Sashe 65
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Daddy ya yi ya ce“to ki daina tsoron kowa. In sha Allah komai ya zo ƙarshe, zamu zauna dasu gobe a san yanda za'a yi kinji” gyada masa kai ta yi, Ya sanya hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya ce“tashi ki je ki kwanta” Toh kawai ta ce sannan ta tashi a sanyaye ta haye. Khadijah ta miƙe tana shirin bin bayanta ya ce“ku kwanta da wuri saboda da wuri nake son mu tafi yanda zamu tadda kowa a gida” ta amsa masa da toh sannan tabi bayansa. Sai da suka bar wajen sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Mami ya ce“ta bani tausayi, she's still young girl” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“sosai. Dan ko Mimi ta girmeta, she's just 17 fa” Daddy ya girgiza kansa ya ce“shiyasa, sam bata da wayo” Jinjina kai Mami ta yi ta ce“Eh nima na lura da haka.”
Koda suka shiga ɗakin zama suka yi suka ci gaba da rera kukansu a tare. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shiru dan kansu, Khadijah ta ce“Daddy ya ce mu kwanta da wuri yanda zamu iya tashi da wuri” toh kawai Nana ta ce a sanyaye sannan ta kwanta a hankali tana lumshe ido. Khadijah ma kwanciyar ta yi a ɗaya side ɗin dan daman sun gama shirin kwanciyar ta ja duvet ta rufe jikinta.
****
Da idanu ya dinga kallonsu sai kuma ya ɗauke kai, Aliyu ya kalli Maimoon dake tsaye a jikinsa ya ce“zaki iya shiga gidan?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh Yaya” Ya saketa sannan ya ce“Tom jeki ki huta kafin nazo” ta gaishe da Abdusammad ya amsa sama-sama sannan ta shige gidan. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya gyara tsaiwarsa yana ƙarewa compound ɗin kallo iska mai daɗi sai kaɗawa take a hankali, Ya ɗan yi jim sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke ta murmushi fuskarsa kamar gonar auduga, Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanu ya ce
“Lafiyarka dai?”
Madadin ya bashi amsa sai kawai ya ga ya ruƙunƙumeshi yana dariya, Abdusammad ya riƙe hannunsa ya ce“A'a wallahi nutsu, kar ka illatani” ɗago kansa yayi yana murmushi ya ce
“Buddy guess what?”
Ɗan juya idanunsa ya yi sai kuma ya ce“ni ban gane ba, kawai ka faɗa min”
Aliyu ya fara jan fingers ɗinsa kamar mace ya ce“soon zan zama father”
Ware idanu Abdusammad ya yi, lokaci ɗaya kuma ya saki wani kyakkyawan murmushi wanda ya daɗe bai yi irinsa ba. Ya kai masa duka yana fadin “amma kai akwai ɗan iska wallahi, har yaushe aka kawo maka yarinyar har ka mata ciki?” Harararsa Aliyu ya yi kafin ya ce“to mene ne a ciki? Ba dai matata bace?”
Ɗauke kai Abdusammad ya yi ya ce“ɗan iska kawai. Daman ni tun da naga kana wani maƙalƙale mata baka ko fita waje na san ba zaka shuka abin arziki ba. Kawai ka saka yarinya ta rainaka”
Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi sai kuma ya ce“nima kenan, kai naga yanda zaka yi”
Haɗe rai Abdusammad ya yi kamar bashi ba ya ce“kamarya ni? Da aurena da mutunci na” Dariya Aliyu ya yi ya ce“kai mana. Allah ne kaɗai ya san abin da zaka yiwa ƴar rainon taka idan an kawota, wa yaga show”
Wani mugun kallo ya watsa masa, ya ƙara masa da harara sannan ya yi tsaki ya ce”aikin banza. Kai daɗina da kai baka da hankali wani lokacin”
Ban da dariya babu abin da Aliyu ke yi, Ya dafe cikinsa sannan ya ce“daga faɗar gaskiya? Allah ya nuna mana to” wani dogon tsaki yaja ya yi gaba dan ba zai ma iya zama a wajensa ba ya ce“Allah ya baka sauƙi” Aliyu ya amsa da Amin yana dariya har sannan. Ganin ya yi gaba abin sa yasa shima ya juya ya nufi cikin gidansa. Ya yi nisa yaja ya tsaya maganar Aliyun na masa yawo a ƙwaƙwalwa, yaja wani sabon tsakin yana ayyana ta inda zai iya wata mu'amala da Nana, yarinyar da yake ma kallon yarsa. Saurin kawar da tunanin ya yi a fili ya ce
“Astgfirullah”
Sannan ya yi gaba yana sake girgiza kansa.
****
Washegari da sassafe around 7:00am suka gama shiri cikin wata atampa glitter da Mami ta ɗinka musu. Ko powder babu wadda ta shafa a cikinsu dan duk jikinsu a sanyaye yake, suka fito parlon suna jiran Daddy. After 5mins ya fito yana gyara zaman babbar rigar jikinsa Mami na biye dashi da kuma Adeel, Tsaye ya samesu suka gaisheshi ya amsa cike da fara'a sannan ya maida idanunsa kan Mami ya ce“to sai mun dawo ko” murmusawa ta yi ta ce“Allah ya dawo daku lafiya.” sannan ta ƙarasa inda suke tsaye ta dafa Nana ta ce“daughter sai yaushe?” rungumeta Nana ta yi ta fara kuka ƙasa-ƙasa. Mami ta ɗagota tana goge mata hawayen ta ce“haba dai kuka, shikenan kuje Allah ya tsare.”
