← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 125

Sashe 10

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

****Around 5:20 na yamma wayarta ya fara ƙara, tana zaune gefen closet ɗin Inteesar tana gyara mata kaya, ta daga idanunta tana kallon wayar da ke kan drawer, rigar da ke hannunta ta ajiye sannan ta tashi ta ɗauki wayar, ɗagawa ta yi kafin ta yi magana taji ya ce

"I'm outside"

Okay ta ce sannan ya kashe kiran, ta ɗan yi jim sai kuma ta sauke nunfashi ta koma ta ƙarasa kwashe kayan. Mayafinta ta ɗauka ta yafa bayan ta ɗan gyara fuskarta ta fito parlon, Inteesar ce kawai zaune tana game a tap ɗinta, Nana ta kalleta ta ce"Intee ina Mom?" Inteesar da idanunta ke kan tv ta ce"tana ɗaki bacci take" Ajiyar zuciya Nana ta sauke tana godiya ga Allah a ranta, a fili kuma ta ce"to bari naje na siyo recharge card kin ji" gyaɗa mata kai kawai tayi dan gaba ɗaya hankalinta na kan kallon da take, Nana ta fice daga parlon da sauri. Babu kowa a compound ɗin dan haka ta ƙarasa har wajen gate, ganin da gaske babu wanda ya shigo ya sanya ta fita daga waje ta tsaya, wayarta ta ɗago ta yi dialing numbernsa bugu ɗaya ya ɗauka murya a sanyaye ta ce"na zo ban ganka ba" sir Junaid da ke bayanta ya ce"gani a bayanki" da sauri ta juya tana kallon bayan nata. Tsaye yake jikin motarsa Camry yana sanye da wata shadda fara tas ɗinkin jamfa, ya ɗora hular zanna bukar akansa, sai kallonta yake hannayensa naɗe a ƙirji. Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu ya yi mata kyau matuƙa, ta ƙarasa wajen har sannan bata dauke idanunta daga kansa ba, shima kuma kallonta yake dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce"ina yini?" bai amsa ba sai gyara tsaiwarsa da ya yi yana kallonta ya ce"sorry na taso ki Nana" ɗan murmushi ta yi ta ce"babu komai sir" haɗe fuska ya yi ya ce"bana son wannan sunan" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sake mai da kanta ƙasa ba tare da ta ce komai ba. Sun daɗe a haka kafin ya numfasa ya ce"kin san me yasa nace mu haɗu?" Girgiza masa kai ta yi ya gyaɗa kansa kana ya ce"good, ina son mu san abin yi ne Nana, ina son na san ta hanyar da zan iya mallakar ki, wallahi tallahi ina sonki Nana! Ina ƙaunar ki! Amma naga kamar ke baki gane hakan ba, yarinta ta hana ki fahimta"

Runtse idanunta ta yi saboda jin furucinsa, tayaya ma zai ce bata fahimta ba? Ya san yanda ita ma take ji a cikin ranta ne? Ya san irin son da take masa? Me yasa yake nanata ita yarinta ta mata yawa? Why?.

"Nana baki ji na?"

Maganar Junaid ta dawo da ita daga tunanin da take, numfasawa ta yi sai kuma a hankali ta ce"na fahimta mana, nima ina sonka, kuma ka san da haka, da ba don son da nake maka ba babu yanda za'a yi nayi abin da na san iyayena ba zasu ji daɗi ba idan suka ji, da ba zan fito nazo dan na haɗu da kai ba. Dana haƙura da koda kiran ka ne, amma ka san me? Bana iyawa, idan nayi tunanin na rabu da kai nabi zaɓin dangina sai zuciya ta dinga faɗa min ba dai dai bane hakan, sai ta dinga kwaɗaita min irin alkkharanka, sai ta dinga tuna min baya. Wallahi sir ina sonka, tun ban san mene ne son ba, tun ban fahimci abin da yake nufi ba, amma ya zan yi? So ka ke na bijirewa gidanmu? ko kuwa na kai ka nace su aura min kai?"

Junaid ya dinga kallonta yana nazarin kalamanta, yanda take magana wani lokacin har tsoro yake bashi, maganganunta suna shige shekarunta, ta iya tsara zance. Agogon dake maƙale a hannunta ta kalla sai kuma ta ce"ba'a san na fito ba a gida" Junaid ya sauke zazzafan numfashi kafin ya saita nutsuwarsa ya ce"ba haka nake nufi ba Nana, what I mean is koda sau ɗaya ne ki gwada faɗawa iyayenki abin da ke cikin ran ki, ki gwada sanar dasu akwai wanda ki ke so, tun da har yanzu ba'a yi maganar wanda zaki aura ba. I
Maybe idan ki ka yi haka ke ki samu a bar ki da wanda ki ke so, daga sanda ki ka tambaya ni kuma zan fara zuwa gidanku, tun ana korata na tabbata wata rana ba za'a koreni ba Nana" ya ɗan yi shiru yana karantar yanayinta, ganin kamar ta fara ɗaukan abin da yake cewa ya sanya ya ci gaba da faɗin" ki samu ki yi maganar da mahaifiyarki cikin nutsuwa da fahimta, na san ba zata ƙi ba, domin da wuya ki ga iyaye mata suna son irin wannan auran haɗin. Ki yi mata magana yanda zata fahimceki ba da sauri ba sannan kuma ta sigar da zata ji daɗi, ba wai da hargagi ba, na tabbata idan har ki ka yi hakan zamu iya cin nasara!"

