← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 125

Sashe 114

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har sannan bai ce komai ba, Ta leƙo fuskarsa taga idanunsa a rufe. Ta jima tana kallon kyakkyawar fuskarsa kafin ta tashi daga jkinsa, ta share hawayenta sannan sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Sai da yaji ƙarar rufe ƙofa sannan ya buɗe idanun sa, Ya tashi zaune yana kallon ƙofar. Can kuma ya koma ya yi kwanciyarsa.

Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da wani sabon kukan, Ita bata san laifin da ta yi masa ba, Gashi a rayuwarta ta tsani a shareta. Shi kuma sararsa kenan duk sanda ta yi masa wani laifi to ba zai kulata ba ranar, Gajiya ta yi da kukan bacci ya ɗauketa a wajen, Around 11pm ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta kwanta akan hannunta sai numfashi take sauketa a jere a jere alamun baccin baya yi mata daɗi. Ƙarasawa kan gadon ya yi ya gyara mata kwanciyar, Ta sauke ajiyar zuciya tana motsa bakinta, Ɗan murmushi ya yi sannan ya shafa dogon gashinta. Ya rufeta da duvet, Ya jima zaune yana kallon ta kafin ya kwanta shima, Ya jawota jikinsa ya rungumeta, Kamar jira take ta sake shigewa jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Ya kashe hasken ɗakin sannan ya lulluɓe su a tare nan da nan bacci ya ɗauke shi. Kiran sallar farko ya tashi ya bar ɗakin, Ya koma nasa ya ɗauro alwala sannan ya wuce masallaci, Koda ya dawo bai shiga daƙinta ba ya shige nasa ya yi kwanciyarsa. Sai ƙarfe 11:00 na safe sannan ta tashi daga bacci, Ta shiga banɗaki ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata atampa glitter ɗinkin A-shape, Ta ɗaura ɗankwalin akanta sannan ta fito parlour. Neman waje ta yi ta zauna duk da yunwar da take ji, Bata fi 5mins da zama ba ya shigo parlourn, Ganin yana shirin wucewa ya sanyata tashi tsaye, Ta ƙarasa ta tare gabansa tana kallon sa a sanyaye ta ce

“Dan Allah uncle...”

Kallon ta ya dinga yi fuska a ɗaure,Kafin ya ce“Matsa min hanya.” Madadin ta yi abin da ya ce sai kawai ya ga ta faɗa jikinsa tana kuka, Shiru ya yi yana saurarenta, Ta dinga rera kukanta kafin daga bisani ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce

“Dan Allah uncle ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake ba kaji.”

Janye jikinsa ya fara ƙoƙarin yi, Ta sake ƙanƙameshi tana sakin wani sabon kukan, Ya ɗauke kansa saboda dariyar da ke neman kwace masa, Sai da ya yi clearing throat ɗinsa sannan ya kalleta fuska ɗaure ya ce

“Me ki ka min?”

Girgiza kanta ta yi cikin kuka ta ce

“Wallahi ban sani ba, Ban san me nayi maka ba”

“Ko?”

Ya tambayeta yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai kawai ta yi. Ya janyeta daga jikinsa ya ce

“Idan ki ka tuna abin da ki ka yi min sai ki zo ki bani haƙuri”

Daga haka ya ratsa ta gefenta ya haye sama abin sa, Tsayawa ta yi a wajen tana nazarin maganar da ya faɗa, To me ta yi masa? Ta buga ƙafafunta a ƙasa kafin ta bi bayansa a hankali. Zaune ta same shi gefen gado yana danna wayarsa, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefensa ta ce

“To ai ban san me nayi ba Uncle.”

Kallon ta ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To tun da baki sani ba tashi ki ban waje”

Langwaɓar da kanta ta yi, Ta kwanta akan cinyarsa sannan ta ce“To ai na ce ka yi haƙuri kuma”

“Ba zan haƙura ba!”

Ya yi maganar yana ajiye wayar hannunsa, Shiru Nana ta yi tana kallon sa. Can kuma ta ce“To idan baka haƙura ba ya zan yi?”

Yanda ta yi maganar kamar zata fashe da kuka ya kusa bashi dariya, Ya tsuke fuska ya ce“Ina ruwana da yanda zaki yi?”

Tura baki ta yi, Ta sauka daga jikinsa ta kwanta a kan gadon ta rufe idanunta. Bai ce komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da wata leda, Ya ajiye a ƙasan gadon yana kallon ta ya ce

“Tashi ki dafa min abinci”

Jiki a sanyaye ta tashi ta fice daga ɗakin, Ya girgiza kansa sannan ya nemi waje ya zauna. Sai da ta ɗan yi jim a wajen tana ƙarewa kitchen ɗin kallo kafin ta ɗauko wuƙa. Doya ta ɗauka ta feraye sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora akan wuta, Ta nemi kujera ta zauna tana jiranta, Bayan ta dahu ta kwashe sannan ta fasa kwai ta saka albasa da kayan ƙamshi, Ta saka maggi sannan ta ɗora mai akan kasko ta fara soyawa. Bayan ta gama ta dauko wani flask mai kyau ta zuba a ciki, Sannan ta ɗora farfesun kayan ciki a wata tukunyar, Ta gama shima ta zuba a flask sannan ta ɗiba ta ɗora akan tray ta nufi saman, A parlour ta ajiye ta koma ta dauko tea flask da cups ta dawo ta ajiye. Sannan ta shiga ɗakin, Zaune ta same shi ya sauya kaya zuwa wasu English wears riga armless da cargon 3-quater gashin kansa ya zubo gefen kafaɗarsa gwanin ban sha'awa.

