Sashe 68
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yatsine fuska ta yi ta ce“ban gane nan bada jimawa ba?. Ai ina, dole ta tare gobe, bana son wani neman magana, an riga da an gama komai na al'adar auren budurwa da ita, dan haka gobe a sadata da dakin mijinta. Dan so nake na koma Njomboli kuma ban tafiya sai naga yanda zaman nasu zai kasance aradu!”
Shiru Hajiya Babba ta yi dan bata son musu da ita. Abba ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce“kul kul Ahmadi, ina ganin girmanka dan haka kar ka ce zaka saka baki anan. Ko ka manta batun yarka ake?” shiru Abba ya yi bai yi maganar ba, ta kalli Mama wadda ke faman murmushi tun ɗazu ta ce“Ke Fatime ki shiryata gobe ki kaita ɗakin mijinta. Nima zan biyo bayanku”
Da fara'a sosai Mama ta amsa. Abdusammad ya ɗan kalleta ganin yadda ta zaƙalkale tana magana, ji yayi kamar ya maƙureta saboda haushi, sai dai sanin babu yanda ya iya da ita ya sanya shi yin kwafa yana sake maida hannunsa ga fuskarsa. Duk abin nan da yake Papa na lura dashi, ya girgiza kansa a hankali. Kasa ci gaba da zama ya yi, ya miƙe yana gyara zaman rigar jikinsa ya ce
“excuse me pls”
Daga haka ya yi waje da sauri, da harara ta bi shi sai kuma ta ce“kaga shashashan ɗa? Ina magana ya yi wani fitarsa. To idan ma yarinyar ce baya son a kai masa wallahi sai dai ya ƙarata, dan gobe sai ta tare a gidansa.” Murmushi kawai suka yi sanin halin faɗanta yasa babu wanda ya tanka, ta gama barbaɗin jarabarta ta tashi ta bar wajen, Sai a sannan Abba ya sauke numfashi ya ce
“Allah ya kyauta.”
Da Amin suka amsa sannan ya yi musu sallama ya tashi ya bar parlon dan dare ya fara. Da idanu Papa ya bi shi sannan shima ya fice daga parlon.
****
Kai tsaye gidansa ya nufa, yana jin wani irin ɗaci a ransa. Zaune ya sameta a parlon Noor na kan cinyarta tana bacci, ya haye sama ba tare da ya amsa sannu da zuwan da take masa ba. Ɗakinsa ya shige ya zame duk kayan jikinsa ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya dafa bango yana sauke ajiyar zuciya jin yanda ruwan ke ratsa fatarsa. Abu ne ke neman haɗe masa goma da ashirin, idan ya tuna Nana matsayin matarsa take sai yaji duk hankalinsa ya tashi, he just can't believe a ce wannan yar yarinyar sunan matarsa take amsawa. Babu abin da ya sake ƙona masa rai sai maganganu da Atta ta yi ɗazu, kenan har wani tunanin samun wani abu take daga gare shi? Da wannan yar yarinyar, yaja wani dogon tsaki wanda bai san sanda ya kubuce masa ba. Ya ɗauki mintuna masu tsawo a haka kafin ya rage gudun showern ya yi wanka sannan ya ɗauro alwala ya fito yana sanye da bathrobe. Zaune ya sameta kan gadonsa ta yi jigum da alama jiransa take, Ya ɗauke kansa daga gareta ya nufi mirror ɗinsa, mai ya shafa sannan ya gyara kansa. Yana gamawa ya buɗe press ya dauko wasu riga da wando na bacci masu taushi ya saka, sannan ya feshe jikinsa da turare. Duk wannan abun ya dake akan idanun Zahra yake yin su, dan koda na sakan ɗaya ta kasa ɗauke idanunta daga kallonsa, wata sabuwar soyyayarsa take ji na yawo a cikin zuciyarta, ji take inama ta tashi ta rungumeshi ta yi bacci a jikinsa kamar da. Sai dai ta san yanzu hakan ba mai yiwuwa bane, dan sharadin daya kafa mata ba zata iya dashi ba, Nana ba zata taɓa yafe mata ba. Wannan tunanin ya sanya zuciyarta tsinkewa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta. Sam bata san sanda ya zo gabanta ba, bata san sanda ya zauna a gefenta ba. Sai kawai tattausan hannunsa da taji akan nata, ta yi saurin kallon hannun nata sai kuma ta kalli gefenta na dama. Gani ta yi yana mata murmushi, ai kuwa kamar jira take ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani raunataccen kuka. Hannunsa ɗaya ya ɗora a bayanta yana shafawa a hankali, ta dinga kuka kamar ba zata daina ba. Sai da ta fara jin abin da ke damunta ya fara raguwa sannan ta ɗago kanta daga jikinsa har sannan tana shessheƙar kuka. Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen fuskarsa a sake kamar ba shi ba ya ce“Ya isa haka to” jinjina masa kai ta yi tana murmushi mai haɗe da kuka ta ce“Doctor tam.” Ya ɗan yi shiru yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame kamar ba ita ba, har wasu kasusuwa ne suka mata ƙawanya a wuya. Duk wanda ya ganta sanda suka zo ƙasar nan ya kalleta yanzu ba lallai bane ya ganeta. Ya riƙe fuskarsa da duk hannayensa biyu yana murmushi ya ce
“naga kin ƙara kyau?”
