← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 125

Sashe 90

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko saurarenta bai yi ba ya jawota gaba ɗaya, Ya kunce bathrobe ɗin ta yi saurin shigewa jikinsa tana sakin kuka a hankali, Girgiza kansa ya yi sannan ya ɗauko rigar ya zura mata. Bayan ya kammala ya juya ya fice daga ɗakin, After 15mins ya dawo cikin wasu sabbin kayan fuskarsa ta sake fresh da alama wanka ya sake, Ya ƙarasa wajen injection ɗin daya ajiye ya fara haɗawa, Nana ta dinga kallon sa da ɗan mamaki, bayan ya gama haɗawa ya hawo kan gadon hannunsa riƙe da syringe ɗin, Ta yi saurin tashi zaune duk da jikinta babu ƙwari, Ganin tana neman guduwa ya sanya ya riƙota, Ya jawota jikinsa fuskarsa a haɗe babu alamar wasa. Kuka ta saka masa ta fara yarfe hannu, Ya jingina da fuskar gadon yana kallon ta, Cikin kuka ta ce

“Uncle dan Allah kada ka yi min allura ban so, zafi take min.”

Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce

“Baki son allurar?”

Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana hawaye, Ya ɗan taɓe baki sai kuma ya ce“To kina son na baki sweet?” gyaɗa masa kai ta sake yi, gaba ɗaya fuskarta a shagwaɓe take tamkar jaririya sai narke masa take. Ya zaro wata chocolate a aljihun wandonsa yana kallonta. Ta haɗiye yawu tana kallon ledar chocolate ɗin, ɓarewa ya yi ya kutsuro yana kallonta ya ce

“Haa.”

A hankali ta buɗe bakin nata, Ya saka mata chocolate ɗin ta fara taunawa a hankali tana lumshe ido. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke kansa, Ta kwanta akan ƙirjinsa tana ci gaba da tauna chocolate ɗin, sam bata san ya dauƙo allurar ba, Ya ɗan janye rigarta dan daman ta tattare, ya ɗora tsinin allurar a jikinta sannan ya yi bismillah ya yi mata. Wani irin ƙara ta saki tana ɗagowa daga jikinsa, Ya yi saurin saka bakinsa cikin nata yana shafa bayanta, Kuka ta dinga yi tana ƙoƙarin cizonsa a bakin, Shi dai ya yi shiru yana tsotsar lips ɗinta a hankali. Ta ci gaba da kukanta tana dukansa a ƙirji, Ya ɗan yi murmushi yana riƙe hannunta. Cikin yan mintuna kuma jikinta ya fara saki, Ta mai da kanta ƙirjinsa har sannan bai zare bakinsa daga nata ba, Itama ta fara tsotsar nasa lips ɗin a hankali a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da yaga baccin nata ya fara nisa sannan ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita, Ta saki ajiyar zuciya tana turo baki gaba wanda yake ta sheƙi, Murmushi kawai ya saki ya ɗan ja kumatunta a fili ya ce

“Rigimammiya!”

08106608363
Nanameera.
*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 54.

Ya gyara mata duvet ɗin ya rufeta gaba ɗaya sannan ya sauka daga kan gadon, Remote ya ɗauka ya ƙaro gudun ac sannan ya kashe leds ɗin dakin ya juya ya fice. A parlour ya samu Zahra tana bawa Noor abinci, Ya zauna ɗan nesa dasu. Ta sauka daga jikin Zahra hannunta riƙe da ƙaramin plate mai ɗauke da chips ta nufosa, Murmushi ya yi yana ajiye wayar hannunsa ya ce

“Noorie.”

“Abbie ka bani abinci.”

To kawai ya ce sannan ya ɗauketa ya ɗorata kan cinyarsa. Ya fara bata abincin tana masa hira, wani ya amsata wani kuma ya yi shiru. Zahra kuwa ta dinga kallon su ba tare da tace komai ba, daga ƙarshe ta tashi ta bar parlourn. Da idanu ya bita sai kuma ya ci gaba da abin da yake, bayan ya gama bata abincin ya sauketa yana cewa

“Oyah muje ki kwanta. Dare ya fara yi”

“Abbie ka ɗaukeni to!”

