ya bada zaman lafiya.” da Amin suka amsa duka sannan suka yi waje, Atta ta bi bayansu da sauri. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa da ita, koda suka shiga gaba ɗaya sauran suna zazzaune, Papa, Abba, Hajiya Babba, Aliyu. Mama ta shiga da ita ta zaunar da ita can kusa da Hajiya Babba sannan ita ma ta nemi kujera ta zauna, Papa ya buɗe wajen da addu'a sannan aka yi salati, kafin ya fara magana ya ce“Ina Abdusammad ɗin kuma?”

“Yana hanya Papa."

Aliyu ya bashi amsa da sauri, ko rufe baki basu yi ba ya buɗe ƙofar parlon ya shigo. Nan da nan ƙamshi turarensa ya gauraye parlon, sanye yake cikin wata dakkakiyar shadda Madam gezner ash colour, Ya ɗaura hular zanna akansa. Ɗinkin babbar rigar ya amshe jikinsa sosai ya zauna akan a jikin aka ɗinka, ƙafafunsa sanye da Gucci shoes ash colour, Idan aka ce ka yi rating nasa to tabbas za'a iya bashi ɗari a ciki goma. He looks quite and elegant, Duk da fuskarsa a haɗe take babu annuri hakan bai hana kyansa bayyana ba, farar fatarsa sai sheƙi take, kana ganinsa kada ango sabon aure. Ya saki ƙofar ganin yanda suke kallonsa ya sanya ya sake tsuke fuskarsa, Kujerar da Aliyu ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaishe su ɗaya bayan ɗaya, suka amsa a sake sannan Papa ya fara bayanin da zai yi. Nasiha sosai ya yi musu daga shi har ita, kana ya yi fatan Alkhairi, Hajiya Babba ma ta yi tata maganar sannan Atta. Abba kuwa cewa ya yi bashi da abin faɗa, dan haka Mama ta rufe taron da addu'a suka shafa.
Chapter 72 · 0% Book details