← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 125

Sashe 66

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kamar yanda na faɗa dole sai mun yi haƙuri. Saboda mu iyayene, babu alfanu cikin fushi da yara. Yanzu idan ka yi fushi da ita Alhaji hakan ba zai haifar mata da ɗa mai ido ba, ba zata shiryu ba, sai dai ma ta sake lalacewa. Domin fushin iyaye akan ya'ya masifa ce babba, kome suka aikata dole ne mu yi haƙuri. Kuma ba'a cewa an sallama ɗa, idan ka sallamata ka nunawa Allah ka zaga akan amanar daya baka, ka butulce masa. Na san kuma ba zaka so kayi hakan ba, Laifi ne ta riga da ta aikata shi, wanda idan aka biyo abun tun daga farko ma bata da wani laifi, ƙaddara ce, duk abin da ta yi yarinta ce. Laifin na yaron daya ɗauketa hotunan ne”

Daddy ya yi shiru yana kallon Abba wanda ya yi ƙasa da kansa yana jin zuciyarsa na tafasa. Ganin halin da yake ciki ya sanya Daddy numfasawa kafin ya ci gaba da faɗin

“Dan Allah Alhaji Ahmad kayi haƙuri. Ka yafe mata, ka ɗauki komai a matsayin ƙaddara, kada ka ce zaka riƙeta a ranka. Yarinya ce ƙarama, har yanzu bata kai munzalin hankali ba. Ballantana ace tana sane ta aikata abin da tayi. Maganar aure kuma ka aura mata kowane, tun da daman ita ba ƙi ta yi ba, tana gudun abin da zai je ya dawo ne, kuma har yanzu bata san kun ga hotunan ba. Da nasan ba zata taɓa biyoni ba, bana gari sanda ta zo, da wallahi a ranar zan dawo muku da ita.”

Ya ƙare maganar a tausashe. Girgiza kai Papa ya yi cikin mutuntawa ya ce“haka ne Alhaji, wannan haka yake. Haƙuri shi ne ribar zaman duniya, kuma dole mu yi hakuri da wawtar ya'yanmu. Kamar yanda mu ma iyayenmu suka yi haƙuri da tamu, Babu wnada ya shige ƙaddara ta faɗa masa, komai girmansa komai ƙanƙantarsa. Ni wallahi tausayi ma yarinyar ke bani, Allah ya jarrabeta da ƙananun shekaru, sauran ƴan uwanta duk suna zaune hankali kwance.”

Daddy ya ce“Allah sarki. Daman haka Allah ke ikonsa, wani bawan sai ya yi ta jarrabashi daga wannan sai wannan, wani kuma kamar bai zo duniya dan wahala ba. Amma ubangiji da kansa yake faɗa gwargwadon jarrabawarka, gwargwadon kusancinka gareshi. Kaga ashe jarrabawa na tafiya da imanin mutum ne”

Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Allah mai girma, Allah ya bamu ikon cinye jarrabobinmu” da Amin suka amsa a tare sai kuma parlon ya dauki shiru. Abdusammad hankalinsa na ka Abba wanda har sannan bai ce komai ba, ganin kamar jiransa ake ya sanya ya ce“Abba dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba laifinta bane, idan ma tana da laifi to bai shige na kula yaron data san ba ɗan danginta bane. Kuma nayi magana dashi yaron kansa, ya tabbatar min da cewa shi ne ya sanya aka ɗaukesu hotunan saboda ya dinga mata barazana ta yarda ta aureshi, amma bai ce mata ta gudu ba. Batun guduwarta nada alaƙa da Safwan ne da Zahra. They're behind it”

Ya yi shiru yana jin ɗaci a kasan ransa. Da mamaki suka dinga kallonsa, Har Abba sai da ya kalleshi. Papa ya ce“ka yi mana bayani yanda zamu fahimta Abdusammad” numfasawa ya yi sannan ya basu labarin duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Papa ya dinga girgiza kansa cike da mamaki da al'ajabi, Shi kansa Daddy sai da abun ya taɓa shi. Ya kalli Abba wanda ya yi shiru har sannan ya ce

“Ka gani Alhaji. Gaba ɗaya ma ba laifinta bane, yaudararta aka yi. Dan haka dan Allah ka yafe mata”

Ɗago kansa ya yi ya kalleshi. Sai kuma a hankali ya zare glasses ɗin dake idanunsa, ya sanya hanky ya goge hawayen dake maƙale cikin kurmin idonsa. Ya yi gyara murya kafin ya ce

“Ni daman ban riƙeta ba. Ban kuma taɓa tunanin aibatata ba, kawai tana bani tausayi ne, yanda rabuwarta ta lalace da ƙananun shekaru. Amma tun da an yi haka babu komai, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, ya rabamu da mummunar ƙaddara.”