Murmushi ta yi a sanyaye ta ce“doctor ka yafe mini yanzu?” shiru ya yi kamar ba zai bata amsa sai kuma ya ce“shikenan ya shige. But kada ki sake irin haka kin ji, na san ba halinki bane, ƙoƙarin ɓata ki ake but karki biye musu Zahra. Na yarda dake fiye da yanda ki ke tunani, bana son ace daga gareki aka samu matsala..dan hakan zai haifar da maganganu acikin gidan nan, ni kuma duk wanda ya zageki ko ya aibata ki ba zan ji daɗi ba. Dan haka dan Allah Zahra kar ki sake.”
Ya ƙare maganar in a very polite tone. Kasa cewa komai ta yi kawai ta sake rungumeshi tana jin wani sabon so da ƙaunar mijin nata na shigarta. Ya yi shiru yana sauke numfashi, ba komai ya sanya ya yi hakan ba sai dan zuwan da Nana za ta yi. Idan har ya nuna mata baya shiri da Zahra ba zasu taɓa zaman lafiya ba kuma hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba, dan ya san halin Nana kamar yunwar cikinsa. Janye jikinta ta yi daga nasa tana lumshe idanu, ya sake jawota jikinsa yana ƙoƙarin kunce zaren sleeping dress ɗin dake jikinta. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi ya manna mata kiss a goshi, ta sake maƙalewa a jikinsa tana rufe idanunta, tana jin sa har ya sauke rigar ƙasa, Jin hannunsa akan fatar jikinta ya sanyata sauke wata ajiyar zuciya tana ɗan ƙanƙameshi. Cikin yan sakkani kuma wasan nasu ya fara neman sauyawa..
****
Amma ta dinga kallonsa ganin kamar bai san abin da take cewa ba, Ta ajiye cup ɗin akan table sannan ta zauna gefensa a hankali ta dafashi, Ya juyo a ɗan firgice yana kallonta, a sanyaye ta ce
“tunanin me kake ne? Ina ta maka magana baka saurarena”
Girgiza kansa ya yi yana furzar da iska daga bakinsa ya ce“Abun ne, hankalina ne sam yaƙi kwanciya.” da mamaki ta ce“dame fa?”
“Akan auren Nana da Abdusammad. Gobe zata tare inji Atta, kuma kin san babu wanda ya isa yaja da maganarta, tsoro nake kada wata fitinar ta ɓullo tsakaninsu dalilin zuwan Nana.”
Shiru Amma ta yi, lokaci ɗaya taji jikinta ya yi wani irin sanyi. Can dai ta numfasa ta ce“gobe kuma? Me yasa ba'a faɗa mana da wuri ba amma?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“ai babu wani abu da za'a yi shiyasa, kawai Fatima ce zata rakata.”
“But at least ya kamata a sanar dani ko da abin da zan shirya mata.”
Abba ya kalleta wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗauke kansa yana kallon tv ya ce“kira min ita.” Toh kawai ta ce sannan ta mike jiki a saluɓe ta nufi ɗakin Nanar.
Kwance ta sameta har ta yi shirin bacci. Ta taso ta sannan ta dawo parlon ta zauna, after 2mins Nana ta fito tana jan ƙafa a hankali, hannunta ɗaya akan idanunta tana murzasu saboda baccin data fara yi. A gefen Abba ta zauna ta jingina da jikinsa, Ya gyara mata zama dan so yake ta fahimceshi ya ce
“Tashi zaune ki ji Nana.”
Toh kawai ta ce sannan ta gyara zamanta, dan tun bayan abin da ya faru bata sake masa musu ba. Ya dinga kallonta dan har ga Allah tausayinta yake, Ita ma kallon nasa take. Ganin damuwa akan fuskarsa ya sanyata wartsakewa gaba ɗaya, Ta yi shiru tana jiran abin da zai ce. Sauke nannauyan numfashi ya yi kafin ya fara magana cikin nutsuwa.
“Nana ina son ki buɗe kunnawanki ki ji abin da zan faɗa miki. Ba'a fasa aurenki ba saboda bakya nan, an ɗaura miki aure a ranar kamar yanda aka ɗaurawa yan uwanki!”
Sai da taji gabanta ya fadi, Ta zaro idanu tana kallonsa, Lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba daga idanunta, bakinta na rawa ta ce“Abb...Abba nima an yi min aure? Wa aka aura min?”
Kallonta ya yi ganin yanda take kuka a hankali yasa ya ce“banason wannan kukan kin ji. Duk abin da na faɗa miki kuma ki yarda” gyaɗa masa kai kawai ta yi, dan ita daman bata ji zata musa masa ba ko me yace kuwa. Ta shirya karɓar duk abin da Allah ya bata. Ganin ta kwantar da hankalinta yasa ya ce
“An ɗaura aurenki da uncle ɗinki Abdusammad!”
A tsaye suka ganta ta dinga kallonsa bakinta na rawa ta shiga girgiza kanta, can kuma ta yi luuu ta faɗi ƙasa a sume..
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 42.
Murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta yi bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta hangeta tsakiyar gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Amma ta sauke numfashi sai kuma ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki hannunta riƙe da mug ɗin, A kan drawer ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna tana kallonta a sanyaye, kasa ce mata komai ta yi, ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta dake tashi a sanyaye. Sun ɗauki mintuna a haka kafin daga bisani Amma ta sauke ajiyar zuciya ta dafata cikin tattausar murya ta ce
“Nana!”
A hankali ta ɗago kanta. Amma ta ƙura mata idanu ganin yanda hawaye da majina suka cika mata fuska, Amma ta girgiza kanta tana kai hannunta fuskarta ta ce“ya isa haka kin ji. Ki daina kuka”