← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 125

Sashe 21

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Me ya sa ki ka mareta bayan ta gaba take dake? Wannan ne abin da aka koya miki raina na gaba da ke?" Girgiza kanta ta yi tana murza idanunta, ya ce"kar ki sake faɗa da kowa kin ji yarinyar kirkina" yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanyata gyaɗa masa kai, Zahra dake tsaye bayansu ta yi murmushi. Ƙarasowa wajen ta yi tana riƙe da Noor, ya kama hannun yarinyar ya dorata akan cinyarsa yana murmushi ya ce"my angel" wasa ta fara yi da gemunsa tana dariya, Zahra ta nufi hanyar kitchen dan ɗora musu abun breakfast. Tashi Nana ta yi tana faɗin"na tafi uncle" haɗe fuska ya yi ya ce"dawo nan" ganin yanda ya yi maganar babu alamun wasa ya sa ta koma ta zauna tana kallonsa.

"Korar ki ake anan ɗin da ki ke sauri haka?"

Ya ƙare maganar yana harararta, sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, ya mai da idanunsa kan Noor ya ce"kin yi azkar?" gyaɗa masa kai ta yi cikin ƙaramar muryarta ta ce"mun yi da Aunty Nana" jin jina kansa ya yi ya ce"uhm, Aunty Nana ta iya ashe?" kamar jira take ta ce"eh Abbiey ta iya sosai, har ma fa karatun Qur'an muka yi, gashi muryarta da daɗi, kamar kai" daga shi har Nana dariya suka dinga yi, Ya ja kumatunta ya ce"to ko dai ita zata koma tutor ɗin ki?" gyaɗa masa kai ta yi tana wani juya idanu kamar babba ta ce"eh Abbiey, ta iya koya karatun"

"Na kai Abbiey?"

Nana ta yi maganar tana jawo hannunta, jin jina kanta ta yi tana murmushi, ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"iyye au ta fini? Oya sauka ki koma jikinta to" sake narkewa ta yi a jikinsa ta dunƙule hannunta na dama ta daki ƙirjinsa ta ce"a'a fa Abbiey, babu wanda ya fika even Ummina sai dai ta biyo bayanka, u're the best Daddy in the world" rungumeta ya yi tsam a jikinsa yana murmushi ya ce"daɗina dake hankali princess" dariya ta dinga yi ƙasa-ƙasa dai dai nan Zahra ta fito daga kitchen ɗin tana kallonsu ta ce"kun bar ni ina ta faman aiki ku kuma kuna nan kuna hira ko?" Tashi Nana ta yi tana fadin"Ayyah Aunty mu je na tayaki" taɓe baki ta yi ta ce"da can baki ce zaki tayanin ba sai da na roƙa? To ki yi zamanki, nima dai an jima zan je gidan namu yan'uwan tun da abun haka ne" tuntsirewa da dariya Nana tayi tana nufar kitchen ɗin ta ce"aaa kar ki kai mu in da Allah bai kai mu ba" Zahra ta yi murmushi ta ce"ai gaskiya ce" daga haka ta sake kallonsa ta ce"yallaɓai kai ba zaka taya mu ba?" Ɗan zaro idanu ya yi sai kuma ya kwaɓe fuska kamar ƙaramin yaro ya ce"a'a dai Ummi ku je ni zan zauna da princess" ko ƙarasa maganar bai yi ba ta fara jan hannunsa tana faɗin "ai ko sai ka taya mu wallahi!" Babu yanda ya iya haka ya tashi bayan ya sauke Noor ya nufi kitchen ɗin, ta yi murmushi sannan ta sauyawa Noor tashar cartoon ta bar wajen.

Nana ta dinga kallonsa ganin ya shigo kitchen ɗin, ya ɗan haɗe girarsa babu walwala ya ce"mene ne ki ke wani kallona?" Girgiza kanta tayi tana ƙoƙarin ƙunshe dariyar da ke cinta, y yi kwafa yana saka slice cucumber a bakinsa kafin ya ce"zan yi maganinki ne yarinya" ita dai bata ce masa komai ba har Zahra ta shigo, ta ɗan kallesu sai kuma ta nufi gaban cooker tana fadin"ku ka wani tsaya min a tsaye" gyara tsaiwarsa ya yi jikin fridge sannan ya ce"to ai bamu san me zamu yi ba Hajiya" sai da ta murɗe gas ɗin sannan ta ce"ga albasa nan ka yanka min, ke kuma Nana ki ferayen dankalin nan" toh Nana ta ce sannan ta ɗauki wuka ta fara abin da ta sakata. Zahra ta juyo tana kallonsa ganin har sannan bai ko motsa ba yasa ta ce"ai ko idan baka yi aiki a gidan nan ba yau ba zaka yi breakfast ba!" Kamar zai yi kuka ya ce"wai da gaske?"

