← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 125

Sashe 51

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nana Allah ya ƙara sauƙi bari naje” toh kawai Nana ta ce ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta cewa kowa komai ba, suma hakan bai damesu ba dan ba da ita suke hirar su ba. Suna nan har kusan ƙarfe 10:00 na dare sannan Abdusammad ya ce kowa ya tafi. Nan da nan kuwa kowa ya watse ya yi apartment ɗinsu aka bar wa gobe sauran.

Zahra na zaune gefen gadon bayan sun gama waya da Aunty Khadijah idanunta ya yi luhu-luhu da alama ba ƙaramin kuka ta ci ba, ta dinga jujjuya envelope ɗin hotunan dake gabanta. Ganin lokaci na tafiya ya sanya ta mike ta zura hijabi sannan ta fice daga ɗakin.

Around 11:00 na dare Amma ta buɗe dakin ta shigo, kwance ta samu Nana ta juya baya ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa ta a hankali ta ce

“Nana!”

Buɗe idanunta ta yi dan daman ba bacci take ba, ta tashi zaune tana jingina da jikin gadon. Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“ya jikin naki?”

“Da sauƙi Amma”

Ta ce a sanyaye. Jinjina kai Amma ta yi sai kuma kowa ya yi shiru, can kuma Amma ta ce“ko zaki dada abincin?”

Girgiza kai ta yi kafin ta ce“a'a Amma na ƙoshi ma”

Amma ta jinjina kanta sai kuma ta mike ta ce“to ki kwanta ki yi bacci sai da safe”

To kawai Nana ta ce sannan ta zame jikinta ta kwanta. Amma ta rage mata gudun ac sannan ta kashe hasken ɗakin ta juya ta fita.

Nana na ganin ta fita ta tashi zaune sannan ta jawo wayarta, ta buɗe password ta koma WhatsApp cikin sa'a ta samu Khadijah na online, dan haka ta tura mata message tana tambayar meya hanata zuwa. Khadijah da ba zata iya tsayawa bata amsa ba ta kirata ta WhatsApp bayan ta ɗaga ta ce

“kin san me ya hanani zuwa Nana?”

Shiru Nana ta yi dan ba ƙaramin haushinta taji ba, Khadijah ta yi murmushi dan tasan halinta ta ce

“to Daddy ne bai dawo ba. Kin da daman nace miki sai ya dawo zan zo”

Nan ma Nana ta yi shiru tana kwanciya a kan gadon, Khadijah ta yi tsaki ta ce

“Ina miki magana kina jina banza”

Sai a sannan ta sauke wani wahalallen numfashi cikin sanyin murya ta ce

“Yaushe zaki zo?”

Ta yi maganar a takaice. Khadijah ta taɓe baki ta ce

“wai dan zaki yi aure shi ne ki ka wani fara magana da isa? To gobe”

Nana ta ce“alright zan jira ki. Ki gaida Mami”

“Zata ji, ta ce da bata da patient ai har Yola zata zo”

Ɗan murmushi Nana ta yi dan ta san Mami farin sani ta ce“Allah sarki. Ki ce ina gaisheta”
Okay kawai Khadijah ta ce sannan suka katse wayar. Nana ta ajiye wayar a gefe tana lumshe idanunta, gaba ɗaya ji take kamar ba ita ba. Tunanin abin da zai faru gobe idan har Junaid ya ji an ɗaura aurenta shi ne ya fado mata, dan haka ta gaza samun sukuni balle ta samu nutsuwar bacci.

****
Safwan ya dinga kallon wayarsa kafin ya ƙarasa da mamaki ya ɗauketa yana tsane ruwan kansa dan fitowarsa kenan daga wanka, ya ɗaga wayar ya kai kunne kafin ta yi magana ya ce

“Aunty Zahra lafiya?”

Murya can ƙasa Zahra ta ce“lafiya kalau Safwan kana gida ne?” gyaɗa mata kai ya yi kamar yana gabanta sai kuma ya ce“Eh ina ciki”

“To ko zaka ɗan fito dan Allah ina compound ɗin” toh kawai ya ce sannan ya kashe wayar har sannan bai daina mamaki ba. Ya ɗauko jallabiya a press ɗinsa ya zura sannan ya saka slippers ya fito daga ɗakin. Babu kowa a parlon dan har an kashe haske, ya buɗe ƙofar ya fito. Tsaye ya hangeta ita ɗaya ya ƙarasa a sanyaye yana kallonta ya ce

“Aunty Zahra lafiya dai?”

Zahra ta juyo tana kallonsa sai kuma ta yi murmushi ta ce“lafiya kalau Safwan kawai ina son magana da kai ne”

Safwan ya ɗan yi jim sai kuma ya ce“to ina ji”

Zahra ta ɗan kalli both hand side ɗinta sannan ta sauke numfashi ta zaro envelope ɗin daga cikin hijabi ta miƙa masa. Safwan ya dinga kallon envelope ɗin ba tare da ya karɓa ba, ganin irin kallon da yake mata na neman karin bayani yasa ta sauke hannunta sannan ta ce

“na san kasan Siyama yar Yayata ce ko? Kuma ka san nasan kana sonta, kana da burin aurenta sai dai ka rasa ta inda zaka ce baka son Nana. Ko kuma ka ce ka fasa aurenta”

Safwan ya yi shiru yana kallonta, ta ɗan murmusa sannan ta ci gaba da faɗin

“zan so ace ka auri Siyama ko dan na samu yar uwa a gidan nan. Haka kuma zan so ace ka aureta kodan farin cikinka saboda haka na zo maka da abin da zai iya sakawa a fasa aurenka da Nana koda a filin ɗaurin auren ne!”

