← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 125

Sashe 12

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiyarki? Ko an yi miki wani abun ne?" Girgiza kanta ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce"a'a kawai kaina ne yake ciwo" Jin jina kansa ya yi ya ce"okay bari na kira Sultan ya zo ya dubaki" da sauri ta ce"a'a Daddy idan na kwanta ma zai daina"

"And what are you waiting da baki kwanta ɗin ba?" Daddy ya yi magana babu yabo babu fallasa, tashi ta yi jiki a sanyaye ta bar parlon, ya bita da kallo sai kuma ya yi tsaki ya ce"i don't know what wrong with this childrens wallahi" Mami ta sauke numfashi kana ta ce"Allah dai ya kyauta" .

****
Hameed ya girgiza kansa still looking at her ya ce"amma Hajiya ni sai naga daman ba haka aka yi ba, ko mu ba za'a tambayemu ba at least a tambayi yaran, kowacce dole akwai wanda take ganin idan aka aura mata she's will be okay ko?" Hajiya Babba dake zaune kan sofa tana jan cazbaha ta ce"Yanzu da aka zaɓawa kowa mene ne ai bu Hameed? Kowacce ɗan uwanta aka bata, zata fara sonsa bayan aure, yanda zaku kyautata musu shi ne zai sanya su so ku" Hameed ya numfasa sannan ya ce"shikenan Hajiya, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi" murmushi ta yi dan daman tasan shi bashida matsala ta ce"Amin, Allah ya baku zaman lafiya" a sanyaye ya ce"Amin" sannan ya tashi , dai-dai nan Aliyu ya shigo parlon bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa suka yi sannan ya ƙaraso ya gaida Hajiya ta amsa sannan ya zauna, Hajiya ta ce"Aliyu lafiya dai?" murmushi ya yi ya ce"Alhamdulillah Hajiya, daman mun yi waya da Buddy ne ya ce gobe yana tafe in sha Allah"

Ba Hajiya Babba ba har Hameed sai da ya yi murmushi sannan ya ce"da gaske Yaya?" gyaɗa masa kai Aliyu ya yi ya ce"haka ya ce min, kuma nasan tun da ya ce haka to zai zo ɗin" Hameed ya jinjina kansa ya ce"Tom Allah ya kawo shi lafiya" da Amin ya amsa sannan ya haye sama da sauri. Hajiya Babba data kasa ɓoye farin cikinta ta ce"shi da kansa ya ce maka zai dawo ɗin?" gyaɗa mata kai Aliyu ya yi ya ce"Eh Hajiya yana nan tafe in sha Allah" ajiyar zuciya ta sauke ta ce"to Allah ya kawo shi lafiya" Amin ya ce sannan ya miƙe yana kallonta ya ce"zan je wajen Abba ya ce na faɗa masa zai zo" toh ta ce sannan ya juya ya fita.

A bakin ƙofar shiga apartment ɗin ya ganta hannunta riƙe da warmer, tana ganinsa ta sunkuyar da kanta murya na rawa ta ce"s..sannu da zuwa Yaya" ɗan murmushi ya yi ya ce"yauwa Maimuna ina zuwa?" ba tare da ta ɗago ba ta ce"Hajiya zan kai wa abinci" Aliyu ya jin jina kansa ya ce"okay kai mata ki zo ina jiranki" toh kawai ta ce sannan ta shige gidan da sauri. Ko minti biyu bata yi ba ta fito ta sameshi tsaye inda ta bar shi, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta sake sunkuyar da kanta ta ce"Yaya gani" Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce"muje to" bata musa masa ba suka fara tafiya a jere, sai dai tunaninta yana wani wajen daban, Sun kusa kai wa Apartment ɗin sannan ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin "Maimuna" saurin ɗago kanta ta yi dan duk sanda ya kirata da wannan sunan sai taji zuciyarta ta buga, ya tsaya cak yana kallonta ya ce"Are you happy or not?" kasa cewa komai ta yi sai sunkuyar da kai take, hawaye ya fara sauka kan fuskarta. Ɗan rage tsawonsa ya yi ya leƙa fuskarta ganin yanda take kuka ya sanya ya ce"haushi ki ke ji kema?" girgiza kanta ta yi, ya ce"to tell me meyasa ki ke kuka? uhm" kasa cewa komai ta yi har sannan sai kuka take a hankali, Aliyu ya sauke numfashi kafin ya ce"okay tun da ba zaki faɗa min ba daina kukan, kin ga Abba zai tambayeki me ki ke wa kuka" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta shiga share hawayenta da gefen mayafin dake jikinta. Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"to muje" daga haka suka ci gaba da tafiya.

****

Ƙarfe 9:10pm aka buɗe ƙofar ɗakin, kwance take har sannan akan gado sai hawaye take, Abba ya dinga kallonta kafin ya ƙaraso cikin ɗakin ya zauna gefen gado ya ce"Nana lafiya?" da sauri ta ɗago kanta, ganin Abbanta ya sanya ta tashi zaune, ta ƙarasa wajensa kawai ta rungumeshi tana fashewa da kuka. Abba ya dinga shafa kanta ba tare da ya ce komai ba, kuka take bana wasa ba, har wani jan numfashi take kamar zata shiɗe. Abba ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce"mene ne? faɗa min"

Cikin kuka ta ce"Abba wai aure za'a yi mana?" Da mamaki yake kallonta kafin ya ce"wane ya faɗa miki wannan maganar Nana?" Cikin shassheƙar kuka ta ce"Amma ce, Amma ta ce aure za'a yi mana" numfasawa ya yi sai kuma ya jinjina mata kai ya ce"haka ne, an kusa muku aure in sha Allah" sake fashewa ta yi da wani sabon kukan, Abba ya ce"mene ne kuma?"

