Sashe 45
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“To idan bai auri Nana ba ni zan saka a kawo masa mata daga gidana, Akwai yarinyar wajen Kaltume Haule sai ya aureta dan wallahi sai ya ƙara aure” ta ƙare maganar tana gyaɗa kai. Abdusammad da ke zaune kusa da Papa ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, Abba ya yi shiru can kuma ya ce“Amma Atta...”
Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu. Cike da masifa ta ce
“Wallahi ba za'a fasa maganar auren nan nasa ba, dole ne sai ya yi aure dan ba zai ci gaba da zama da wadda ba danginsa ba, tana haifa masa ya'ya muna haɗa zuri'a da wasu can bare”
“Atta kina da gaskiya, Nima ina goyan bayan ya ƙara aure. Dan daman nayi shiru ne kawai dan na ya ba da hankalin yarinyar, amma tun da har akwai wadda za'a iya haɗa sun kawai a haɗa su, son samu ma a haɗe da auren duka a yi ranar Juma'an”
Da sauri Abdusammad ya kalli Hajiya Babba wadda ta yi maganar a nutse, Lokaci ɗaya ya ji jkinsa ya yi wani irin sanyi. Dan ya san ko da wasa ba zai taɓa tsallake umarninta ba. Dan haka ya sauke kansa a hankali. Abba daya lura da yanayinsa ya ɗan yi jim can kuma ya kalli Papa da har yanzu bai ce komai ba ya ce
“Yaya kana ji fa”
Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Ai duk abin da suka yanke dai dai nan Ahmad. Daman bai yi shawara da kowa ba sanda zai aurota, bai kallemu matsayin iyaye ba yaje ya yi son ransa. Dan haka yanzu dan an aura masa ƴar dangi ai bana jin zai ƙi amincewa.”
Shiru Abba ya yi dan tun da yaji duk sun ce haka to babu makawa sai sun saka ya sake auren, Abdusammad ya tashi ba tare da ya ce komai ba ya fice daga parlon. Da harara Atta ta bi shi sai kuma ta ce“Ka daɗe baka yi zuciya ba. Wallahi tallahi sai ka yi auren nan, idan ma wani surkullen aka yi maka sai mun warware shi”
Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Atta kenan”
“To ai naga kamar ba kansa ɗaya ba, ji ana maganarsa ya tashi ya mai da mu gantallalu” Abba bai sake cewa komai ba ya mike ya musu sallama ya bar parlon shima. Atta ta buɗe baki sai kuma ta yi kwafa ta ce“Ɗan uwan ɗayan, wato dan ya tashi shi ne shima ya tashi to ku je da baƙin halinku”
Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“Atta ki shiga ciki ki huta kin deɓo gajiyar hanya”
Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a kafin na shiga cikin a kira min Sulaimanu ya je ya ɗauko Haule a gida” Toh kawai Hajiya Babba ta ce dan ta san halinta da kafiya, tun da ta ce hakan ba zata tashi ba har sai ta gama abin da ta yi niyya.
****
Aunty Khadijah da ke zaune gefen Kaddu ta girgiza kanta idanunta cikin na malamin ta ce“to yanzu mene ne abun yi? Gaba ɗaya Zahra ta fara bijirewa maganata, sam bata ɗaukan abin da nake faɗa mata. Ni kawai gara da kan ka ka yi min maganin waccan yarinyar, ko a yi mata kurciya ta bar gidan kawai. Ko kuma ta shiga duniya”
Malamin ya yi shiru kamar me tunani, can kuma ya fashe da dariya ya ce“babu wata duniya da zata shiga. Sannan babu ruwanmu da yarinyar a cikin aikin da zamu yi yanzu” Aunty Khadijah ta kalli Kaddu sai kuma ta kalli malamin da mamaki ta ce“Ta yaya haka zai yiwu?” Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce“wannan ba damuwar ki ba ce, ni na san yanda zan saka ta yiwun. Ke dai abin da nake buƙata daga gareki shi ne ki bada haɗin kai”
“Ni wannan ba damuwata ba ce, muddin zan samu biyan buƙata to koma mene ne zan yi shi. Kawai ka tabbatar da cewa Siyama ta shiga cikin wannan gidan a matsayin suruka. Ko suna so ko basa so”
Aunty Khadijah ta yi maganar a ɗan fusace. Jinjina kai Malamin ya yi ya ce“Ki ɗauka an gama wannan maganar!”
****
Washegari ta kama ranar Laraba, wanda a ranar ne zasu yi henna's party a cikin estate ɗin. Ƙarfe 8:00 na safe Maimoon ta shigo apartment ɗin, Amma na ƙoƙarin shiga kitchen dan fitowar kenan ta ganta. Gaisheta ta yi ta amsa sannan ta ce“Nana tana ciki?” gyaɗa mata kai Amma ta yi kafin ta ce“eh tana ciki” okay kawai ta ce sannan ta nufi bedroom ɗin Nana.
Tura ƙofar ta yi ta hangeta zaune ƙasan gado ta jingina da jikin gadon fuskarta a rufe, mayar da ƙofar ta yi ta rufe sannan ta ƙaraso ciki tana kallonta a sanyaye ta ce
“Nana!”
Shiru taji ta yi mata, dan haka ta durƙusa tana ƙoƙarin janye hijabin jikinta ta ce“Nana mene ne...”