“Uncle na gama”

Ta ce tana kallon sa, Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ajiye wayar hannunsa ya ce

“Okay I'm coming"

To kawai ta ce sannan ta juya ta fice daga ɗakin, Zama ta yi kan kujera ta kunna tv ta fara kallon wata drama da ake haskawa a Netflix, After some minutes ya fito hannunsa riƙe da ledar ɗazu, Ya nemi waje a ƙasa ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa. Kafin ya yi magana ta taso ta tsuguna a gabansa, Plate ta ɗauka ta zuba masa abincin sannan ta haɗa masa tea ɗin ta miƙa masa. Ta koma ta zauna tana ci gaba da kallon ta,

“Kefa?”

Taji ya tambaya, Kallon sa ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“Na ƙoshi”

Wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya ce

“Kin taso anan ko sai na ɓata miki rai?”

Tura baki ta yi sannan ta tashi, Ta koma ƙasa kusa dashi ta zauna. Wani empty cup ɗin ya dauka ya zuba mata tea ɗin, Ya miƙa mata sannan ya saka plate ɗin a tsakiyar su ya ce

“Ohya eat!”

Kamar zata yi kuka haka ta ɗauki shayin ta kai baki, Ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye, Haɗe rai taga ya sake yi ya ce

“Ba zaki ci ba?”

Girgiza kanta ta yi sannan ta saka hannu ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki, Dakyar ta tauna tana yamutse fuska. Ya gyara zamansa yana kallon ta har sannan, Ganin ta jingina da jikin kujerar ya sanya ya ce

“Nana yaushe na fara wasa dake?”

Kamar zata yi kuka ta ce“wallahi uncle na ƙoshi”

“Idan na sake miki magana sai kin gwammace baki sanni ba Nana!”

Ganin how serious he's ya sanya ta sake ɗaukan ɗaya ta kai baki,Dakyar ta dinga taunawa, Tana dira cikinta ta tashi da gudu ta bar wajen, Da idanu ya bita sai kuma ya miƙe bayan ya ajiye cup ɗin hannunsa, Bayanta ya bi, Ya sameta durƙushe cikin banɗaki sai kwarara amai take. Da mamaki ya ce

“Subhanallahi”

Ya ɗagota yana kallonta ya ce

“Mene ne?”

Bata iya cewa komai ba sai numfashi take saukewa, Ya girgiza kansa sannan ya janyeta daga wajen. Sai da ta wanke bakinta sannan ya sanya ta fito, Ya gyara wajen ya biyo bayanta. Zaune ya sameta kan sofa sai numfarfashi take, Ya ƙarasa ya zauna gefenta sannan ya jawota jikinsa, Sosai yaji zafi a jikinta, Ya ɗago kanta ya ce

“Baki da lafiya ne?”

Girgiza kanta ta yi kawai, Ya rungumeta ya ce

“Sannu to”

Kwace jikinta ta yi ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, wani aman ta sake yi, Ya dinga kallon ta ganin yanda take aman kamar zata amayar da kayan cikinta, Sai da ta gama ta wanke bakinta sannan ya kalleta ya ce

“Zo nan”

Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya ɗauketa kamar ƴar baby suka fita daga toilet ɗin, Ɗakinsa ya kai ta ya kwantar da ita sannan ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa goshinta ya ce

“Sannu, Bari na shirya mu je asibiti”

Ita dai bata ce komai ba sai lumshe idanunta da ta yi, Ya tashi ya fice daga ɗakin. Koda ya dawo samu ya yi ta yi bacci, Dan haka ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa, Shi kaɗai ya dinga murmushi yana shafa kanta, Can kuma ya tashi ya ɗauki car key ɗinsa ya fice daga gidan.

Yinin ranar a kwance ta yi sa, Sai wajen ƙarfe 6:30 na yamma sannan ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin wata doguwar riga brown colour, Ta saka ɗan ƙaramin hijabi sannan ta sakko ƙasa, Yunwa sosai take ji, kuma bata jin zata iya cin abin da ta dafa, dan haka kawai ta tafi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ta shiga zaune ta samu Atta da Mama suna magana, Sai Hajiya Babba da ke zaune tana karanta azkar, Sallama Nana ta yi sannan ta gaishe su, Suka amsa a tare, Kallon ta Hajiya Babba ta yi ganin ta tsaya ta ce

“Nana lafiya dai?”

Gyaɗa kanta ta yi a hankali ta ce“Ba komai Hajiya.”

“Nana zo nan”

Mama ta yi maganar idanunta na kanta, Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, Mama ta taɓa wuyanta sannan ta ce

“Baki da lafiya ne? Me ke damun ki?”

Ta jera mata tambayoyin, Sunkuyar da kai Nana ta yi ta ce“Zazzabi nake Mama”

“Shi Abdusammad ɗin bai kai ki asibiti ba?”

Cewar Hajiya Babba tana kallon su, Gyaɗa mata kai Nana ta yi tana hawaye. Hajiya Babba ta ɗauki wayarta da ke gefenta ta yi dialing numbern sa, Ringing ɗaya ya ɗauka murya babu walwala ta ce

“Abdusammad kana ina?”

Daga can ɓangaren Abdusammad da ke zaune parlon Aliyu ya ce

“Ina gidan Aliyu Mama”

“Ka zo ina neman ka yanzu”

Toh kawai ya ce sannan ta kashe wayar, Ta mayar da idanun ta kan Nana wadda ta sunkuyar da kanta tana hawaye ta ce

“Kin ci abinci?”

Girgiza kanta ta yi, Hajiya Babba ta ce

“To me zaki ci?”

“Ni bana cin komai”
Chapter 114 · 0% Book details