← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 125

Sashe 50

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ƙare maganar tana mai da kanta ga kallon waje. Aunty Khadijah ce ta matse hannunta murya can ƙasa ta ce“ke wace irin shashasha ce?”

Juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“Mom kin ji fa abin da ya ce, ya ma za'a yi na yarda da wannan mutumin ya wani taɓani. Ni gaskiya a'a!”

Ta sake ɗauke kanta. Shiru Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta mai da Idanunta kan malamin wanda yake kallonsu tun ɗazu ba tare da ya ce komai ba, ta ɗan kirkiri murmushi kana ta ce“Malam babu wata hanyar ne? Ko ni na fansheta, ka ga budurwa ce wallahi bata taɓa sanin namiji ba”

Haɗe rai ya yi muryarsa babu wasa ya ce“to idan kin fansheta kece zaki aureshi? Kada ku manta gobe ne ɗaurin aure nan, dan haka ni babu ruwana zaɓi ya rage naku”

Aunty Khadijah ta yi shiru dan jikinta ya yi sanyi, ta kalli Kaddu wadda ita ma su ɗin take kallo sai kuma ta mayar da idanunta kan Siyama ganin yanda ta juyar da kai yasa ta ce“zo ki ji” daga haka ta miƙe tana riƙe hannunta. Soro na biyu ta jata tana mata wani irin kallo ta ce“kina son ki lalata mana aiki ne? Kin san wahalar da muka sha har muka kawo i yanzu?”

Siyama ta tura baki tana leƙan ciki ta ce“to wai Mom baki ji me ya ce ba, wai na bashi jikina zai min wani aiki. Ni wallahi ba zan iya ba”

Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to mene ne a ciki? Duk ba ke ake nemawa farin ciki ba? Shi ne zaki watsa mana ƙasa a ido”

Siyama ta yi rau-rau da idanu ta ce“kenan na yarda na bashi kaina? To shi kuma Safwan ɗin fa? Idan aka yi auren ya gane ni ba budurwa ba ce”

Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta ce“to taya za'a bar shi ya gane? Ko ma ya gane me zai iya bayan kin riga da kin mallakeshi. Ai babu yanda zai yi da ke, kuma wannan aikin da za'a yi shi ne zai saka ya bijirewa gidan ya ce shi ke yake son aura ba wacce yarinyar ba. Kin ga idan har baki yarda ba shikenan mun ɓata lokacinmu a banza, kuma burinmu ba zai taɓa cika ba”

Siyama ta yi shiru tana kallonta ba tare da ta ce komai ba, tunaninta ya kasu gida biyu, ta yarda da abin da ake faɗa mata ko kuma ta ƙi yarda. Jin bata ce komai ba yasa Aunty Khadijah faɗin

“Mu je ko”

Kasa yi mata musu ta yi, ta samu kanta da bin bayan mahaifiyar tata wanda ke nuni da cewa ta amince da duk abin da ta ce.

****
Around 6:00 na yamma motarsu ta yi parking a compound ɗin gidan, kasancewar ranar ake yinin yan mata yasa ko ina yake a cike. Jama'a an taru sai shige da fice ake. Amma ce ta fara fitowa daga motar sannan Nana ta fito, Amma ta riƙeta tana sake mata sannu, Abba ya kalli Sultan wanda ke tsaye ya ce

“Kaje ka huta Sultan ka sha wahala”

Girgiza kai ya yi ya ce“ba komai Abba. Bari naje na faɗawa Hajiya Babba”

Abba ya ce“a'a kada ka sanar da ita yanzu, a bari ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Ka ga yanzu jama'a sun taru” Sultan ya jinjina kansa kafin ya ce“,haka ne kuma, to bari naje ciki” okay kawai Abba ya ce sannan ya amshi ledojin drugs ɗin da ke hannunsa. Yabi bayan su Amma dan tun fitowarsu ta shige ciki ita da Nana. Ta ƙofar baya ta shiga gudun kada mutane su damesu, ta kai Nana bedroom ɗinta ta zauna sannan ta ce

“Sannu bari na kawo miki abinci”

Riƙe hannun Amma ta yi tana girgiza kanta ta ce“na ƙoshi Amma” Amma ta zauna gefenta ta jawota jikinta ta rungumeta muryarta na rawa ta ce

“Nana dan Allah ki kwantar da hankalinki, kada ki yi abin da zai sa mu rasaki. Ba zamu jure ba, dan Allah dan Annabi ki yi hakuri ki bar maganar nan kin ji" Amma ta ƙare maganar tana ɗago kanta. Murmushi mai haɗe da hawaye Nana ta yi kafin ta ce“na bari Amma, wallahi na bari. Ba zan sake maganar ba, koda auren Yaya Safwan na nufin rasa rayuwata zan aureshi, ba zan bari Abba ya yi baƙin ciki dani ba”

Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin shessheƙar kukanta. A hankali ta dinga shafa bayanta tana sake bata haƙuri. Ana haka Aunty Ramlah ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonsu ta ce“Yaya ya jikin Nanar?”

Ganin yanda duk suke kuka ya sanya jikinta ya yi sanyi fiye da misali, ta zaune gefen gadon murya a sanyaye ta ce

“Lafiya dai Yaya?”

Amma ta ɗago kanta tana janye Nana daga jikinta ta ce“da sauƙi Alhamdulillah” daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin. Da idanu Aunty Ramlah ta bita sai kuma ta kalli Nana wadda ta kwanta kamar gawa ta ce

“Nana ya jikin?”