Cikin shassheƙar kuka ta ce“Mami yaushe zaki zo?” murmushi Mami ta yi kafin ta ce“nan kusa in sha Allah kinji.” Toh kawai Nana ta ce sannan Daddy ya ce“to idan kun gama muje kun san jirgi baya jira” sakinta Mami ta yi tana musu Allah ya tsare, Khadijah ta rungumeta ta ce“sai mun dawo Mami” Allah ya tsare ta ce sannan tabi bayansu Daddy da suka yi waje. Adeel ne yaja motar kai tsaye kuma filin tashin jirage na Malam Aminu Kano suka nufa, basu daɗe ba kuma jirginsu ya tashi zuwa Yola.
08106608363,
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 40.
Tafiyar awa ɗaya ce ta kawo su Adamawa, jirginsu ya sauka a filin tashin jirage na Yola international airport. Bayan sun fito daga airport suka shiga mota dan already Daddy ya yiwa wani friend ɗinsa magana akan zuwansu, kai tsaye kuma M-Shuwa Estate suka nufa. Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Nana ta yi nisa cikin tunani, gabanta sai faɗuwa yake. Tsoronta ɗaya abin da zai faru idan ta koma gidan, Khadijah dake danna wayarta a hankali ta dinga kallonta time to time a haka har suka ƙarasa estate ɗin. Sai da suka tsaya a bakin gate ɗin wajen securities kafin suka basu damar shiga da motar ciki. A compound ɗin su Nana suka yi parking, saboda mutanen da suka hango tsaye, Nana ta ɗan waro idanunta tana son ganin su wane a tsaye, sai dai kai tsaye ba zata ce gasu ba saboda sun juya baya. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe motar ya fito, Sai a sannan Khadijah ta kalleta ganin bata da shirin sauka ta ce“Nana mun zo fa” numfasawa ta yi sai kuma ta gyaɗa mata kai. Khadijah ta buɗe side ɗinta ta fito tana gyara zaman mayafin jikinta, A sanyaye Nana ta buɗe motar ta fito tana riƙe da wayarta. Ganin Daddy ya yi gaba ya sanya ta kalli Khadijah kamar zata yi magana sai kuma ta yi shiru, Daddy kuwa wajensu Abba ya ƙarasa da suke tsaye shi da Papa da Abdusammad. Sallama ya yi musu suka amsa sannan suka gaisa fuskarsa a sake ya ce
“Yallabai wajenka nazo” ya yi maganar yana kallon Abba dan ya riga da ya san shi. Murmusawa shima Abba ya yi ya ce“Tom Alhaji muje ciki” jinjina kansa ya yi sannan ya juya ganin yanda suka cake ya ce
“Ku tawo mana”
Maganar ta sanya hankalinsu kai wa inda su Nana ke tsaye, cikin rashin sa'a idanunta ya sauka cikin na Abba. Wani irin abu taji ya zo mata wuya, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. Abba ya haɗiye wani miyau mai ɗaci sannan ya kalli Daddyn Khadijah murya a shaƙe ya ce
“lafiya dai Alhaji?”
Dafa shi Daddy ya yi ya ce“idan mun shiga ciki zaka ji” shiru kawai Abba ya yi yana kallonsa, Jiki a sanyaye suka ƙaraso wajen, barin Nana data sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta kalli Papa ta gaishe shi. Da murmushi a fuskarsa ya amsa, dan har ga Allah yaji daɗin ganinta, Ta saci kallon Abdusammad wanda ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, a hankali ta sunkuyar da idanunta sannan ta gaishe shi. Ba zaka taɓa cewa dashi take ba, dan ko motsi bai yi ba ballantana ta saka ran yaji abin da tace. Ta ɗan yi shiru tana jin hawaye na neman zubowa kan fuskarta, ta kalli Abba wanda ke kallonta sai kawai ta tafi zata shige jikinsa. Ɗaga mata hannu ya yi wanda ya sanyata dakatawa, cikin kakkausar murya ya ce
“Kar ki kuskura!”
Ya faɗi maganar yana nufar cikin gida kamr zai tashi sama. Daddy ya sauke numfashi sai kuma ya kalli Papa da Abdusammad ya ce“muje ciki kuma dan Allah” toh Papa ya ce masa, Abdusammad kuwa girgiza kansa ya yi ya ce“sorry ku je kawai” Daddy ya ɗan murmusa kafin ya ce“Da ka yi haƙuri mun shiga cikin” ya buɗe baki zai yi magana Papa ya riƙe hannunsa ya ce“muje” daga haka suka nufi cikin gidan. Daddy ya juyo yana kallonsu ganin Nana sai kuka take ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce“kar ki damu komai zai shige kin ji." Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta daina kukan ba, Ya kalli Khadijah ya ce“ku samu guri ku zauna ko ku koma mota kafin mu gama” toh kawai ta ce masa sannan ta riƙe hannun Nana. Ya juya ya nufi gidan shima. Kalle-kalle ta fara yi can ta hango wata bukka ta zamani nesa dasu kaɗan, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ja hannun Nana suka ƙarasa wajen. Zama ta yi sannan ta saki hannunta, Nana ta ja kujera ta zauna ta ɗora kanta kan table ɗin wajen ta ci gaba da kukanta a hankali.
****
A parlourn kuwa Abba ne zaune kan sofa sai Abdusammad a kusa da shi, ɗaya kujerar kuma Papa ne zaune. Daddy kuma na zaune kujerar dake facing ta Abba idanunsa maƙale a kansa ya ci gaba da fad'in