← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 125

Sashe 118

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gaskiya Nana kina bani mamaki, Ke a haka zaki ci gaba da zama?”

Kallon ta kawai Nana ta yi da rashin fahimta, Ta gyara zamanta sannan ta ce

“To ya zan yi Amani? Kullum ma a haka nake, Ni na gaji ma wallahi, Ji nake kamar na mutu.”

Wani kallo Amani ta yi mata sai kuma ta ce

“Au to zauna, Ƴar ƙaramar ki dake ki wani fara haihuwa, Da kin haifi ɗa ko ɗaya ne shikenan zaki ga kin fara canzawa, Komai ya nemi ya ƙare miki. Ya ma za'a yi na bari na haihu? Ai ko Deen ya sani wlh ba zan haihu ba har sai na gama karatu, Na koma na zauna sannan na haifi ko ɗaya ne”

Mu'ash da ke danna wayarta ta ce

“Bare kuma ni! Kin ga yanzu dai shekarar mu biyu da aure ko? To sau biyu ina ɓari, Dana samu ciki nake zubarwa, Akan me? Tab!”.

Ita dai Nana kallon su kawai take can kuma ta ce

“To ni ai ban san yanda zan yi ba. Sai dai na bari idan na haihu nayi planning”

“Shi kuma wannan cikin fa?”

Amani ta tambayeta, Ɗan haɗe rai Nana ta yi ta ce

“Sai na haihu ai”

Jinjina kai Mu'ash ta yi ta ce

“Oh har sai kin jira kin haifi wannan cikin dai bai rufe wata biyu ba?”

Kamar zata yi kuka ta ce“To Mu'ash ya zan yi wai?”

“Ki zubar!”

08106608363
Nanameera.*Page 69.*

Girgiza kai Nana ta yi muryata a sanyaye ta ce“Ni dai gaskiya ba zan iya ba. Uncle faɗa zai yi min..”

Wani dogon tsaki Amani taja kafin ta ce“amma ke dai baki da tunani wallahi! Ki ji min hauka, to bari zaki yi ya gane?” Kallon ta Nana ta dinga yi da rashin fahimta. Mu'ash ta ce“Nima abin da na gani kenan, Ya za'a yi ma ki bari ya gane. Ai kawai yi zaki yi a zuwan ɓarewa ya yi da kansa” Marairaice fuska Nana ta yi ta ce“Ni gaskiya tsoro nake ji, Idan kuma ya gane fa?” Takaici ne ya ishi Amani, A ɗan fusace ta ce“Ai sai ki bari ya gane ɗin!” Tura baki Nana ta yi bata ce komai ba. Mu'ash ta gyara zamanta ta ce“Kina ji Nana, Kawai za'a baki tablet ne ki sha, Da zarar kin sha 15mins sun yi yawa cikin zai ɓare.” Ita dai Nana bata ce komai ba sai kallon ta take, Mu'ash ta ci gaba da cewa

“Kin ga idan ya zube sai ki ce kema baki san garin ya ya ba, Sannan kada ki yarda ki sha yana gidan, Ki bari sai ya fita. Yanda zaki iya cewa faɗuwa ki ka yi, Kin ga shikenan kin huta, Bayan kwana biyu sai ki yi planning har ki gama karatun ki”

Kasa cewa komai Nana ta yi tana kallon su, Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, Taji tana son zubar da cikin, amma tana tsoron abin da zai iya biyo baya. Can dai ta ce

“To zan fara shawara da uncle”

Baki buɗe suka dinga kallonta, Amani ta miƙe cike da takaici ta ce“Idan ban bar wajen nan ba sai baƙin ciki ya kasheni, Sai ki je ki yi shawarar dashi!”

Tana gama faɗin haka ta yi gaba fuuu kamar zata tashi sama. Da idanu suka bita, Sai kuma Mu'ash ta kalle ta ta ce

“Kina ji Nana, babu maganar shawara dashi, ai ba zai bar ki ba. Musamman da ki ka ce ƴar sa ta mutu, ba zai taɓa yarda ki zubar da cikin ba. Kawai ki zubar”

“To idan ya kamani fa?”

Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Girgiza kai Mu'ash ta yi ta ce“Ba zai kama ki ba. Babu abin da zai faru”

Shiru Nana ta yi tana tunanin hukunci da zata yanke, Can dai ta numfasa ta ce“Ni dai wallahi bana so!”

Daga haka ta tashi ta bar wajen da sauri, Da idanu Mu'ash ta bi ta sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce

“Allah wadaran naka ya lalace, Nana! Nana!”

****
Bayan sallar isha'i tana kwance akan cinyarsa yana operating system ɗin gabansa, Kamar wadda aka tsikara haka ta mike zaune tana kallon sa ta ce

“Uncle”

“Uhm..”

Ya ce ba tare da ya ɗago kansa ba, Ɗan sosa kanta ta yi kafin ta kwaɓe fuska ta ce

“Dama tambayar ka zan yi”

Ɗago manyan idanunsa ya yi ya zuba mata, Ta yi saurin ɗauke nata. Babu yabo babu fallasa ya ce

“Nana ki bar ni na gama abin da nake dan Allah.”

“To magana zan yi fa”

Ta bashi amsa kamar me shirin fashewa da kuka, Rufe system ɗin ya yi dan ya san tun da ta fara haka ba zata bar shi ya ƙarasa ɗin ba. Ya jawota jikinsa ya ce

“Ina ji mene ne?”

Hannunsa ta saka ta fara murɗa lallausan gemunsa kafin ta ce

“Uncle wai ba zan iya karatu ba idan ina da ciki?”

Da sauri ya kalleta ya ce

“wane ya faɗa miki?”

Tura baki ta yi ta ce“Ni kawai ka faɗa min!”

