Sashe 49
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“shikenan Nana. Allah ya baku zaman lafiya, zuwa an jima kuma saƙona zai iso ga mahaifinki.”
Daga haka ya katse kiran, girgiza kai Nana ta yi sai kuma ta sake dialing number amma sai aka ce mata a kashe. Ta koma gefen gado ta zauna lokaci ɗaya ta fashe da kuka, kifa kanta ta yi akan cinyarta ta fara rera kukanta, ta dinga jin zuciyarta na mata wani irin zafi da suka, tana nan zaune har bayan mintuna biyar wayarta ta fara ruri dan haka ta ɗago kanta da sauri ta ɗauki wayar da tunanin Junaid ne. Sai dai ganin lambar babu suna yasa ta kawar da wannan tunanin, ta yi kamar ba zata daga kiran ba sai kuma wata zuciyar ta ce mata
“Idan kuma shi ya sauya lamba ya kira ki fa?”
Ta sauke numfashi sai kuma ta ɗaga kiran bakinta na rawa ta ce
“Salamu alaikum”
Daga ɗaya ɓangaren aka ce
“Ina magana da Nana ne?”
Nana ta yi shiru tana tunanin inda ta san muryar, ganin ta kasa tunawa yasa ta ce
“Eh ni ce.”
Siyama ta gyara zamanta kan sofa sannan ta ce
“kece wadda ki ke shirin auren Safwan ko? To ki sani tun wuri gara ki rabu dashi. Domin Safwan ba mijinki bane, ni zai aura. Ki fita a sabgarsa tun kafin ran ki ya ɓaci wallahi, dan zan iya komai akan sa, ke zan iya kasheki akansa”
Nana ta yi shiru sai kuma ta ce
“tam na gode.”
Daga haka ta kashe wayarta ta yi jifa da ita, sai kawai ta sake fashewa da wani irin kuka. Nan da nan tari ya fara turnuƙeta, sai kuma ta fara aman jini har da guda-guda dai dai nan Amma ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug. Sai dai halin da taga Nana ya sanya ta saki mug ɗin a ƙasa ta ƙarasa gabanta cikin tashin hankali ta ɗagota tana faɗin
“Nana! Nana! Ke Nana”
Ko kaɗan Nana bata jin abin da take faɗa, dan babu alamar tana tare da ita. Dan haka ta tashi da gudu ta fice daga ɗakin, Abba na tsaye a balcony shi da Sultan ta ƙarasa cikin tashin hankali take faɗin
“Yallabai Nana! Nana”
Abba ya kalleta ganin yanda take kuka yasa ya ce“lafiya me ya samu Nanan?”
Bata iya bashi amsa ba sai girgiza kanta kawai take, Sultan kuwa bai jira sun gama maganar ba ya nufi cikin gidan da sauri. Ganin haka yasa Amma da Abban suka bi bayansa.
Sultan ya dinga kallonta ganin halin da take ciki yasa ya sunkuya ya ɗauketa kamar ƙaramar yarinyar suka fito daga ɗakin, Abba ya biyo bayansa. Aunty Ramlah kuma ta rike Amma ganin babu ko mayafi a jikinta, cikin kuka take ƙoƙarin janye hannunta tana faɗin
“Ramlah ki cikani dan Allah, ki bar ni na bisu”
“To Yaya amma ki fara saka mayafi”
Aunty Ramlah ta ƙare maganar cike da damuwa.
****
Around 3pm Sultan ya fito daga ward ɗin hannunsa riƙe da wata takarda, Abba da Amma da ke zaune suka mike a tare suna kallonsa. Ganin bai ce komai ba yasa Abba ya ce
“Ya jikin nata?”
Miƙewa Abba takardar hannunsa ya yi cike da damuwa ya ce
“Ban san mene ya dameta haka ba da har ya haifar mata da wannan ciwon, but koma mene ne ya kamata a ɗau mataki akansa”
Abba ya warware takardar ya shiga karantawa. Bayan ya gama ya ɗago kansa yana kallon Sultan cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce
“Nana ce ke fama da ciwon zuciya?”
Sultan ya gyaɗa masa kai jiki a sanyaye. Amma ta riƙe Abba cikin tashin hankali ta ce“ciwon zuciya kuma? Nanan tawa?” Abba ya riƙe hannunta ba tare da ya ce komai ba. Fashewa ta yi da kuka tana kallon Sultan ta ce“ina take? Ina son na ganta” da hannu ya nuna mata ɗakin da aka kwantar da Nanan. Ta yi gaba da sauri ba tare da ta sake cewa komai ba, Abba ya numfasa sai kuma ya naɗe takardar yana kallon Sultan ya ce“ya jikin nata?”
“Da sauƙi sosai ta farfaɗo ma. Muje ka ganta”
Okay kawai Abba ya ce sannan yabi bayan Sultan jiki a sanyaye.
Zaune suka tarar da Amma gefen gadon ta riƙe hannun Nana sai kuka take, Abba ya tsaya jikin ƙarfen gadon yana kallon Nana wadda idanunta ke rufe tana sauke numfashi a hankali. Sultan ne ya yi ƙarfin halin cewa
“Dan Allah Amma ki yi haƙuri”
Tashi ta yi daga wajen ta juyo tana kallon Abba ta ce“Idan har kana son Nana. Idan har baka shirya rasata ba dan Allah dan Annabi ka bar maganar auren nan. Wallahi shi ne abin da ya haifar mata da wannan mugun ciwon, ka taimaka ka bar maganar auren nan. Kada ka yi abin da zamu rasa yar mu da kanmu”
Abba bai ce komai ba, sai numfasawa da ya yi. Sultan ya kalli Amma da mamaki ya ce”Nana bata son auren nan?”
