← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 125

Sashe 6

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi irin na manya ta yi ta ce"kuna gulmarsa sai na kira shi na faɗa masa" haɗe hannaye Safwan ya yi kamar zai yi kuka ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya Babba mai makkah da Madina, sai na dawo" daga haka ya yi gaba yana faɗin"Yaya sai na dawo" Allah ya tsare Aliyu ya ce yana murmushi. Hajiya Babba ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Aliyu ta ce"yaushe ya ce maka zai dawo?" sai da ya yi sipping ruwan dake hannunsa sannan ya ajiye cup ɗin ya kalleta cike da nutsuwa ya ce"cewa ya yi wai abubuwa sun yi masa yawa yanzun, amma zai duba ya gani" Hajiya ta yi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba, sai dai yanayinta gaba ɗaya ya sauya. Lura da hakan ya sanya Aliyu ya dafa hannunta cikin sanyin murya ya ce"don't worry Hajiya, ni zan saka ya dawo in sha Allah" jinjina masa kai kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa.

****Ƙarfe 2:15 na rana ya turo ƙofar ɗakin, kwance take kan gadon ta rufe idanunta. Ya ƙaraso ya tsaya a gabanta, kallonta ya dinga yi ganin how beauty she's da take baccin, ya ɗan yi murmushi yana jin wani sabon so da ƙaunarta a cikin zuciyarsa, idan har ba'a aura masa Nana ba bai san halin da zai shiga ba. Yanzu idan ba ita aka zaɓa masa ba fa? ya yi tambayar cikin zuciyarsa, kawar da tunanin ya yi yana jin ƙirjinsa na wani irin zafi. Ya sunkuya ya taɓa wuyanta, babu zafi sosai sai ɗan ɗimi da ba'a rasa ba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya zai bar ɗakin

"Yaya Sultan"

Yaji ta kira shi a hankali, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya amsa ba, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta ɗan sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce"ka maidani gida" wani irin kallon rainin hankali ya dinga yi mata kafin ya harɗe hannayensa a ƙirji still looking at her ya ce"idan naƙi fa?" shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya zabga mata wata uwar harara sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ɗago kanta tana murguɗa masa baki a fili ta ce"tun da dai nasan hanya sai nayi tafiyata" daga haka ta sake komawa ta kwanta tana lumshe idanu, tun gurin asuba sai yanzu taji mararta ta yi sauƙi, shiyasa take mugun tsoron ganin ƙarshen wata ya yi dan idan ta tashi menstruation ɗaiɗaikun mutane ne da ba zasu sani ba a cikin estate ɗin su, dan ciwo take kamar me naƙuda. Koda a ce tana Aun to sai an dawo da ita gida ko kuma Abba ya sanya Sultan ɗin yaje ya dubata a can.

Tana nan kwance after 10mins wata nurse ta shigo, kallonta ta yi fuskarta cike da fara'a ta ce"Nana ya jikin?" ɗan murmushi ta yi ta ce"da sauƙi sister Zahra" Nurse ɗin ta gyaɗa kai ta ce"ai gashinan nagani, dan ɗazu da alama bakisan inda kanki yake ba, kedai sannu. Kina cikin irin matan da ake jarraba da ciwon mara yayin al'ada, ciwo kamar na haihuwa" langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce"wallahi sister Zahra ji nake kamar zan mutu, ni dama bana period wallahi! Daman ni juya ce!" Tuntsirewa da dariya Zahra ta yi, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta haɗe rai dan ta tsani a dinga mata dariya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ce"Ban da shirme irin naki Nana wane ya ce miki juya bata period?" tura baki ta yi ta ce"nima haka naji"

"Ki ka ji a bakin wa?"

Zahra ta tambayeta, ɗauke kai ta yi ba tare da ta bata amsa ba. Sanin tun da tayi hakan ba magana zata yi ba ya sanya ta ce"Daman doctor ya ce nazo na tafi dake" bata ce komai ba ta sakko daga kan gadon, mayafin rigar data gani a gefen gadon ta ɗauka ta yafa sannan ta yi waje ba tare da ta sake bi ta kan Zahra ba, murmushi kawai Zahra ta yi sannan tabi bayanta.

Tsaye ta sameshi a reception suna magana da wani likitan, ya dinga kallonta fuskarsa babu alamar walwala ya ce"kin zo kin shige ko sai na makeki anan wajen" tura baki ta yi sannan ta nufi hanyar fita daga asibitin tana tafe tana waiwayensa, ganin bai tawo ba ya sanya tana fita daga ƙofar reception ɗin taja ta tsaya kusa da wata flower. Ta dinga kalle-kallen sauran flowers ɗin da aka ƙawata wajen dasu, cike da sha'awa.

Tun daga nesa yake kallonta da mamaki fal akan fuskarsa, he just can't believe ace ita yake gani, kasa jurewa ya yi ya nufi inda take tsaye da sauri har yana tuntuɓe, daga gefenta ya tsaya ya harɗe hannayensa a ƙirji cikin shaky voice ya ce

“Nana!”

