Sashe 35
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda ta koma apartment ɗin Zahra bata samu kowa ba kamar ɗazu dan haka ta haye sama da sauri ta koma ɗakin da take, tana shiga taji wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, sai da ta zare hijabin jikinta ta ajiye gefen gado haɗe da kit ɗin data karbo sannan ta ƙarasa ta dauki wayar, Junaid ta gani a jikin numbern dan haka ta buɗe sakon gaba ɗaya
_Nana kenan, kin ɗauka zan iya rabuwa da ke haka cikin sauƙi? Kin ɗauka ban san me nake ba, ban fara son ki dan na barwa wani ke ba, ina sonki ne dan na rayu da ke, ina son ki kalla saƙon dana baki da kyau kafin ki yankewa kan ki hukuncin, amma ki sani ba zan taɓa yarda ki bar ni ba, komai runtsi komai walaha ke tawa ce, tawa ni kaɗai NAANAH!_
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 22.
Nana ta dinga kallon saƙon da wani irin mamaki, me yake nufi to? Wace magana yake? Girgiza kanta ta yi da sauri kuma ta kalli inda ta ajiye kit ɗin data shigo da ita, cikin hanzari ta ƙarasa gaban gadon ta zauna sannan za jawo kit ɗin ta fara buɗeta a hankali, har ta gama buɗewa gabanta faduwa yake, ta zaro hanky ɗin da yake magana sai ƙamshin turare yake, kallonsa ta dinga yi tana jujjuya shi, a fili ta ce“to me yake nufi?” sai kuma ta ajiye shi a gefe tana ƙoƙarin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin da take cikin. Ƙura mata idanu Nana ta yi kafin ta sanya hannunta na dama ta ɗaukota, haka kawai ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa, ta runtse idanunta a hankali ta ce
“Ya Allahu”
Ta sauke numfashi kafin ta fara ƙoƙarin buɗe envelope ɗin bugun zuciyarta na sake tsananta, hannunta ta sanya ciki tana taɓa takardun dake ciki, da mamaki ta janyo su duka tana sake ware idanunta dan ganin mene ne a ciki, wata irin zabura Nana ta yi ta miƙe tsaye jikinta ya fara wani irin rawa kamar ana kaɗa ganga, baki buɗe take kallon hoton wanda ya kasance hotonta ne kwance kan gado daga ita sai ƙaramar vest wadda bata kai ga rufe cibiyarta ba, sai ɗan ƙaramin underwear, kanta a buɗe babu dankwali.
Ta durƙushe a ƙasa tana wani irin numfashi dan tsabar tashin hankali kuka ya gagara zuwar mata, hannunta na rawa ta janye hoton inda na biyunsa ya bayyana kuma wanda ya fishi muni, hotonta ne da waccan shigar wannan karon ma a kwance sai dai a kusa da ita Junaid ne daga shi sai boxer, ta sanya hannunta ta rufe bakinta jin wani irin kuka yana neman tawo mata. Haka ta dinga buɗe hotunan ɗaya bayan ɗaya har ta kai ƙarshe, lokaci ɗaya ta yi jifa da hotunan tana sakin wata irin matsananciyar ƙara, dai dai lokacin Zahra ta shigo ɗakin da sauri tana kallon ta ta ce“Nana lafiya mene ne?”
Bata iya bata amsa ba sai wani irin numfarfashi take, ganin haka yasa Zahra ta ƙarasa inda take durƙushe da sauri ta dafata tana faɗin “mene ne Nana? Meke damunki? Baki da lafiya ne?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta faɗo jikinta a sume, Zahra ta dinga jijjigata cikin tashin hankali tana faɗin
“ke Nana! Mene ne? Me aka miki?”
Ganin bata san ma tana yi ba ya sanya Zahra ta kwantar da ita a ƙasa ta tashi da sauri ta fice daga ɗakin, ba'a jima ba ta dawo hannunta riƙe da rogar ruwa mai sanyi, ta ƙarasa inda take sannan ta buɗe robar ta ɗan yayyafa mata ruwan, ajiyar zuciya Nana ta sauke ba tare da ta buɗe idanunta, Zahra ta ajiye ruwan a gefe sannan ta ɗagota tana cewa“mene ne Nana? Meya faru? Ke da wa?” Bata ce komai ba, dan babu alamar ma tana fahimtar abin da Zahran ke cewa, Banda numfarfashi babu abin da take. Zahra ta rasa yadda zata yi da ita, dan haka ta tashi da niyyar ɗaukan wayarta ta kira Abdusammad, Sai dai takardar da taji ta taka a ƙasa ya sanya ta kalli wajen da sauri, da mamaki take kallon farar takardar dan hoton a kife yake, ta ɗan sunkuya ta ɗauko sannan ta juya shi, saurin ja da baya ta yi ta riƙe gefen dresser ta dinga kallon hoton baki buɗe, lokaci ɗaya kuma ta mai da Idanunta kan Nana da ke kwance gefe, girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa kan fuskarta, ta yi wurgi da hoton sai kuma ta sake kallon ƙasa sai a sannan taga tarin hotunan dake warwartse a wajen, ta bi kowanne ta ɗauko sannan ta ajiye gefen drawer ta koma kusa da Nana ta zauna tana kuka ta ce“Nana garin Ya ya? Me ya sa? Me yasa zaki yiwa kan ki haka? Me yasa?” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka, Kasa cewa komai Nana ta yi sai wani irin kuka daya kwace mata, ta ɗora kanta kan cinyar Zahra ta dinga rera kuka kamar ranta zai fita. Kasa hanata Zahra ta yi dan ta san akwai buƙatar ta yi kukan duk da ba shine mafitarta a yanzu ba, Kusan mintuna goma kafin ta fara rage sautin kukan nata, Zahra ta ɗago kumburarrun Idanunta ta kalleta cikin kuka ta ce“Akan me ki ka yi haka Nana? Yaushe haka ta faru? Meya sa?”
