← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 125

Sashe 24

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“saurayina ne, malamin mu ne a Aun, tun ina jss muke tare, at first na ɗauka kyautatawa ce kawai tsakaninmu, dan tun da ya zo school ɗin ban sake rasa wani abu ba, shi ne yake koya min karatu idan ban iya ba, shi ne yake sakani na gyara kuma ya hanani ba dai-dai ba. Sai da muka zo senior sannan ya faɗa min abin da ke ransa, to nima daman ina son shi a sannan ɗin, duk da ban san mene ne son ba, amma naji yana burgeni, kuma naji ina son na aureshi. Dan haka muka fara soyyaya dashi sosai, kullum sai mun haɗu a Aun, saboda ni yaƙi barin makarantar duk da iyayensa sun yi kokarin saka shi yin haka, a kwana a tashi naji son shi na ƙaruwa a zuciyata, duk da a lokacin nasan mataki da kuma tsarin gidanmu, amma a duk lokacin da naji ina son na bar shi sai naji zuciyata tana yimin zafi, sai naji numfashina na ƙoƙarin barin ƙirjina. To a sannan na gane ba zan iya rabuwa da sir Junaid ba, ba zan iya barinsa ba, dan haka na ɗauki aniyar sai na aure shi koda hakan na nufin zan ɓata da kowa, ma ɗauki aniyar sauya al'adar danginmu, yanda za'a dinga bawa kowace yarinya yancin auren wanda take so. Za'a daina mana auren haɗi, domin yawanci ba wanda ka ke so ake baka ba, dan haka ni sir Junaid nake son aure, kuma sai na aureshi!”

Ta ƙare maganar tana shessheƙar kuka, Zahra ta dinga kallonta tana nazarin kalamanta, she just can't believe a ce Nana ke faɗar irin wannan maganar, magana irin ta manya cike da nutsuwa. Ta numfasa kafin ta ce

“kenan kina shirin tarwatsa dangin ku? Kin yarda ki zama almakashin da zai datse zumuncin da ke cikin dangin ku? Kin yarda ki zama wadda iyayenta zasu yi Allah wadai da haihuwarta? Kin yarda ko Nana?”

Girgiza kanta ta yi still crying ta ce“a'a Aunty, bana son na tarwatsa zumunci kawai ina so...”

“kawai me Nana? Shirin ki na auren bare dai dai yake da tarwatsa dangin da iyayenki suka sha wahala wajen samar dashi, kin san mene ne zumunci kuwa Nana? Kin san girman da yake dashi? Kin san falalar da take cikinsa? Kin san yanda ubangiji ke kallon duk wanda ya sadar dashi? Mene ne yake damunki Nana? Yarinta? Ko kuma wannan ba yarinta ba ce son zuciya ce, tun da har ki ka gane ki lalata zumuncin Allah to tabbas son zuciya ce a cikin lamarin ki.”

Ban da kuka babu abin da Nana ke yi, ta ɗago runannun idanunta tana kallonta ta ce“to aunty ya zan yi? Na bari na auri wanda bana sonsa? Na bari a lalata min farin ciki? Na yi shiru ina gani”

Jinjina kai Zahra ta yi ta ce“eh ki yi shiru, domin babu wanda ya taɓa bin iyaye kuma ya taɓe, Nana kin san wani abu?” girgiza kai ta yi, Zahra ta gyara zama sannan ta ci gaba da faɗin

“idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin raba tsakanin ki da Abba ne, saboda Abba ma ɗaya daga cikin ƙashin bayan wannan zumuncin, su ne suka assasa shi, suka sanya ake auratayya a tsakani saboda a samar da tsaftacen dangi da babu bare a cikinsa. To i dan har ƴar sa zata bijire me hakan ke nufi? Kina son tozarta mahaifinki ne, kina son lalata farin cikin wanda ya fifitaki fiye da komai, wanda yake ɓata lokacinsa da ƙarfinsa domin samar miki da abin da ki ke buƙata, wanda yake baki komai ba tare da ya miki gori ba, idan ki ka raunata zuciyarsa kina nan kin yi dai dai kenan? Kina ganin zai yi alfahari da ke? Ke kaɗai ce yarsa dan haka duk wata taƙama da uba ke yi akan yayansa ke dake kaɗai yake da wannan damar, idan har ki ka ƙi wannan auren tamkar kin wulaƙanta shi ne a idon duniya, kin nuna ce shi bai isa da ke ba, ballantana har wasu su ga girmansa su girmama hukucinsa. Idan har kina ganin wannan shi ne abin da ki ka zaɓa shikenan Nana, ba zan takura ki, ba kuma zan miki dole ba, amma idan da ni ce a matsayin ki...”

“za ki haƙura da Junaid domin kare martabar mahaifin ki da kuma dangin ki”

Zahra ta gyaɗa mata kai, ta runtse idanunta tana hawaye ta ce

“to nima zan yi hakan aunty, zan bar wanda nake so domin kare martabar Abbana, ba zan taɓa yin abin da zai sanya shi a damuwa ba, nayi alƙawarin zan zame masa farin ciki, ba zan saka shi takaici ba, ba zan bari a daina ganin girmansa ba, na haƙura da Junaid aunty, na haƙura dashi na haƙura Aunty...”

Zahra ta dinga kallonta cike da farin ciki, ta tashi ta ƙarasa gabanta ta tsuguna sannan ta kama hannayenta ta riƙe cikin nata ta ce“da gaske Nana? Kin haƙura dashi? Ba zaki sake kula shi ba? Ba zaki sake shiga harkarsa ba?”

