← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 125

Sashe 34

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Khadijah ce ta ce“yauwa Amal daɗina da ke hankali, su ai basu gane hakan ba, idan yanzu Siyama ta auri ɗan dangin nan ai kin ga mun ƙara yawa, sunanmu zai daukaka mu ma” murmushi Amal ta yi ta ce“wallahi fa Aunty, ai ki saka ran ki a inuwa da tuggu da makirci sai ya aureta wallahi sai dai idan bai shigo hannunmu ba” tsaki Safeena ta yi ta ce“to sai naga a lokacin da har zai shigo hannun naku bare kuma ya yarda ya auretan, yanzu haka nan da wani satin ma shi ya yi aurensa” wata dariyar mugunta Siyama ta yi sai kuma ta ce“to ai shi tuni yana hannu bari ki ji ba'a shiga dawa dan ƙarya, ko yanzu na kira shi a waya nace masa gani a gidansu ya zo wallahi sai ya zo” ba Safeena kaɗai ba har Zahra sai da ta yi mamaki, ta kalleta a sanyaye ta ce“Siyama me ya sa? Akan me ki ke son dole sai kin shiga tsakanin zumucin su? Mene haka dan Allah?” yanda ta yi maganar cikin sanyin murya ya sanya Aunty Khadijah yin tsaki kafin ta ce“ni ba wannan ba yanzu za ki taimaka ayi maganar nan ko ba zaki yi ba?”

Zahra ta girgiza kanta ta ce“a'a gaskiya ni ba zan jawo abin da zai dameni ba, kudai ku ke ku yi ta yi”

Shiru Aunty Khadijah ta yi tana tunanin yanda zata yi, ashe daman mutumin ƙarya yake mata? Ya ce idan ta tambayi Zahra ba zata bijire ba, sai ma ta fi kowa ɗaukan abun da gaske, but why?.

“Danƙari!”

Ta ce a ranta, amma sam bata yi tunanin duk sun ji maganar ba, Zahra ce ta sake cewa“ni dai dan Allah dan Annabi ku bar wannan maganar, ni wallahi dana san irin abun da zai faru kenan da ban zo ƙasar nan ba, wannan wace irin masifa ce?!”

Taɓe baki Amal ta yi sai kuma ta ce“haba Yaya Zahra ke baki son ci gaban gidanku sai na wani gidan?”

Miƙewa tsaye Zahra ta yi a fusace ta ce“ke kar ki ɓata min rai Amal! Ni idan wannan abun ne ya kawo ku to gaskiya nagode da ziyara ku tashi ku tafi!”

A fusace ita ma Aunty Khadijah ta ce“iyee wato korarmu ki ke daga gidan ki ko Zahra? Korarmu ki ke” ɗauke kai Zahra ta yi ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce“ni in dai irin wannan maganar ce ta kawo ku to wallahi gara ku tafi, dan banga amfanin zuwan naku ba!” ta ƙare maganar tana wara hannayenta. Jin jina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh lallai kin isa! To bari ki ji zamu tafi amma wallahi tallahi sai Siyama ta auri Safwan koda hakan na nufin ke zaki bar gidan!”

Da wani irin expression Zahra ke kallonta sai kuma ta yi murmushi yaƙe ta ce“to Allah ya baki sa'a Aunty, Allah kuma ya tabbatar?” daga haka ta yi hanyar sama fuu ta bar su tsaye.

Tashi itama Safeena ta yi tana kallonsu rai ɓace ta ce“gaskiya wannan ba adalci bane, akan me za'a lalata auren wadda take ciki saboda na wadda ba'a yi ba? Wannan gaskiya ba adalci bane! Kuma Allah ba zai bar ku ba wallahi” daga haka ta ɗauki gyalenta ta yi sama da sauri itama.

Zaman daɓaro Aunty Khadijah ta yi akan kujera tana tunanin mafita, yanzu ya zata yi da Zahra? Ita ce makamin da zata riƙe domin ganin auren nan ya yiwu amma gashi sam taƙi bada haɗin kai, wayarta ta zaro ta shiga danna kira sannan ta kai wayar kunne, ringing ɗaya ta ɗauka kafin ta yi magana Aunty Khadijah ta yi saurin katseta ta hanyar faɗin

“Kaddu ni wannan mutumin zai cuta? Ni zai yaudara? To wallahi ƙarya yake” Kaddu dake kwance kan gadon hotel ɗin ta tashi zaune tana faɗin “mene ne ya faru? Ki min bayani yanda zan gane”

“Kaddu Zahra taƙi aminta da buƙata ta, tama ƙi saurarena ke ƙarshe ma dai korata take daga gidanta”

Girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“haba da sake wallahi, ita ta isa, na rantse miki ko kaffara ba zan yi ba akan dole ta yi biyayya, sai dai idan ba wajensa muka je ba, ki jira kawai ki ga da kanta zata dawo tana baki haƙuri wallahi yanda zata yi a maganar auren nan ke ba zaki iya yi ba, kawai ki zuba mata idanu”

Numfasawa Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“amma hankalina ya ƙi kwanciya Kaddu, na kasa samun sukuni sauran sati ɗaya fa bikin”

Tsaki tayi ta ce“ko ranar ɗaurin auren ne sai ya auri Siyama, kuma ki jira ki gani” Okay kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta dago kanta ta kalli su Siyama da ke tsaye cirko-cirko ta ce“ku tashi mu tafi” okay kawai suka ce sannan ta tashi itama suka fice daga parlon.