"Abba ni bana son aure karatu nake son nayi, bana son nayi aure yanzu dan Allah Abba"

Ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce"in dai karatune zaki yi a gidan mijinki, amma nan ba da jimawa ba zaki yi aure Nana"

Tashi ta yi daga jikinsa, ta sauko daga kan gadon ta tsuguna a gabansa tana kuka ta ce"dan Allah Abba kada ka bari a yimin aure yanzu, ka bari nayi karatu Abba, bana son aure wallahi"

Bai ce komai ba sai kawai ya tashi ya fice daga ɗakin, Nana tabi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da wani kukan tana dafe kanta.

Daren ranar babu wanda ya yi bacci wadatacce a cikinsu, kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa, kowacce da irin nata matsalar. Nana kuwa kwana tayi tana kuka, sai da aka fara kiran sallar asuba sannan ta tashi ta yi sallah ta shiga rokon Allah akan ya hana su haɗa auren nan da ita domin ko kaɗan bata son ta yi aure da yarinta. Washegari ya kasance asabar, dan haka babu wanda ya fita daga mazan gidan har mata, tana ta kwance har ƙarfe goma kafin kiran Junaid ya tayar da ita, kasa ɗaukan wayar ta yi dan tasan bata da wani amfani. Ta dinga kallon wayar har kiran ya katse, ganin wani sabo ya shigo ya sanya ta kashe wayar gaba ɗaya, ta sake fashewa da kuka. Amma ce ta shigo dakin tana sanye da wata doguwar riga ta lace, ta dinga kallonta kafin ta ce"da kin tashi shi ne baki fito ba?" shiru ta yi bata ce komai ba, Amma ta sake cewa" ki tashi ki fito zan aikeki" ji tayi kamar ta zunduma ihu ta cewa Amma ba zata je ba, dan ko kaɗan bata son fita daga ɗakin, amma babu dama, dan haka ta tashi ta shige toilet ɗinta ta yi wanka a gurguje ta fito. Doguwar rigar yadi ta sanya sannan ta dauki hijabi har ƙasa ta saka ta fito, zaune ta sami Abba a parlon yana karatun news, ta gaishe shi a sanyaye ba kamar yanda ta saba ba, amsawa ya yi shima kuma bai sake bi ta kanta ba ya ci gaba da abin da yake, Amma ta fito daga kitchen tana kallonta ta ce"ki je wajen Mama ki ce wai gaki" shiru Nana ta yi bata amsa ba kuma bata tafi ba, Amma ta zabga mata harara kana ta ce"baki ji ne ina magana" waje ta yi ba tare da ta amsa ba, Abba ya bita da kallo har ta fice sannan ya kalli Amma ya ce"ki bita a hankali" bata ce masa komai ba ta koma kitchen ta ci gaba da aikin da take.

Tafiya ta dinga yi a hankali tana tunane-tunanenta, har suka ƙaraso gabanta bata sani ba, sai da Maimoon ta riƙe hannunta sannan ta ɗago kanta da sauri tana kallonsu, kowanensu idanunsa a kumbure yake, basu ce mata komai ba suka ja hannunta suka ci gaba da tafiya. Har suka je garden ɗin babu wadda ta ce komai, ita dai Nana bin su take da kallo har suka shiga ciki, sai a sannan Maimoon ta saki hannunta ta ce"kin ji abin da ya faru ko?" gyada mata kai ta yi sannan ta ce"ke wa zaki aura?" shiru Maimoon ta yi bata amsa mata ba, ta juya ta kalli Hameeda ta ce"kefa Hameeda?" madadin ta amsa mata sai kawai ta fashe da kuka, ta faɗa jikinta, duk yanda Nana take jin jikinta babu kwari haka ta riƙe Hameeda itama kawai sai ta fashe da kuka. Amrah ce tayi ƙarfin halin cewa"ku daina wannan kukan kar wani ya zo ya ganmu" a fusace Nana ta ce"to a gani ɗin, wallahi ni ba zan auri wani ba idan ba Junaid ba! sai dai na mutu babu aure na rantse, amma ba zan auri wani ba idan ba shi ba!"

Kallonta suka dinga yi babu wanda ya tanka, Amrah ta dafa Hameeda dake kuka kamar ranta zai fita ta ce"da a ce za'a bar ni, da a ce zan iya dana bar miki Yaya Sultan Hameeda, wallahi da sai na barki kin aureshi, ni auri koma wane, domin nima ba shine zaɓin zuciyata ba, bashi nake so ba!" Da sauri Hameeda ta kalleta cikin kuka ta ce"na sani Amrah, na san zaki iya bar min shi, ko kaɗan ban ga laifinki ba, kawai zuciyata ce ta kasa yarda, na kasa haƙura dashi, ji nake kamar mafarki nake, kamar zan aure shi, amma na san har abada hakan ba zai faru ba, Allah ba haka ya so ba, bai ƙaddara ya zama mijina ba, Yaya Hameed shi ne zaɓin Allah kuma zaɓin iyayena" da sauri Nana ta ce"Amrah Yaya Sultan za ki aura? Ke kuma Hameeda Yaya Hamid za ki aura? To ke kuma fa Maimoon?"
Chapter 12 · 0% Book details