Da Amin suka amsa masa sannan Abdusammad ya ce“Abba babu abin da ya sameta fa. Ba wai ya lalata bane ko wani abu, kawai dai ya ɗauketa hotunan ne, ka daina damun kan ka dan Allah.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleshi a sanyaye ya ce“da gaske?” gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi. Ya zame jikinsa daga kan sofar ya durƙusa ya yi sudujusshukur ya godewa Allah sannan ya tashi ya koma ya zauna. Daddy ya yi murmushi ya ce“mun gode sosai Alhaji, Allah ya ƙara girma” girgiza kai Abba ya yi ya ce“a'a kai ne ka cancanci mu yiwa godiya. Ka tunasar dani abin da na manta, sannan ka tawo tun daga wani gari dan kazo ka gyara ɓarna. Allah ya biya ka da gidan aljanna” Da Amin suka amsa sannan ya sake cewa“To yanzu ya maganar auren nata? Za'a bari ta huta ne ko kuwa akwai wanda zai aureta yanzu?” murmushi Abba ya yi ya girgiza kansa ya ce“ai an ɗaura mata auren tun ranar” washe baki Daddy ya yi ya ce“masha Allahu. Wane mijin?” da hannu Abba ya nuna masa Abdusammad wanda ya yi shiru ya ce“shi ne ya aureta tun a ranar” murmushin jin daɗi Daddy ya yi yana kallonsa ya ce“naji daɗi sosai wallahi, Allah ya sanya albarka ya bada zaman lafiya.” Suka amsa da Amin sannan ya miƙe yana gyara rigar jikinsa ya ce”to Alhaji ni zan shige a ƙara haƙuri” miƙewa duk suka yi Abba ya ce“da sauri haka? Ba zaka yini ba?” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“da wuri nake so na koma ne. Jiya na dawo ƙasar” Papa ya ce“Allah sarki. To Allah ya bada lada, mun gode sosai” ya amsa da Amin sannan suka fito daga parlon a tare. Ganin bai gansu ba ya sanya ya kira wayar Khadijah, bayan ta ɗaga ya ce ta fito dan haka ta taso tana riƙe da hannu Nana suka dawo wajen. Daddy ya dafa Nana ganin yanda idanunta suka kumbura ya ce“Mamana ya isa haka kukan. Komai ya shige kinji.” da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta kalli Abbanta, ganin ita yake kallo yana murmushi ya sanya ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙanƙameshi. Abba ya rungumeta tsaf a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Ita kuwa sai faman kuka take, Murmushi duka suka yi ban da Abdusammad wanda har sannan fuskarsa babu yabo babu fallasa. Daddy na murmushi ya ce“to ba zaki zo muyi sallama ba?” sakin Abba ta yi ta dawo wajensa kanta a ƙasa. Ya ce“Allah ya yi albarka ya kiyaye gaba kin ji.” a sanyaye ta amsa da Amin. Ya sake musu sallama sannan ya kalli Khadijah ya ce“muje ko” da sauri Nana ta kalleshi sai kuma ta ce“Daddy ba zata zauna anan ba?” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a'a Nana. Idan an kwana biyu sai ta zo” bata ji daɗi ba, kuma ba dan taso ba suka yi sallama da Khadijahn ta rakasu har mota sannan ta dawo gurin Abbanta. Sam taƙi yarda da bar jikinsa, Papa ne ya kalleta yana murmushi ya ce“to ni bari na shige office, kije Apartment ɗin Hajiya Babba kin ji” to kawai ta ce ya juya ya bar wajen sannan suka nufi gida ita da Abba..

Amma na zaune gefen gadonta ta rufe fuskarta da hannunta tana tunani wanda ya zamar mata dabi'a taji an bude ƙofar ɗakin. Da sauri ta ɗago kanta, sai dai wadda ta gani ya sanya ta miƙe tsaye zumbur bakinta na rawa ta shiga nunata da yatsa tana cewa

“Naaana. Nana?! Ke ce?"

Da gudu ta tafi ta rungumeta. A tare suka fashe da kuka, Amma ta dinga taɓa ta kamar zata zare ta ce

“Nana. Nana ke ce? Ina ki ka tafi ki ka bar mu? Me yasa Nana?”

Kasa bata amsa ta yi sai sake ƙanƙameta da take. Abba ya shigo ɗakin yana kallonsu, bai ƙoƙarin hana su ba ya ɗauki abin da ya zo ɗauka sannan ya fice daga ɗakin ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan sanar da ita..

****

Is been a days da dawowar Nana gida, lokacin kowa na estate ɗin ya san ta dawo, Safwan har sannan bai iya zuwa ya sameta ba duk da ya ji sauƙi, Zahra kuwa idan hankalinta ya yi dubu to ya tashi, dan tsoronta ɗaya ranar da za'a ce Nana ta shigo gidan a matsayin matar Abdusammad. Bangaren Nana kuwa babu abin da ke damunta, sai dai koda yaushe tana ɗakinta dan tun bayan sanar da ita da aka yi cewa Safwan ya fitar da hotunanta bata sake samun sakewa ba. Kunyar kowa take ji, Idan har ka ganta a waje to sai dai apartment ɗin Hajiya Babba idan Atta ta kirata dan har sannan taƙi komawa Njomboli. Yau ma kamar kullum tana zaune a daƙinta tana game aka buɗe ƙofar ɗakin, bata ɗago kanta ba amma ta katse game ɗin tana jiran abin da Ammar zata ce. Jin an yi shiru ya sanya ta ɗago kanta a hankali, idanunta ya sauka akan Zahra dake tsaye bakin ƙofar ɗakin. Sauke idanu ta yi ƙasa, Zahra ta numfasa sannan ta shigo ɗakin ta mayar da kofar da rufe. Ƙarasowa ciki ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon Nana. Ita kuwa ɗauke kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta a hankali, Sun ɗauki mintuna a haka kafin Zahra ta yi ƙarfin halin cewa

“Nana”

Kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta tuna da abin da Amma ta ce mata, dan haka ta amsa ciki-ciki, hakan bai damu Zahra ba dan bama ta yi tunanin zata amsa ba ɗin. Ta numfasa sannan ta ce“na san ba lallai bane abin da zan nema amma ya zama dole na faɗa miki koda ba zaki yarda ba. Dan Allah Nana...”

“Babu komai Aunty, Ni ban riƙe ki ba. Allah yaga zuciyata”
Chapter 66 · 0% Book details