Ta yi maganar tana miƙo masa hannu, Murmushi kawai ya yi sannan ya ɗauketa ya fara juyi da ita, ta dinga dariya tana ƙanƙamesa. Kafin daga bisani ya nufi apartment ɗin Zahran da ita.

****
Nigeria.

Safwan ne zaune kan kujera idanun sa zube akan Haule wadda ta sunkuyar da kanta ƙasa, Tun da ya shigo yake kallon ta. Ya kasa gane wane yanayi yake ciki, farin ciki ne ko kuwa baƙin ciki? Ya ɗan numfasa kafin ya ce

“Allah ya sauke ki lafiya, Ya bamu mai albarka.”

A zuciya ta amsa da amin dan bakinta ya yi mata nauyi, Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi yana ajiye ledojin dake hannun sa ya ce

“Sai da safe.”

Sai a sannan ta ɗago kanta ta kalle shi da runannun idanunta, Tayi saurin sauke su ƙasa kafin ta ce

“Allah ya tashe mu lafiya.”

Da amin ya amsa sannan ya juya ya bar parlourn, Haule tabi bayansa da kallo kuka na tawo mata. Yana fita Amma na fitowa daga dakin, Ta ƙaraso wajen jin shessheƙar kukan Haulen, Zama ta yi gefenta ta dafata ta ce

“mene ne abun kuka kuma Haule?”

“Amma shikenan na rabu da Yaya Safwan? Shikenan ba zamu tafi gida tare ba? Ni ban ce sai ya zo inda nake ba. Kawai ya maidani gidansa, zuciyata zafi take min Amma!...”

Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Amma ta yi tana saurarenta cike da tausayawa, Can dai ta ɗan bubbuga bayanta ta ce

“Kaddara ce ta haɗaku, kuma ita ce ta raba ku. Ba zai yiwu ki ci gaba da zama da Safwan ba Haule, Saboda dalilin yana da ƙarfi. Ki sakawa ran ki haƙuri, har Allah ya saukeki lafiya ki samu wani mijin ki yi aurenki.”

Haule ta sake fashewa da wani sabon kukan tana faɗawa jikin Amma, Ta dinga rera kukanta kamar ranta zai fita. Ita kanta bata san sanda ta fara son Safwan ba, bata san kuma dalili ba. amma ji take kamar ta tashi tabi bayansa, kamar taje ta roƙe shi akan ya maidata daƙinta. Sun ɗauki lokaci a haka kafin Amma ta ɗago fuskarta ta fara goge mata hawayen ta ce

“Kuka yanzu ba naki bane Haule, ki kwantar da hankalin ki. Ko dan lafiyar abin da ke cikinki.”

A hankali ta gyaɗa kanta, Amma ta ce“Tashi ki shiga ciki, idan aka yi Isha'i sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba dan ta ce tana nemanki.”

“ko naje yanzu?”

Haule ta yi tambayar a sanyaye,

“Baki gaji ba?”

Amma ta ce tana kallon ta, gyada mata kai ta yi ta ce“Eh Amma zan iya zuwa.” Numfasawa ta yi kafin ta ce“to tashi ki je Allah ya tsare” Haule ta amsa da amin sannan ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta fice daga parlon, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta. Nana ce ta faɗo mata arai, dan haka ta jawo wayarta dake kan table ta fara dialing numbernta, sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba dan haka ta mayar da wayar ta ajiye ta tashi ta koma ciki..

Tsaye ta hangesu bakin apartment ɗin Hajiya Babban, ta ƙarasa a sanyaye tana sunkuyar da kanta. Kasa shigewa ta yi dan haka ta ɗan durƙusa ta ce

“Hamma ina yini?”