"Abbiey da gaske nake" ta ƙare maganar tana matsowa gabansa, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta ya dinga kallonta kafin a hankali ya kai bakinsa kan nata, saurin janyeshi ta yi tana rarraba idanu, ya ɗan haɗe fuska ya ce"mene?" da idanu ta nuna masa Nana wadda take faman feraya, ya taɓe baki sai kuma ya ce"and so?" Daga haka ya sake kai bakinsa, kasa hana shi tayi tana ji ya yi kissing ɗinta a deep one. Ƙarar kissing ɗin ya sanya Nana juyowa, amma ta yi gaggawar ɗauke idanunta ta ci-gaba da abin da take, cikin rashin sa'a wuƙar ta shige mata hannu saboda yanda ta diririce tamkar ita aka wa kiss ɗin. Ta saki ƴar ƙara tana janye hannunta, da sauri Zahra ta janye jikinta daga wajen ta ƙarasa gabanta, sai dai jinin data gani ya ɗan ɗaga mata hankali, ta ce"subhanallahi Nana garin yaya?" Ƙarasowa wajen ya yi ya kama hannun wanda yake ta zubar jini sai kuma ya ce"garin gulma ya sanya ki ka yanke ko?" wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Jan hannun ya yi wajen sink ya kunna ruwan, sai dai yana wankewa wani jinin na sake zuba, dan haka ya kashe kawai ya kalli Zahra ya ce"ban tissue" cikin hanzari ta zari tissue ɗin ta miƙa masa, ya naɗeta dayawa sannan ya ɗora a wajen, ta ɗan runtse idanu saboda zafin da taji. Cikin yan sakanni tissue ta jiƙe jagab da jinin ya ɗan yi tsaki sai kuma yaja hannunta bai ce komai ba suka fita daga ɗakin. Zahra ta yi kamar ta bi su taji ya ce"Madam concentrate on what you are doing" cak ta tsaya ba dan taso ba, ta juya ta ci gaba da aikin zuciya babu daɗi.

Ɗakinsa ya shiga da ita, ta ɗan lumshe idanu saboda wani sassayan ƙamshi daya cikata, ya ƙarasa gaban dresser nashi ya dauki wani perfume na kwalba ya buɗe, ƙoƙarin janye hannunta ta fara yi ganin yana shirin fesa mata kamar za ta yi kuka ta ce"Uncle zafi fa" banza ya yi mata ya feshe wajen da turaren, tsananin azabar da taji ya sanya ta faɗa jikinsa tana sakin wani marayan kuka, ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe bai ce mata komai ba, ya mayar da turaren ya ajiye sannan ya janyeta daga jikinsa yana faɗin "next time ki tsaya gulma kin ji" daga haka ya juya ya nufi toilet, tura baki ta yi sai kuma ta koma gefen gadon daya sha gyara ta zauna, ta yi shiru tana tunanin yanda maganar, ita kaɗai ta dinga tura baki har kusan 5mins kafin ya fito fuskarsa a jiƙe da hannunsa, da mamaki ya dinga kallonta sai kuma ya ce

"Kee!"

Yanda ya yi maganar ya sanyata firgita ta sunkuyar da kanta ƙasa, fuska a haɗe ya ce"me ki ke min akan gado? Salon ki lalata min? Tashi my friend" ɗago idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce"ayyah uncle zama nayi na ɗan huta fa" a ɗan tsawace ya ce"baki ji me nace ba? Tashi ki fita!" Da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, ya bita da harara sai kuma ya yi tsaki.

****
Bayan sun kammala breakfast ta tashi ta kwashe duk kayan ta kai kitchen sannan ta kalli Zahra ta ce"Aunty na tafi"

"Ke Nana ba zaki bari sai an jima ba?"

Girgiza kanta ta yi ta ce"zan je na ɗauki wayata ne, na san an yi min magana ta WhatsApp ban gani ba" Zahra ta ce"okay amma da kin bari an jima zan je gidanmu sai mu tafi tare ki rakani, kin ga kema kya ga gari ko?" Nana ta ɗan yi shiru tana tunani

“ki bita, This is great opportunity da zaki haɗu da Junaid!”

Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan, Zahra ta sake cewa"Nana fa?"

Ɗan murmushi ta yi ta ce"Tom Aunty zan je" Zahra ta ce"yauwa yar gari, to je ki yi wanka sai ki bawa Atu tama Noor " to kawai ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs bayan ta kira Noor ɗin. Zahra ta mai da Idanunta kan Abdusammad da ke danna wayarsa hankali kwance ta ce"Yallaɓai kai zaka kai mu?" bai kalleta ba ya girgiza kansa ya ce"a'a driver ya kai ku dai, zan fita idan na dawo sai na biya na dauko ku, mun gaisa dasu Mommy ma" Zahra ta sauke numfashi kafin ta ce"okay tom bari na tashi naje na shirya kar mu yi late, idan zamu fita sai mu biya ta wajen Amma na faɗa mata ba?"
Chapter 21 · 0% Book details