Sauke numfashi ta yi tana kallonsa dan har cikin ranta taji ta gamsu da abin da ya ce dan haka ta ce"shikenan I'll give it a try in sha Allah, zan yi maganar da Amma idan na koma gida"

Murmushin jin daɗi Junaid ya yi ya ce"yauwa Nana, shiyasa nake sonki" dariya ta yi tana rufe fuskarta, ya girgiza kansa sannan ya koma ya buɗe motarsa. Wata leda ya fito da ita sannan ya dawo ya miƙa mata yana fadin"your favorite" kallon ledar ta dinga ba tare da ta amsa ba, ya sake cewa"karbi mana" girgiza kanta ta yi ta ce"ba'a san na fito wajen ka ba, idan aka ganni da leda dole ne a tambayeni" Junaid ya ce"bafa wani abun ba ne, naman kaza ne na siyo miki" murmushi ta yi ta ce"tom nagode, amma ka bar shi" Babu yanda bai yi da ita ba amma taƙi yarda ta amsa ledar daga ƙarshe ya hakura ya bar ta dan Nana ta fi shi gardama. Sallama suka yi ta koma gida shi kuma ya bar wajen cike da begenta, koda ta shiga parlon zaune ta sami Aunty Ramlah tana danna wayarta, tana ganinta ta ce"daga ina ki ke ne?" a ɗan rabe ta ce"a'a...a'a daman recharge card naje siyowa zan yi waya nawa ya ƙare" Aunty Ramlah ta ɗago ta kalleta sai kuma ta ce"shi ne ba zaki faɗa min na miki transfer ba?" ɗan murmushi ta yi ta ce"ai kina bacci shiyasa" taɓe baki ta yi ta ce"to kin samo katin?" gyaɗa kanta ta yi tana shirin zama suka ji ana knocking. Koda ta buɗe gate man ɗin gidan ne tsaye yana ganinta ya ce"Yauwa hajiya wai Nana ta zo in ji Sultan zasu tafi" okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Aunty Ramlah da bata motsa ba ta ce"mene?" tura baki ta yi ta ce"wai Yaya ne ya zo yana jirana"

"Da wuri zaku tafi kenan?"

Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta nufi cikin ɗaki ta ɗebo sauran abin da ta bari, ko minti goma bata ƙara a gidan ba suka yi sallama ta fito. Zaune ta sameshi cikin mota idanunsa zube kan titi kuma cikin glasses kamar ɗazu. Buɗe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba, shima ɗin bai yi magana ba ya yiwa motar key suka bar unguwar.

Tafiyar mintuna talatin ta kawo su gida. Nana ta sauke ajiyar zuciya jin ya gama parking ta fara ƙoƙarin buɗe motar ta sauka, gam ta jita a rufe dan haka ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka ta ce"Yaya dan Allah ka buɗe min na fita" banza ya yi mata ya ci gaba da danna wayarsa, gajiya ta yi da magiyar ta koma ta zauna tana takure jikinta waje ɗaya kamar daga sama taji ya ce

"Wane ne wanda ya tsaida ke ɗazun?"

Sai taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, nan take miyan cikin bakinta ya ƙafe ta dinga kallonsa amma ta gagara furta koda kalmar 'A' ce, a fusace ya juyo ya daka mata wata irin tsawa mai firgitarwa yana kallonta jijiyoyin kansa dun sun mimmiƙe idanunsa ya yi wani irin jaa, ko ba'a faɗa maka ba kasan ransa ya gama ɓaci. Kasa magana ta yi sai rawa jikinta yake, rabon da a yi mata irin wannan tsawar har ta manta, ganin bata ce komai ba ya sanya ya sake daka mata wata razananniyar tsawar ya ce"Ba da ke nake magana ba!" fashewa ta yi da kuka, bata yi aune ba kawai ta ji ya sauke mata mari akan fuskarta, iyaka rikicewa Nana ta rikice, ta kasa koda kukan saboda tsananin azabar marin sai jan numfashi take, tun da take a rayuwarta babu wanda ya taɓa marinta sai yau, dan haka ta fice hayyacinta. Sultan ya dinga kallonta yana wani irin huci kamar zaki, har wani ruwa ne ya kwanta a cikin idanunsa saboda masifa. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce"Yau sai kin faɗa min wane ɗan iskan ne yake zuwa wajenki, tun da har kin yi girman da zaki dinga haɗuwa da maza. Wallahi tallahi ba zaki bar motar nan ba har sai kin faɗa min alaƙar ki dashi!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 7...
Chapter 10 · 0% Book details