Sultan ya kalleta dan bai ma ganeta ba, can kuma ya ce“au Haule lafiya kalau, ke ce a daren nan?” gyaɗa masa kai ta yi kafin ta kalli Amrah ta ce“Sannu ya jikin?”

“Da sauƙi Alhamdulillah.” cewar Amrah tana murmush, Safwan ne ya kalleta kamar ba zai magana sai kuma ya ce

“Ina zaki je da daren nan?”

Sai da taji zuciyarta ta buga, Ta ɗan runtse idonta murya can ƙasa ta ce“Hajiya Babba ke kirani.”

“Okay, amma idan kin daɗe ki kwanta anan kawai. Ki daina yawo” toh kawai ta ce sannan ta bar wajen a sanyaye. Sultan ya girgiza kansa yana kallon Safwan fuska babu annuri ya ce

“amma ka cutar da yarinyar nan wallahi. Ni ban so ma wannan cikin ba, yarinya ƴar ƙarama zata zama bazawara har da ɗa...”

Shi dai Safwan bai ce komai ba, dan shima zuciyarsa ba wani daɗi ta yi masa ba. Can dai ya ce

“Goben zan shigo asibitin.”

Sultan ya ɗan harararesa sannan ya ce“kada ma ka shigo, ka zauna ka kashe kanka. Kusan 1 week ina maka magana amma kana shareni” girgiza kai Safwan ya yi cikin sanyin murya ya ce“ba zaka gane bane. Zan zo dai”

“Allah yasa.” cewar Sultan, Ya ɗan yi murmushi sannan ya kalli Amrah dake ta yatsine fuska ya ce“Sai da safe, Allah ya raba lafiya.” da Amin ta amsa sannan ya sake yiwa Sultan ɗin sai da safe ya bar wajen, Sultan ya ɗan kalleta ganin ta durƙusa ya ce

“mene ne?”

“Yaya nagaji, cikina zafi yake min.”

Riƙo hannunta ya yi ya ce“Sorry muje gida.” ta ɗan gyaɗa kanta sannan suka fara tafiya a hankali.

****
Gibson Jalo.

Anty Khadijah ta ɗan kalli Umma sai kuma ta yi dariya ta ce“Ai Umma na kusa auren da gaske in sha Allah. Nan bada jimawa ba zaki ga an fara zancen auren” Umma ta ɗan taɓe baki ta ce“Yo Khadijah kalar wannan zancen yau na fara jin sa a wajenki?.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“Allah wannan karon da gaske nake Umma”

Umma ta ce“To Allah ya tabbatar da alkhairi.”

“Amin kuma kin ga...” maganar ta tsaya saboda wayarta dake ringing, Ta ɗan kalli screen ɗin wayar ganin sabuwar lamba ya sanyata ɗagawa, Ta ce

“Hello.”

“Assalamu alaiki.”

Tashi Aunty Khadijah ta yi ta haye sama da sauri, Ɗakinta ta shiga ta saka key ta rufe sannan ta ce

“Akan me ka ke kirana? Bana faɗa maka ni ba sa'ar aurenka ba ce?”

Girgiza kansa ya yi yana murmushi can kuma ya ce“Khadijah kenan, daman kiran ki nayi na nemi yafiyarki. Wallahi bada wani abu nayi wannan maganar ba, amma ina son ki yi haƙuri ki yafe min.” Anty Khadijah taja wani dogon tsaki kafin ta ce

“An faɗa maka ni irin waɗanda zaka yiwa wayo ce? To bari kaji wallahi koda wasa ka sake kirana sai nayi maka rashin mutunci, Wani ƙazami da kai!”

Bata jira amsar da zai bata ba ta sauke wayar daga kunne ta katse kiran tana jan wani dogon tsaki. Tsabar takaici ya sanya ta yi wurgi da wayar ta faɗa tsakiyar gado, Ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana tunani. Ta fuskanci idan bata yi maganin mutumin nan ba sai ya sakata a masifa, Ta yi kwafa ta tashi ta fice daga ɗakin gaba ɗaya..
Chapter 90 · 0% Book details