Cak maganar ta maƙale a maƙoshinta saboda jinin data ga yana zuba daga bakinta, ta ɗagota a ruɗe tana faɗin
“ke Nana, mene ne ya same ki? Mene ne?”
Kasa bata amsa Nana ta yi sai hannunta data riƙe gam tana sauke wani irin numfashi.
Maimoon ta mike da niyyar barin wajen ta sake riƙeta tana girgiza mata kai. Dawowa ta yi ta tsuguna tana riƙe da hannunta ta ce“Bari naje na faɗawa Amma” girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta. Maimoon ta rasa abinda zata yi sai kawai ita ma ta fara kukan, Haka suka dinga rera kukansu ba tare da wani ya jiyo su ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan suka bawa kan su haƙuri, Maimoon ta ɗago fuskarta wadda ta yi caɓa caɓa da hawaye tana kallon Nana ta ce“tashi ki wanke jikinki” gyada mata kai kawai ta yi sannan ta mike a hankali ta nufi toilet. Ita kuma ta naɗe laddumar ta ajiye kan drawer tana ƙoƙarin juyawa wayarta da ke gefen drawer ta fara ringing, dan haka ta kai hannu ta dauki wayar tana ƙarewa sunan da ta gani akan screen ɗin da kallo.
“Junaid?”
Ta ce a fili da mamaki. Ganin wayar ta katse yasa ta mayar zata ajiye sai ga text message ya shigo, kamar bata duba ba sai kuma ta kai hannu ta buɗe wayar gaba ɗaya dan ta riga da ta san password ɗinta. Text message ne da bai shige layi biyu zuwa uku ba an rubuta
_Kina ɗaukan maganganuna wasa ko? To idan Allah ya kai mu an jima lalatattun hotunanki zasu isa ga mahaifinki, dan yanzu ma haka na samu numbern wayarsa. Idan kina son ki tabbatar ki hau WhatsApp na tura miki._
Maimoon ta dinga karanta saƙon ba tare da ta fahimci inda ya dosa ba, lalatattun hotuna? Mahaifinta? Sai kawai ta shiga WhatsApp dan already wifi ɗin ta a kunne yake.
Babu inda bata duba ba amma sam bata ga lambar Junaid ba, ballantana taga saƙon da yake magana akai, kaf unreads ɗin dake wayar Nana da basu shige ashirin ba babu wanda bata duba ba, ganin wadda ta yi magana da ita last Khadijah ce ƙawarta ta Aun yasa ta shiga tana duba chats ɗin su. Ganin bata samu komai ba ya sa ta fita tana sake duddubawa. Can ta hango lock chats ta yi ƙoƙarin buɗewa ta ga ya nuna mata sai ta saka Face id, Ta yi tsaki har sannan tana rike da wayar. Nana ta fito daga toilet ɗin tana goge fuskarta wadda take a jiƙe. Ganin Maimoon tsaye da wayarta a hannunta yasa taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa, nan da nan tari ya turnuƙeta, da gudu ta karasa gabanta ganin tana shirin faɗuwa ta riƙeta tana mata sannu. Har gaban gado ta kawota sannan ta zaunar da ita ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta shiga ganin Amma bata ciki yasa ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta dauki ruwan gora da cup ta fito da sauri. Ɗakin ta koma ta samu Nana in da ta bar ta sai sauke numfashi take dakyar, ta zauna gefenta sannan ta ɓalle murfin robar ta tsiyaya mata ruwan ta miƙa mata. Amsa ta yi ta shanye tas sannan ta bata cup ɗin tana sauke numfashi.
“Ko na ƙara miki?”
Girgiza kanta ta yi tana lumshe idanu. Maimoon ta ajiye robar a ƙasa tana kallonta, After 5mins ganin kamar ta dawo nutsuwarta yasa ta ce
“Nana”
A sanyaye Nana ta juyo ta kalleta sai kuma ta ce“na'am"
Yanda ta yi maganar kamar ba ita ba yasa Maimoon ta dinga kallonta. Sai a sannan ta lura da ramar da ta yi, gaba ɗaya ta sauya kamar ba ita ba. Wuyanta duk ƙasusuwa sun fito duk da daman bata da wata ƙibar arziki, amma ramar tata tafi ƙarfin ta fargabar aure. Idanunta kuwa sun ƙara firfitowa waje kamar zasu faɗo. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
“Wane hotuna Junaid yake magana akai Nana? Yaushe ki ka ci gaba da kulashi? Wasu lalatattun hotunanki ne a hannunsa? Kuma ya akai ya same su.? Me ya sa yake cewa zai faɗawa Abba?”
Maimoon ta jera mata tambayoyin tana kallonta. Da sauri Nana ta kalleta Lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idanunta, ta kalli wayarta dake hannun Maimoon sai kuma ta kai hannu da sauri zata karɓa, Maimoon ta janye hannunta ta ce
“Sai kin fara faɗa min mene ne abin da ya haɗa ki da Junaid?”
Cikin kuka Nana ta ce“Dan Allah Maimoon ki bani wayata, dan Allah ki bani”
Tashi tsaye Maimoon ta yi tana mata wani irin kallo ta ce“Wallahi ba zan baki ba har sai kin faɗa min abin da ya haɗaki dashi. Ki faɗa min wasu hotunanki ne a hannunsa, Idan ba haka ba na rantse sai naje na faɗawa Amma yanzun nan, idan yaso ita ta saka ki faɗa!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 29...