Da wani irin mamaki Safwan ke kallonta, Zahra ta sake mika masa envelope ɗin, wannan karan samun kansa ya yi da amsar envelope ɗin, ya dinga kallonta ba tare da ya yi yunkurin buɗewa ba. Ta numfasa sannan ta ci gaba da fad'in

“Idan har ka yi amfani da abin da ke cikin envelope ɗin nan to zaka samu Siyama cikin sauƙi, koda a gobe ka ke so za'a ɗaura maka aure da ita”

Safwan ya girgiza kansa cikin rashin fahimta ya ce

“Nifa ban gane abin da ki ke faɗa ba Zahra, ban fuskanci in da ki ka dosa ba”

“Ba dai kana son Siyama ba? Kuma ita ka ke son aura ba Nana ba?”

Safwan ya jinjina kansa ya ce“Haka ne. Ina son Siyama, so irin wanda ban taba yiwa wata ƴa mace shi ba. Ina jin idan ban sameta ba kamar ba zan iya ci gaba da rayuwa ba”

Zahra ta yi murmushi dan ta tabbata ta samu abin da take so ta ce

“To idan har kana son Siyama ka yi amfani da abin da na baka, ka ce ka fasa auren Nana. Kana iya kafa hujja dashi”

“Hujja!?”

Safwan ya ce da matuƙar mamaki, gaba ɗaya kansa ya ɗaure. Zahra ta gyada kanta ta ce“Eh hujja, gobe ka gabatar dashi a gaban kowa sannan ka ce ka fasa aurenta saboda abin da kagani. Daga nan ka ce Siyama zaka aura a maimakonta”

Ji ya yi kawai ya gyaɗa mata kai ba tare da ya san ya yi hakan ba. Ta sake murmushi ta ce“ka koma sai da safe”

Daga haka ta juya ta bar wajen, Yafi mintina goma tsaye a wajen baki a sake, kafin yaja jikinsa ya koma ciki dakyar. A kan gado ya ajiye envelope ɗin sannan ya zare rigar jikinsa ya shafa mai ya dauko pyjames ɗinsa ya saka, gaba ɗaya tunani ya hana shi sakat, maganganun Zahra sai kai komo suke masa cikin ransa, yana gamawa ya koma ya zauna yana ƙarewa envelope ɗin kallo.

“Hujja?”

Ya sake furtawa da mamaki, sai kuma ya ɗauki envelope ɗin ya ɓare dan ganin abin da ke ciki, a hankali ya zaro hotunan da suke ciki, lokaci ɗaya ya mike tsaye zumbur yana ƙare musu kallo, so yake ya ƙaryata abin da yake gani amma sam ya kasa, ya sake ƙara light ɗin ɗakin ko idanunsa ke masa gizo, amma ga mamakinsa sai ya ci gaba da ganin abin da ya gani ɗazun. Cikin wani irin tashin hankali da faduwar gaba ya dinga kallon hotunan ɗaya bayan ɗaya, hannunsa sai rawa yake yana girgiza kansa da sauri, gaba ɗaya kusan rasa nutsuwarsa ya yi. Ya yi zaman yan bori a ƙasa kawai sai yaji wasu zafafan hawaye na zubowa daga cikin Idanunsa, bakinsa na rawa ya shiga furta

“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 32.

Ya dinga maimaitawa ko zai samu sauƙin abin da yake ji cikin ransa. Yana nan zaune har bayan mintuna talatin sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya kwashe hotunan ya haɗe su waje ɗaya ya mayar inda suke sannan ya zura cikin drawer. Dakyar ya ja jikinsa ya koma gefen gado ya zauna ƙwaƙwalwarsa cike da tunani kala-kala. A ina aka sami wannan hotunan? Da gaske kuma Nanar daya sani ce? How? Su ne tambayoyin da suka fi tsaya masa arai. Ya ji kamar ya tashi ya koma ya tambayi Zahra sai dai bashi da halin yin hakan, dan lokacin 12 na dare ta kawo kai. Dan haka ya dinga saƙa da warwara shi kaɗai yana tunanin abin da zai wakana gobe.

A ɓangaren Zahra kuwa tana koma gida kitchen ta shige, ta zaro wayarta dake cikin hijabi ta yi dialing numbern Aunty Khadijah. Kasancewar ta san da kiran yasa ringing ɗaya ta ɗauka daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah ta ce

“Zahra ya dai.”

Sai da ta kalli ƙofar kitchen ɗin dan tabbatar da babu kowa a wajen sannan ƙasa-ƙasa ta ce

“Nagama komai fa, na bashi hotunan”

Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta ce“yauwa Zahra aikinki ya yi kyau. Yanzu sauran ya rage namu, daman gobe da wuri zamu zo gidan”

Jinjina kai Zahra ta yi sannan ta kashe wayar, ta jingina da jikin cabinet tana tunanin abin da ta aikata, dai dai tayi? Ko kuma ba dai dai ba. Sanin babu wanda zai faɗa masa gaskiya a sannan ya sanya taja jikinta ta fice daga kitchen ɗin.

Koda ta shiga daƙinta kwanciyarta ta yi dan ko Abdusammad bata nema ba, shima kuma bai nemetan ba saboda ayyuka da suke neman shan kansa.
Chapter 51 · 0% Book details