Ɗauke kansa ya yi yana kallon saitin window, ya ce

“Me zai hana ki karatun ki Nana? Muddin kina da lafiya ai zaki iya zuwa makaranta, Sai dai idan kin kuka haihuwa ki ɗauki hutu”

Shiru ta yi tana nazari, Ya mai da idanunsa kanta ya ja kumatunta ya ce

“Wane ya ce miki ba'a karatu da ciki?”

Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce

“Babu kowa”

“Ƙarya zaki min?"

Ya ce yana tsuke fuska. Sunkuyar da kanta ta yi, Ya girgiza kansa ya ɗago fuskarta ya ce

“Kwana biyu uncle ya yi missing Nanar sa”

Sarai ta gane abin da yake nufi, Dan haka ta fara ƙoƙarin sauka daga jikinsa amma ya riƙeta gam.

“Mene ne?”

Ya ce yana ƙoƙarin zare ribbon ɗin data tufke kanta dashi, Kamar zata yi kuka ta ce

“Uncle bacci zan yi”

“To kwanta”

Ya faɗa yana tura hannunsa cikin sumar kanta, Lumshe idanun ta ta yi, Saboda dadin susar da taji. Ya ɗauke system ɗin daga kan gadon sannan ya gyara mata kwanciyarta, Ya sanya hannunsa ya kashe hasken ɗakin nan da nan duhu ya mamaye ko ina.

****
Yola, Nigeria.

Yau wata ɗaya kenan da tariyar Anty Khadijah, Tana zaune gefen gadonta ta zuba uban tagumi aka yi sallama aka shigo, Ɗaga kanta ta yi tana kallon yaron da ke tsaye a kanta. Yana ɓare gyaɗar dake hannunsa ya ce

“Wai in ji Baba ya ce baki gama abincin ba yunwa yake ji?”

Tsabar baƙin ciki rasa abin ce masa tayi, Ta miƙe ta bar wajen tana kwafa. Tsayawa yaron ya yi yana kallon ta ganin ta koma kan kujera ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin, After some minutes aka buɗe dakin aka shigo cikin ɗaga murya yana cewa

“Khadijah! Khadijah! Khadijah!”

Kallon sa kawai Anty Khadijah ta yi sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, Rai ɓace Malam Garba ya ce

“Ke tsabar rashin mutunci kina ji ina miki magana kin yi min banza! Bayan na aiko yaro baki bashi amsa ba? Me ki ke taƙama dashi ne?”

Miƙewa tsaye ta yi a fusace ta ce

“Ban sani ba ɗin! Ba kuma zan yi bane, Wallahi ba zan ci gaba da dafa uban abinci ba a cikin gidan nan, Ban haifa ba babu wanda zan yi wa girki! Dan haka idan ma zaka nemi mai girka maka abinci ka nema ni ba yar iska ba ce...”

Saukar marukan da taji shi ne abin da ya sanya ta yi shiru da maganar tata, Ta sanya hannayenta duk biyun ta rike kuncinta tana kallon sa. Can kuma ta ce

“Na rantse da Allah baka isa ba! Wallahi ba zan yarda ba! Kai ka isa ka dinga dukana”

Ko rufe baki bata yi ba ya hau ta da duka ta ko ina, Tun tana ƙoƙarin kwacewa har sai da ta ƙasa koda motsi a ƙasan ya sanya ƙafarsa ya take hannunta cikin masifa da kumfar baki ya ce

“Ke har kin isa a gidana? Ban auri wadda zata ɗaga min murya ba! Duk ranar da ki ka kara yi min irin haka wallahi sai na karya ki”

Ya yi ball da ita kamar ya samu ƙwallo, Ta bugu da jikin gado, Ya juya har ya kai ƙofa sai kuma ya dawo yana kallon ta ya ce

“Kuma idan baki tashi kin fito ba wallahi na dawo sai kin raina kan ki!”

Ya zabga mata harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Tsananin azaba ta sanya Anty Khadijah kasa motsi a wajen, Ga ciwon da jikinta ke mata, Ga kuma na duka. Yau kusan kwana uku kenan kullum sai ya yi mata mugun duka da zarar ɗan abu ya haɗa su, Ta dinga kuka a wajen tana numfarfashi, Tafi awa ɗaya kwance kafin ta iya tashi zaune. Gefen bakinta sai jini yake sakamakon marukan da ya yi mata, Dakyar ta lallaɓa jikinta ta tashi ta shige banɗaki, Wanke fuskarta ta yi dan babu wadataccen ruwan da zai ishe ta ta yi wanka. Ta dawo ta kwanta akan kujera tana gursheƙen kuka. Bayan mintuna goma ta tashi tunawa da abin da ya ce, Dan ta san idan ya dawo wani sabon dukan zai mata. Ta dinga takawa dakyar ta fito daga ɗakin, Kasancewar yammacine ya sanya soron ya ɗan yi duhu, Ta nufi soron da yake zaune dan ta tambaye shi abin da za'a girka ɗin. Maganar data jiyo ya sanyata tsayawa cak a bakin ƙofar, Muryar Kaddu taji tana bala'i tana masa magana, Malam Garba ya yi murmushi ya ce

“Ke ki rufe min baki idan har ba so ki ke na ɓatar da ke ba!”

Kaddu da ke tsaye tana jijjiga ƙugu ta kalle shi ta ce

“Idan ka fasa! Dan girman Allah kada ka fasa ɓatar dani, Ka manta duk abin da nayi maka. Haka muka yi da kai? Wallahi baka isa ba, Yanda ka ce zan auri mutumin nan idan na bawa Khadijah wannan maganin ka aureta to wallahi sai ka saka na aure shi! Dole ne wannan, Mahaukaciya ma zaka mayar dani kenan!”
Chapter 118 · 0% Book details