A ɗan firgice ta kalli side ɗin dan bata san da mutum a tsaye ba, sai dai wanda ta gani ya sanya ta ɗan ja baya. Murza idanunta ta yi ko mafarki take amma koda ta sake buɗesa shi ta gani tsaye gabanta cikin kyakkyawar shigarsa sai murmushin da yake ƙara masa kyau yake. Girgiza kanta ta dinga yi nan take hawaye ya cika idanunta, muryarta na rawa ta ce"si...sir...sir Junaid!" sake faɗaɗa fuskarsa ya yi duk da yanda yake jin ransa a cunkushe ya ce"Nana, kin gani ko?mena faɗa miki? Idan har ke rabona ce zan sake ganinki, and gashi na ganki that's means we destined to be together.”

Kuka ta fara yi, kuka na farin ciki bana baƙin ciki ba, kukan da ke nuna irin so da ƙaunar da take masa, cikin shessheƙar kuka ta ce“sir daman zan sake ganinka? kana can kana rayuwarka ko?”

Saita nutsuwarsa ya yi jin kukan na neman kwace masa shima, ya ce“ina can cikin begenki da kuma tunaninki Nana, bana iya baccin yanda ya kamata. Kullum tunanina yanda zan samu haɗuwa da ke, Nana ki bani dama nazo gidanku, ki bani dama na gabatar da kaina a wajen iyayenki, na tabbata zasu karɓeni” fashewa ta yi da kuka tana ci gaba da kallonsa, she wish zata iya bashi wannan damar, ta juya tana kallon ƙofar reception ɗin gudun kada Sultan ya fito. Ganin bata ganshi ba ya sanya ta juyo tana kallonsa ta ce“Sir baka gane halin da nake ciki ba ko? Baka gane abin da nake ta faɗa maka ba ko? They won't allow me! Ba zasu taɓa barina da kai ba ni na sani...”

“Amma ai baki gwada ba Nana! At least give it a try, koda sau ɗaya ne ki gwada faɗa musu kina da wanda ki ke so, ki gwada sanar dasu abin da ke cikin ranki ki ga”

Ta dinga kallonsa amma ta kasa cewa komai, numfasawa ya yi sannan ya sake cewa“me ya kawo ki asibiti?” a ɗan rarrabe ta ce“da...da Yayana muka zo”

“Ba dai shi zaki aura ba?”

Junaid ya yi tambayar a sanyaye, girgiza masa kai ta yi, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce“yanzu ina zan sake ganinki Nana? Akwai abubuwan da nakeson faɗa miki” shiru ta yi kamar me tunani, Junaid ya sake faɗin

“ko zaki je gidan Aunty ɗinki? Sai mu haɗu acan”

Da sauri ta kalleshi dan ta gane in da yake nufi, sun saba haɗuwa acan idan taje hutu daga Aun.

“Kin yi shiru Nana”

Muryarta na rawa ta ce“But sir...”

Katseta ya yi ta hanyar faɗin “just for me Nana, saboda ni!”

Ta runtse idanunta tana jin zuciyarta nayi mata wani irin suya,

“Nana ko...”

“shikenan I'll”

Ta faɗa tana goge hawayen fuskarta wasu na sake zubowa, ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“thank you, yaushe zaki je, gobe?”

“zan kiraka ranar da zan je, cause ba za'a bar ni na fita ba gobe”

Ta faɗa a sanyaye. Junaid ya dinga kallonta yana jin kamar ya tafi da ita amma sanin hakan ba mai yiwuwa bane ya sanya ya ce“okay, zan jira kiran ki” gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya sauke numfashi ya ce“i love you Nana”

Kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“love you too sir”

Juyawa ya yi ya bar wajen da sauri jin hawaye na ƙoƙarin zubo masa. Ta dinga bin bayansa da kallo har ya nufi parking space ɗin asibitin.

“Nana!”

Muryar Sultan ta daki kunnuwanta, sai da ta ɗan firgita, ta sake goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta juya tana kallonsa. Bin ta ya dinga yi da kallo sai kuma ya taɓe baki, bai ce komai ba ya kama hannunta suka nufi hanyar fita daga asibitin, mamaki ya sanya ta kasa yin shiru duk yanda take jin zuciyarta a dagule ta ce“Yaya ina zamu je? Where's ur ride?”

Cak taga ya tsaya, ya saki hannunta ya juyo yana kallonta fuskarsa a tamke kamar bai taɓa dariya ba ya ce“which ride? Bayan motar da ki ka gama ɓata min da ƙazanta” Saurin kallonsa ta yi ya gyaɗa mata gira, ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin kunya na rufeta, she wish ma bata tambayeshi ba, da wannan amsar daya bata. Lura da yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya ya ci gaba da tafiya yana ɗan murmushi, ta dinga bin sa a baya kamar babu laka a jikinta.

Napep ya tsaida musu ya shiga ciki, ganin yanda ta tsaya yasa a fusace ya ce“sai nazo na ɗauke ki ne?” bata ce komai ba ta shiga ta zauna ta takure jikinta a gefe ɗaya ta zuba uban tagumi, ya kalleta sai kuma ya dauke kansa. Sai da suka zo off Girei road sannan ya sauka daga napep ɗin ya tsallaka ya shiga wani eatery dake ɗaya side ɗin, har ya dawo bata san ya fita ba dan zuciyarta tana can gurin masoyinta Junaid, tun da suka rabu take tunaninsa, tana jin ina ma ta bishi sun tafi tare.

“Keee!”

Sultan ya yi maganar yana kallonta, da sauri ta karɓi ledar da yake bata murya a sanyaye ta ce“an gode”

“me ki ke tunani?”
Chapter 6 · 0% Book details