“Da sauƙi”

Ta ce a sanyaye tana rufe idanunta. Aunty Ramlah ta ɗan yi jim sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin.

Bayan sallar magriba Zahra ta shigo parlon Amma tana neman Nana, Amma ta sanar da ita tana cikin daƙinta dan haka ta nufi ɗakin kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba sai Nanar dake kwance tsakiyar gado idanunta a lumshe sai dai ba bacci take ba, ta tsaya a gefen gadon tana ƙare mata kallo sai kuma ta ce

“Nana”

Kamar a mafarki haka Nana taji saukar maganarta, dan haka ta buɗe idanunta a hankali tana kallonta. Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune tana girgiza kanta cikin kuka ta ce

“Dan Allah dan Annabi Aunty Zahra ki barni haka, ki rabu da rayuwata haka. Na fadawa Abba bana son auren amma yaƙi saurarata, dan Allah dan Annabi ki bar ni haka, ki rufa min asiri”

Zahra ta yi wani irin kyakkyawan murmushi sai kuma ta kai hannunta ta dafata. Nana ta dinga kallonta ganin bata ce komai ba, after 2mins ta sauke numfashi ta ce“Nana ni ba wai ina son cutar da ke bane, Ni bana nufinki da sharri. Yanzu ma naji an ce baki da lafiya ne nace bari na zo na duba ki, dan haka ki kwantar da hankalinki”

Nana ta yi shiru tana kallon Zahra da mamaki, Zahra ta sanya hannunta ɗayan ta goge mata hawaye da ke zubowa kan fuskarta ta ce“let bygone be bygone, ki bar damun kanki kada wani ciwon ya sameki” ban da gyaɗa kai babu abin da Nana ke yi dan duk zatonta Zahra ta zubar da makaman yaƙinta ne. Dan haka taji damuwarta ta ɗan ragu da kashi 40, suna nan zaune kowa ya yi shiru aka buɗe ƙofar ɗakin, Maimoon ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar lace ɗin da aka musu, fuskarta ta sha makeup wadda ta ƙara mata kyau. Ta dinga kallon Zahra fuska a haɗe sai kuma ta ƙaraso wajen ta zauna gefen Nana na dama ta riƙe hannunta ta ce

“Nana ya jikin naki?”

A sanyaye ta ce“Da sauƙi”

“ɗazu make up artist ta zo za'a mana make up aka zo kiranki aka ce wai kuna asibiti, Nana ki daina damun kan ki kinji”

Gyaɗa mata kai kawai Nana ta yi, dan da gaske magana wahala take mata. Zahra ta dinga kallon Maimoon ganin bata kulata ba, Maimoon kuwa ɗauke kanta ta yi dan ba zaka taɓa cewa taga Zahra a wajen ba, cikin son cusa mata takaici ta ce

“Yanzu uncle zasu shigo ma, dashi da Haule amaryarsa. Nana kin ganta kuwa? Kyakkyawa da ita”

Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ni na warke fa”

Maimoon ta harareta tana sake riƙe hannunta ta ce“to dan kin warke ba za'a zo a dubaki ba? Harda angonki ma Yaya Safwan zasu zo”

Nana ta yi shiru tana jin ƙirjinta na tsananta bugu, haka kawai idan taji an yi maganar Safwan sai taji ƙirjinta na bugu da sauri. Ta lumshe idanunta wanda ya bawa hawayen dake cikin kurmin damar gangarowa kan fuskarta. Zahra na ƙoƙarin tashi aka sake buɗe kofar ɗakin, dan haka ta tsaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya har suka gama shigowa. Sultan ne sai Safwan, Aliyu, Hamid, Abdusammad, Hamida, Amrah, da kuma Haule.

Zahra ta koma ta zauna ba tare da ta ce komai ba, sannu suka dinga yiwa Nana kowa na jinjina al'amarin barin ganin yanda ta rame ta ƙarmashe kamar ka hureta ta faɗi. Maimoon da ke son baƙanta ran Zahra ta kalli Safwan ta ce

“Yaya baka ga matarka ba? Abar tausayi”

Murmushi kawai ya yi idanunsa zube kan Nana wadda yake ganin ta ƙara wani irin kyau duk da ramar da ta yi, Ganin haka yasa Maimoon ta ce“gobe i yanzu dai ai tana gidanka sai dai idan ɗan baƙin ciki ya mutu!” ta ƙare maganar tana hararar iska. Babu wanda ya fahimci abin da take nufi a wajen sai Abdusammad duk da shima bai gane da wata take ba.

Hamida ta girgiza kanta tana sake kallon Nana ta ce“Allah sarki Nana kamar ba ke ba duk kin rame, ki daina saka komai a ranki kin ji”

“To me zata saka a ranta daman? Bayan tana cikin rufin asirin dangi da yan uwa, ji fa kowa anan nata ne. Duk nan danginta ne, ai yan uwa sun fi komai daɗi”

Maimoon ta sake maganar tana satar kallon Zahra, kamar yadda ta yi tunani haka ce ta faru kuwa dan iya ɓaci ran Zahra ya ɓaci amma gudun kada a gane ya sanya ta danne bata ce komai ba. Haka suka dinga hira ana zolayar juna wanda ya sanya Nana ta saki jikinta har da dariya wadda rabonta da dariya har ta manta. Aliyu ya dinga kwasar Abdusammad da maganar Haule wadda ta yi shiru ta sunkuyar da kai saboda kunya irinta Fulani, hakan kuma ya sake tunzura Zahra ba kaɗan ba. Daga ƙarshe ta tashi tana kallon Nana ta ce
Chapter 50 · 0% Book details