Cikin kuka Amma ta ce“Bata so Sultan, tun ranar da aka fara maganar ta ce bata so. Amma na hanata faɗa, na gargaɗeta akan ta yi shiru. Ban yi tunanin abun zai kai haka ba, ban yi tunanin Nana zata damu kanta irin haka ba, tun daga sanda aka fara maganar auren nan ban sake ganin walwalarta ba. Yarinya ce ƙarama, aure ba dole bane akanta, dan Allah ka fahimtar dashi”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka.
Shiru Sultan ya yi, lokaci ɗaya ya ji jikinsa ya yi wani irin sanyi. Ya kalli Amma wadda ke faman kuka sai kuma ya mai da idanunsa kan Abba wanda tun ɗazu bai ce komai ba, Ya taka har gabansa cikin sanyin murya ya ce
“Abba dan Allah...”
Ɗaga masa hannu Abba ya yi, Sultan ya yi shiru yana kallonsa. Amma ta juyo tana kallon Abba da mamaki jin bai ce komai ba. Ya numfasa sannan ya taka har gaban gadon ya dafa goshin Nana jin babu zafi yasa ya sauke numfashi. Amma ta dawo gurin tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba.
Abba ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsu duka ya ce“Babu yanda za'a yi na janye maganar auren nan, dole sai Nana ta auri Safwan. Wannan shi ne matsayata!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Happy independence day.
Page 31.
Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Sultan ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma gaba ɗaya ransa babu daɗi, bai so a ce haka Abba ya ce ba. Amma dake tsaye gefen Nana ta ƙaraso gabansa dan sam ta kasa jurewa cikin tsananin ɓacin rai ta ce
“Me ka ce Yallaɓai? Ba za'a fasa auren nan ba? Kenan ka shirya ta mutu ta bar duniya?”
Abba ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da idanunsa kan Nana da ke sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya ya ce“Eh. Ba za'a fasa auren nan ba, sai Nana ta auri Safwan, idan ki ka ga an fasa auren nan sai dai idan Safwan ne da kansa ya zo ya ce min baya son Nana, ke to ko haka ne bai isa ba, dole sai ya aureta. Babu yanda za'a yi yara su zo daga baya sannan su nemi ruguza mana dangi, ba zai taɓa yiwuwa ba”
“Kenan gara ka aurar da ita ta mutu ko? Haba dan Allah Nana ce fa, ur one and only daughter, bayan ita fa baka da wata. Ita kaɗai ce amma har ka yi tunanin gara ta mutu akan ƙima?”
Amma ta ƙare maganar a mugun fusace. Abba ya gyaɗa kansa jin tana neman ɓata masa rai ya ce“haka na faɗa Rabi'ah, kuma babu wanda ya isa ya sauya wannan hukuncin dana yanke! Idan har ni Ahmad ni ne na yi cikin Nana kuma ki ke haifeta to wallahi ba zan janye maganar auren nan ba, idan ta so ta mutu.”
Abba ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan tilon ƴar tata da ke kwance tana bacci, ta durƙushe a wajen tana fashewa da kuka. Sultan ya dinga kallonta cike da tausayinta, lokaci ɗaya kuma ya juya ya fice daga ɗakin.
Tsaye ya samu Abba a kofar dakin ya harɗe hannayensa a ƙirji, gumi sai tsatsafo masa yake, ko ba'a faɗa ba kasan ransa a ɓace yake, haka kuma hankalinsa a tashe yake. Sultan yaja ya tsaya yana kallonsa cike da damuwa. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya gyara tsaiwarsa cikin tattausan harshe ya ce
“Abba dan Allah ka yi haƙuri”
Ɗan murmushin yaƙe Abba ya yi yana girgiza kansa ya ce“Babu komai Sultan. Zuwa yaushe za'a iya discharging nata?” Sultan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce“ai jikin nata da sauki ma, ko zuwa magrib za'a iya sallamarta. Kawai dai abin dubawar shi ne halin da take ciki”
Toh kawai Abba ya ce sai kuma ya juya ya koma ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba, Sultan ya sauke numfashi yana cin ransa babu daɗi. Dan ya san halin Abba, muddin ya kafe akan magana to babu wanda yake sauya shi.
Ko da ya koma zaune ya samu Amma gefen gadon sai kuka take a hankali. Hannunta ɗaya akan goshin Nana tana shafawa, ɗayan kuma riƙe da nata hannun. Kallonsu kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba. Shi kansa baya jin daɗin halin da Nanar ke ciki, amma hakan ba zai taɓa sakawa ya bari a zubar da mutuncin gidansu ba, dama ace wata ce ba ƴarsa ba, da zai iya yin shiru idan har iyayenta sun aminta. amma hakan ba zai taɓa faruwa da yar sa ba
“Never!”
Maganar ta suɓuce masa ba tare da ya yi aune ba. Amma ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ɗauke kanta ba tare da ta ce masa komai ba, shima bai damu da shirun nata ba dan daman bai saka ran zata masa magana ba.
****
Siyama ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta kalli Kaddu, lokaci ɗaya ta zumɓura baki tana hararar malamin ta ce
“wallahi ba zai yiwu ba, tabɗijan, ni ba zan iya ba!”