Jinjina mata kai Nana ta yi ta ce“eh aunty, na bar shi wallahi na haƙura, ba zan sake ɗaga maganar ba”

Zahra rasa abin yi ta yi sai kawai ta tashi ta rungumeta tana murmushi ta ce“Allah ya yi miki albarka Nana, ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, ya haɗa ki da mai ƙaunar ki wanda ba zai ɓata miki ba, wanda zaki so shi fiye da tunanin ki”

Ƙanƙameta Nana ta yi sannan ta ce“amin aunty, Nagode, Amma dan Allah kada ki faɗawa uncle ko Abbana”

Ɗagota ta yi daga jikinta tana murmushi ta ce“har abada ba zan taɓa faɗawa kowa ba Nana, ki ɗauka mun rufe wannan maganar a nan”

Jinjina kai ta yi cike da farin ciki ta sake rungumeta tana fadin “nagode auntyna, Allah ya bar mana ke” Zahra ta yi dariya ta ce“amin tare da ke Nanarmu”.

****
Wani irin banza kallo ya dinga masa kafin ya ce“amma dai an yi banza wallahi tallahi, yarinyar ta baka dama sannan ka yi wasa da ita? Ashe ba sonta ka ke ba daman, ba ƙaunarta ka ke ba, a baki ne son wallahi” taɓe baki Junaid ya yi ya ƙarasa kan sofa ya zauna hannunsa riƙe da coffee ya ce“kai dai baka san abin da ka ke ba, yarinyar da nake son na aureta mu samu zuri'a mai kyau da tsafta ita ce zan gudu da ita? Na aureta bada yardar iyayenta ba? Kidding!”

Zama shima Al-ameen ɗin ya yi ya ce“to mene ne shirin ka? Taya zaka sameta bayan kasan babu wata hanya?”

Ɗan murmushin baka san me ka ke ba ya yi masa kafin ya ce“ba dole ba ne na faɗa maka shirina, but when it goes well zaka ji” murmushi Al-ameen ya yi ya ce“daɗina da kai kwanya, dan Allah ka faɗa min mene ne plan ɗin”

Sai da ya yi sipping coffee ɗinsa sannan ya ja gajiyayyun idanunsa ya rufe yana sauke numfashi a hankali, Al-ameen ya ce“ka faɗa min mana dan Allah”

“ba fa zaka ji ba yauwa!” cewar Junaid yana kallonsa, taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce“to ka ci kanka”

****
Ana idar da sallar isha'i suka shigo cikin estate ɗin, Nana ta dinga kallon jama'ar da ke fitowa daga cikin masallacin har idanunta ya sauka akan Abbanta dake tsaye suna gaisawa da Abbansu Hamida, ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“Uncle a sauke ni anan” yana ƙoƙarin parking ya ce“akan me?”

“Abba na hango zan bi shi”

Ta ce a sanyaye. Gyaɗa kansa ya yi sai kuma ya ce“to sauka” ya yi maganar bayan ya ƙarasa parking ɗin. Buɗe handle ɗin motar ta yi ta sauka, babu wanda ya ce komai a cikinsu ta juya ta nufi inda ta hango Abban. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya ci gaba da driving ɗinsa.

Sai da taga ya baro cikin mutane ya nufi hanyar gida sannan tabi bayansa a hankali har ta iske masa dan ba sauri yake ba

“Abba”

Ta kira shi a sanyaye, cak ya tsaya kafin ya jiyo yana kallonta, mamaki ne ya kama shi ya ce“Nana daga ina ki ke?” tana kallonsa ta ce“tare muka dawo da uncle” jin jina kansa ya yi dan sai sannan ya tuna ya ce masa sun fita da Zahra. Ya ce“to tawo mu tafi” ya yi maganar yana miƙo mata hannunsa na dama, ɗora nata tayi akai sannan suka ci gaba da tafiya. Babu wanda ya ce komai a cikinsu, sai dai kowa da abin da yake tunani cikin ransa, shi yana tunanin yanda zai hanata faɗa da mutane, ya yinda take tunanin maganganu da Zahra ta faɗa mata ɗazu. Ta ɗaga idanunta tana kallonsa ba tare da ya sani ba, tabbas ta yi gaskiya, Abba bai cancanci wulakantawa daga gareta ba, bayan duk irin so da ƙaunar da yake nuna mata, bai cancanci ta bijire masa ba, domin bai taɓa zaluntar ta ba. To amma me ya sa take jin zuciyarta kamar ba zata iya haƙura da Junaid ba? Ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da tunanin daga ranta, domin ta bar shi har abada.

Koda suka shiga gidan basu sami kowa a parlon ba sai tv kawai dake kunne, bai saki hannunta ba ya nufi ɗakinsa, ita ma bata yi kokarin janye hannun ba ta bi shi ɗakin. Ɗakin was neat and organized, komai na ciki a tsaftace yake, ta kalli kan gadonsa wanda ya sha gyara farin bedsheet ɗin sai kyalli yake, sakin hannunta ya yi ya nufi wajen gadon, ta dinga kallon ɗakin tana tuna how long rabonta dashi, wajen study table ɗinsa ta ƙarasa ta dinga kallon tarin awards ɗinsa da kuma certificate as a MD of M-Shuwa group of companies, daga can be gefe ta hangi wasu sticky notes ta kai hannunta ta dinga tabawa kafin ta ce“laaa Abba kana da rubutuna har yanzu? Ni na rasa su” ajiye abin da ke hannunsa ya yi ya ƙaraso wajen ya tsaya a bayanta yana murmushi idanunsa ƙur akan note ɗin farko inda ta rubuta “Abba's first born” ɗayan kuma ta saka “world best Daddy”
Chapter 24 · 0% Book details