Ɗago kanta ta yi daga jikin Zahra, ta kasa kallonta dan har sannan hawaye basu bar zuba kan fuskarta ba, Zahra ce ta yi ƙarfin halin sanya hannunta ta fara goge mata hawayen, kafin ta ce“ki daina kuka dan ba shi ne mafita ba a yanzu ki faɗa min ya aka yi haka?”
Tana ƙoƙarin magana wayarta ta shiga ringing dan haka ta kalli wajen a tsorace sai kuma ta tashi da sauri ta ƙarasa inda ta yar da wayar ɗazu ta ɗauka, Sunan Junaid ne akan screen ɗin dan haka ta ɗaga wayar da sauri bakinta na rawa ta ce
“Sir...sir dan Allah... Allah dan girman Allah kada ka yimin haka kaji kada ka yi haka dan Allah”
Murmushi Junaid ya yi yana kallon titi ya ce
“Me nayi miki Nana? Kin ga saƙona ne?”
Fashewa ta yi da wani sabon kukan tana girgiza kanta ta ce
“Dan Allah kada ka bari wani ya ga hotunan nan, dan Allah kada ka tozarta min rayuwa, ka yi haƙuri dan Allah..”
Dariya sosai Junaid ya yi kafin lokaci ɗaya ya haɗe rai cikin kakkausar murya ya ce
“Ai daman babu wanda zai gani Nana, ya za'a yi na bari wani ya ga lalatattun hotunan ki? Ai ba zan bari ba daman, idan har kin bi abin da zan faɗa miki babu wanda zai ji kuma ya gani, amma idan har ki ka kasa yimin biyayya to ki sani ina da irinsu-irinsu copy biyar, zan sake su a duniya kowa ya gani, kin ga ba iya ke kaɗai ba shi kansa dangin da ki ke taƙama dashi saina lalata shi wallahi tallahi kin ji har na rantse Nana!”
Sakin wayar ta yi ta faɗi ƙasa, ita kuma ta silale a hankali ta yi zaman daɓaro akan tiles, Zahra ta dinga kallonta daga inda take zaune, ganin yanda take hawaye kamar an buɗe famfo ya sanya ta taso ta dawo kusa da ita ta riƙeta tana cewa“me ya ce miki Nana?”
Kasa cewa komai ta yi sai kawai ta tashi ta shige toilet da sauri, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta tashi itama ta kwashe pics din ta mayar dasu cikin envelope ɗin sannan ta fice daga ɗakin.
****
Siyama ta dinga kallonsa tana murmushi kafin a hankali ta ce“ai na ɗauka ba zaka zo ba” Safwan da ke tsaye jikin motarsa ya girgiza kansa yana murmushin shima ya ce“haba dai naƙi zuwa, ai na ɗauka har yamma zaku kai a gidan namu” langwaɓar da kai ta yi ta ce“eh ai da yamman muka so kai wa amma sai aka ɓata mana rai” da ɗan mamaki ya ce“wane ya ɓata muku ran kuma?” taɓe baki ta yi ta ce“wata yarinya ce, ta ɗan zagemu to gudun mu ya hatsaniya da ita ya sanya kuma tawo kawai” Gyara tsaiwarsa ya yi sannan ya ce“yarinya kuma? Wace yarinya?”
Shiru ta yi tana kallonsa can kuma ta ce“wai ko Nana naji suna ce mata, yauwa ita ce ma yarinyar da zaka aura ko?”
Kallonta ya dinga yi bai ce komai ba, ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“naga ka yi shiru” Girgiza kansa ya yi yana faɗaɗa fuskarsa ya ce“bakomai, ita Nanan ce ta zageku?” gyaɗa masa kai ta yi ya ce“okay I'll talk to her, ki yi haƙuri kin ji” jinjina kanta ta yi ta ce”bakomai Yaya ai na haƙura tun da dai ƙanwar ka ce” Safwan ya ɗan yi dariya ya ce“to ya garin?” kamar jira take ta fara masa hira babu kama ƙafar yaro, y dinga murmushi yana saurarenta wani ya tanka ta wani kuma ya yi shiru.
****
Bayan sallahr magriba Zahra ta buɗe ɗakin ta shigo hannunta riƙe da tray, Nana na zaune ƙasan gado ta ɗora kanta gefen gadon sai hawaye take, karasowa ta yi ta ajiye tray ɗin gefe ɗaya sannan ta kalleta a sanyaye ta ce“Nana” shiru ta yi mata, dan haka ta sake kiran sunanta, nan ma bata amsa ba, Zahra ta dinga kallonta sai kuma ta kai hannunta ta taɓata ta ce“Nanaa!”
A ɗan firgice ta ɗago kanta, sai kuma ta goge hawayenta ta ce“Na'am Aunty”
“ki tashi ki ci abinci kin ji”
Girgiza kanta ta yi hawaye na zubowa kan kuncinta ta ce“naƙoshi aunty” Zahra ta dinga kallonta cike da tausayawa sai kuma ta ce“a'a Nana baki ƙoshi ba, zo ki ci abinci” sake girgiza kanta ta yi ta ce“wallahi bana jin yunwa, ba zan iya cin abinci ba Aunty” shiru Zahra ta yi can kuma ta numfasa ta ce“Nana faɗa min garin ya ya haka ya kasance tsakaninki da shi? A ina ya ganki har ya miki waɗannan ƙazaman hotunan?” madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta tana faɗin