Acan sama kuwa Zahra ce zaune gefen gado tana hawaye, Safeena dake kusa da ita ta dafata a sanyaye ta ce“dan Allah dan Annabi Aunty ki yi haƙuri, Allah yana tare da ke babu abin da suka isa su yi” cikin shessheƙar kuka Zahra ta ce“tsoro nake ji Safeena, babu abin da Aunty Khadijah ba zata iya ba domin biyan buƙatarta, tana iya kashe min aure indai Siyama zata auri Safwan, ni ba wannan ne ma abin da ya dameni ba, yanda take ƙoƙarin sakani ciki shi ne abin da yafi daga min hankali. Ya zan yi Safeena? Ta ina zan fara ƙoƙarin haɗa Safwan da Siyama? Bayan kuma Nana zai aura, Nana fa, ba zan taɓa iya ruguzawa Nana aurenta ba wallahi, ba zan iya ba, Nana bata cancanci haka daga gareni ba, ita ɗin tamkar ƙanwa take a wajena, idan har zan iya hanaki aure na tozarta ki to tabbas zan iya yiwa Nana haka, kinga ko ba zan taba iyawa ba!”

Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Girgiza kai Safeena ta yi itama tana kukan ta ce“nasani Aunty, na san baki da zuciyar mugunta, dan haka kawai ki riƙe addu'a, nima zan tayaki sannan zan faɗawa Umma” da sauri Zahra ta kalleta sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a kar ki faɗa mata, domin zata ci gaba da ganin baƙin Aunty Khadijah ne, ni kuma ba zan zo haka ba, kawai ki bari Allah ya san yanda zan yi dasu” jinjina kai Safeena ta yi sai kuma ta ce“to Aunty”..

****
Fitowarta kenan daga toilet taji ringing ɗin wayarta, ta ƙarasa kan drawer tana kallon mai kiran, sabuwar number ce dan haka ta goge ruwan hannunta sannan ta dauki wayar, Muryar wanda taji ya sanya ta runtse idanunta, lokaci ɗaya ta ji zuciyarta na wani bugawa da ƙarfi, cikin sanyin murya Junaid ya ce

“tun ɗazu ina ta kiran ki da lambata shi ne ba zaki ɗaga ba ko Nana?”

Shiru ta yi masa, bai damu da shirun nata ba ya ci gaba da faɗin

“shikenan faɗa min kin sauya shawara ko kuwa har yanzu kina nan akan waccan maganar ta ki?”

Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dake ta ce

“Eh ban sauya ba, ko da kana tunanin zan sauya ne? To ka sani har abada ba zan taɓa sauyawa ba! Ba zan dawo gareka ba! Na bar ka, bari irin na har abada”

Lumshe idanunsa ya yi nan take hawaye suka zubo daga cikinsu, ya jinjina kansa yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“okay, shikenan Nana, Allah yasa haka ne mafi Alkhairi, sai dai ina neman wata alfarma a wajen ki koda zata zama alfarma ta karshe da zaki iya min”

Ban da hawaye babu abin da Nana take, ta jinjina kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“ina ji”

“Akwai wani hanky da ki ka taɓa bani kin tuna? To ina son na dawo miki dashi ne, ina waje ko za ki iya fitowa ki karɓa?”

Shiru ta yi kamar me tunani can kuma ta ce

“okay”

Daga haka ta katse wayarta, hijabi ta ɗauka har ƙasa ta saka sannan ta fito daga dakin, koda ta zo parlon bata samu kowa ba dan haka kawai ta yi waje abin ta, da sauri ta dinga tafiya har ta ƙaraso wajen estate ɗin. Ta yiwa mai gadin wajen murmushi da yake mata magana sannan ta ce“bari na karbo sako” to ya ce sannan ta buɗe gate ɗin ta fita.

Tsaye ta hangi wata Camry blue colour ta yi parking sai sheƙi take, kamar me tsoron ƙasa haka ta dinga takawa har taje gaban motar, Junaid ya buɗe driver side ɗin ya fito ya zagayo inda take yana kallonta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, ya jingina da motar yana murmushin ƙarfin hali ya ce“Nana kin rame” kallonsa ta sake yi a ranta ta ce

“har kura ce zata cewa kare maye?”

Dan shima ya ƙaramar rama ya yi ba, a fili kuma ta ce“bani zan tafi” ɗan murmushi ya sake yi ya ce“ba zamu gaisa ba?”

“idan babu abin da zaka bani zan koma ciki dan ina da abin yi”

Ta yi maganar a ɗan fusace, numfasawa ya yi sannan ya buɗe side ɗin da yake tsaye ya dauko yar ƙaramar jakar, juyowa ya yi ya miƙa mata yana kallonta, amsa ta yi itama tana kallonsa ta dinga kallon yar kit ɗin wadda aka yi cealing ɗinta da fari yanki da kuma wasu flowers jajaye, ta dinga kallon kit ɗin dan har ta manta da ita ma, Above 2mins kafin ta ce“sai an jima” jinjina kansa kawai ya yi sai kuma ya ce

“Allah ya haɗa kowa da Alkhairinsa, amma ni nasan ni ne alkharinki Nana” kallonsa ta yi sai kuma ta juya ta yi gaba ba tare da ta bashi amsa ba. Ya tsaya yana kallonta har ta shige ciki sannan ya sauke numfashi shima ya zagaya ya shige motarsa ya bar wajen.
Chapter 34 · 0% Book details