← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 125

Sashe 83

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra ta ce“Nima jiya da daddare yake faɗa min, An jima ai zan zo in sha Allah.” Anty Khadijah ta jinjina kanta tana ƙoƙarin miƙewa ta ce“To Allah ya kai mu.” Tashi ita ma Zahran ta yi ta amsa da Amin sannan ta ce“Ba zaki je wajen Siyama ba?” girgiza kai Anty Khadijah ta yi ta ce“a'a yau ai ba wajenta na zo ba, Sauri nake akwai inda zan je.”

Zahra ta yi murmushi ta ce“To Anty ki gaida gida.”

“Zai ji. Dan Allah Zahra kada ki yi wasa da maganin nan!” Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi ta ce“in sha Allah Anty.” Daga haka suka sake sallama ta nufi motarta ita kuma ta koma ciki.

****
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo dakin, Ya amsa a hankali sannan ya kalleta.

“Na gama uncle.”

Ta ce tana wasa da fingers ɗinta, Jinjina kansa ya yi sannan ya tashi tsaye ya ce“okay muje” bata ce komai ba ta juya ta koma parlourn, Yabi bayanta shima. Durƙushe ya sameta gaban kayan tea ɗin data ajiye, Ta hada masa tea ɗin kamar yanda ta san yana sha sannan ta miƙa masa inda ya zauna. Ta jawo masa bowl ɗin data zuba kazar da kuma plate ɗin data zuba Irish potato ɗin data soya, Kallon ta kawai yake har ta gama ajiye komai ta tashi ta koma kan kujera ta zauna, Ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce

“Ke ina naki abincin?”

“Na ƙoshi.”

Ta ce a takaice, Haɗe rai ya yi ya ce“zo nan.” y nuna mata gefen sa, Kasa masa musu ta yi ta taso ta dawo wajen ta zauna ta sunkuyar da kanta, Ya dauko wani mug ɗin ya tsiyaya mata rabin shayin nasa sannan ya tura mata gabanta. Ita dai ba ce komai ba, Ya yi bismillah sannan ya kai tea ɗin bakinsa, Kallon sa ta dinga yi kamar ta samu tv, Ya kalleta ya ce“Wasa nake miki?” Sai a sannan ta ɗauki mug ɗin ta kai bakinta dan ba ƙaramar yunwa take ji ba, kasancewar jiya bata ci abinci ba ta zauna jiransa. Ganin shayin kawai take sha ya sanya ya ce“Ba zaki ci abincin ba?” Ya kare maganar yana tauna naman dake bakinsa, Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“Ni bana ci, na ƙoshi.”

Ya dinga kallon ta can kuma ya ce“Da ki ka ci me?”

“Ni bana ci, Ba zan ci ba."

Yanda ta yi maganar tana yatsine fuska ya sanya shi murmushi, Ya ce“Saboda me?”

Kamar zata yi kuka ta ce

“To ba ka ce idan naci kazar sai ka ci amarcin ba, ni kuma bana so. Dan haka ai ban ci kazar taka ba ko?” Ta ƙare maganar tana kallon sa hawaye ya cika kurmin idonta. Sosai ta bashi dariya amma ya dake ya ce“To ai ko kin ci ko baki ci ba ni sai naci amarcin yarinya, Dan haka it's better for you ki ci abincin ki.”

Shiru Nana ta yi tana kallon sa, nan da nan hawaye ya fara zubowa akan fuskarta. Abdusammad kuwa ɗauke kansa ya yi yana kai naman bakinsa ya fara taunawa a hankali, Yana jin yanda take shessheƙar kuka a hankali, Ya juyo yana kallonta sai kuma ya janye kanta ba tare da ya yi magana ba ya buɗe bakinta da hannunsa, A hankali kuma ya kai nasa bakin ya juye mata kaf naman dake bakinsa. Wani irin jan numfashi Nana ta yi, Ya saketa ya ɗauke kansa, Ta dinga kallon sa tana kuka kuma taƙi tauna naman, Kamar ba zai magana sai kuma ya ce

“Cinye nace”

Cikin kuka ta ce“wallahi ni ba zan ci ba. Ni bana so, Ni ka bar ni kawai!”

Ganin yanda duk ta daga hankalinta ya sanya shi yin murmushi kafin ya ce“Shikenan na fasa cinye abin ki.” Ya tura mata bowl ɗin gabanta, Kallon sa ta yi taga ya gyaɗa mata kai. Ta ɗauke idanunta hawaye na sake zubowa ta fara tauna naman, Tashi ya yi ya koma kan kujera ya zauna dan ya ƙoshi, ita kuwa gyara zamanta ta yi a ƙasan ta fara cin kazar tana lumshe ido, kasancewar naman kaza na daga cikin abin da take so. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta fara gyatsa, Dan haka ta haƙura ba dan ta daina mata daɗi ba, Ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta tashi ta koma kujerar daya zauna ta zauna ita ma, Kallon ta ya yi sai kuma ya dauke kansa ya mayar kan tv inda yake kallon aljazeera, Ta fara lumshe ido saboda ƙoshin da tayi ga kuma sanyin ac dake dukanta.

“Bacci zaki yi?”

Ta ji ya tambayeta, Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“Zo ki kwanta” ya nuna mata cinyarsa, Kamar jira take ta matsa kusa da shi ta ɗora kanta akan cinyarsa ta sanya hannayenta duk biyun ta zagaye ƙugunsa. Ta rufe idanunta tana shirin baccin ta ji ya ce

“Ki yi baccin idan kin tashi sai ki je wajensu Amma, cause gobe zamu shige.”

Cikin magagin bacci ta ce“Uncle ka bar ni anan.”

Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kansa ya ce

“Naƙi ɗin. Tare zamu tafi in sha Allah, Da a ce baki da visa ne shi ne zan bar ki amma tun da kina da tare zamu tafi.”

Tura baki ta yi tana ƙoƙarin rufe idanunta ta ce

“Ni ba ran bika ba.”

Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ja dogon hancinta ya ce“To bari muga.” bata sake cewa komai ba ta fara baccinta, Shima ɗin bai sake mata magana saboda saukar numfashinta da ya fara ji.

****
Safwan na zaune gefen gadonsa, hannunsa rike da wata farar takarda yana dubawa, Can kuma ya linke takardar ya ja idanunsa ya lumshe, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun sa. Yana nan zaune aka buɗe ƙofar dakin, bai daga kansa ba dan duk zatonsa Siyama ce, Haule ta ƙaraso ciki hannunta riƙe da ruwan gora ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta jima a tsaye ganin bai buɗe idanunsa ba ya sanya ta ce

“Hamma!”

Muryarta da yaji ya sanya shi buɗe idanun sa, Ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. Haule ta sunkuyar da kanta ta ce“Ga ruwan in ji Anty Siyama.” Jinjina kansa ya yi sai kuma ya miƙa mata hannu, Ta miƙa masa ruwan ya karba sannan ya ce“Nagode!.” bata ce komai ba taja ta tsaya, Safwan ya buɗe ledar dake gabansa ya fara zaro drugs ɗin, ɗaya bayan ɗaya ya dinga ɓalla yana sha har ya kammala. Ita dai Haule sai kallon sa take cike da tausayi, Bayan ya kammala ya ajiye empty bottle ɗin akan drawer. Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya zata fita taji ya ce

“Haulat!”

Cak ta tsaya, kafin ta juyo tana kallonsa, Da hannu ya yi mata alama da ta zo. Ta dawo gefensa ta zauna ta sunkuyar da kanta. Safwan ya dinga kallon ta ba tare da ya ce komai ba, Ita ma ɗin bata yi yunkurin yin wata magana ba, Can dai ya numfasa ya ce

“Haule ina son ki yafe min kin ji, Ki yafe min abin da na yi miki da kuma wanda zan miki, Dan Allah kin ji...”

Ya yi shiru hawaye na biyo kuncinsa, Haule da hankalinta ya tashi ya girgiza kanta tana kuka ta ce

“Babu abin da ka yi min Hamma, idan ma kuma ka yi min to na yafe maka. Wallahi ban taɓa riƙe ka ba, Na yafe maka Hamma!.”

Cikin shassheƙar kuka ya ce“Kin yafe min Haule? Har zuciyarki kin yafe min?” gyaɗa kanta ta yi tana hawaye itama. Safwan ya ja numfashi ya sauke sannan ya janyo takardar dake gefensa ya miƙa mata, Sai da taji gabanta ya faɗi, Amma ta karba ba tare da ta ce komai ba. Safwan ya jingina da jikin gadon sannan ya ce

“Ki je ki kai wa Hajiya Babba, Ko kuma Yaya Abdusammad duk wanda ki ka samu kin ji.”

Gaba ɗaya sai taji jikinta ya yi sanyi, wani irin sanyi wanda bata san dalilinsa ba, Ta miƙe hannunta riƙe da takardar ta ce“To Hamma Safwan.” yanda ta fadi sunan nasa ya sanya shi rufe idanun sa, ƙirjinsa na tsananta bugu, Ta juya ta fice daga ɗakin ya bita da kallo lokaci ɗaya kuma ya fashe da wani irin kuka kamar ƙaramin yaro. Tana fita Siyama ta shigo ta tsaya gaban gadon tana kallon sa, Ta daɗe a tsayen har sai da taji ya fara daina kukan ya koma jan numfashi sannan ta ce

“Ka sake tan?”

Gyaɗa mata kai ya yi ba tare da ya buɗe idanunsa. Siyama ta yi murmushi sannan ta ce

“Better!”.

08106608363
Nanameera.

*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 51.

Shiru Safwan ya yi bai ce mata komai ba, Siyama ta sake cewa“Yanzu ka ga sai muyi zaman mu tare, babu wadda zata sake shigowa gidan nan da sunan mata. Ni kaɗai na isheka” Jinjina kai kawai ya yi kafin ya zame ya yi kwanciyarsa akan gadon, ta daɗe tsaye a wajen kafin daga bisani ta juya ta fice daga ɗakin. Haule na fita ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba tana tafe tana tunani, Haka kawai taji zuciyarta bata yarda da takardar ba. Dan haka ta ja ta tsaya a wajen tana ƙoƙarin warwarewa, Abdusammad ta hango tsaye shi da Aliyu suna magana. Sai kawai ta fasa buɗewa ta nufi wajen da sauri, Kallon ta suka dinga yi har ta ƙaraso wajen ta gaishesu suka amsa sannan ta ce

“Arɗo daman Yaya Safwan ya ce na baka.”

Kallon takardar da take miƙo masa ya yi, Sai kuma ya kalli fuskarta. Can dai ya karɓi takardar ya warwareta.

_Ba sai na faɗi dalilina ba, amma ina son ku yafe min. Ni Safwan Muhammad Shuwa na saki Matata Haule saki ɗaya, saki biyu. Ina fatan zata yafe min abin da nayi mata, Safwan Mhd shuwa._

Da wani irin mamaki Abdusammad ya ɗago ya kalli Haule, ganin yanda tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsa ya sanyata cewa

“Arɗo lafiya? Ko wani abun ya samu Hamma?”

Bai iya bata amsa ba, Aliyu ya karɓi takardar ya karanta, Ban da innalil lahi babu abin da yake ja. Ya kalli Abdusammad wanda ya yi shiru yana tunani ya ce
Chapter 83 · 0% Book details