Sashe 60
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“me ka ce? Ka cire Nana daga cikin dangin nan? Kenan ka zareta daga matsayinta na yar ka?”
Juyowa Abba ya yi yana kallonta sai kuma ya janye jikinsa ya ce“Eh haka nace!”
Daga haka ya koma ɗakinsa rai ɓace..
Silalewa ƙasa Amma ta yi ta fashe da wani raunataccen kuka, Aunty Ramlah ta riƙeta ba tare da ta ce komai ba. Numfasawa kawai Papa ya yi sai kuma ya fice daga parlon, Shi kuwa Abdusammad ciki ya shiga gurin Abba.
****
Ƙarfe 11:30 na safe Mami ta shigo ɗakin, suna zaune tare sai dai babu wacce ke magana cikin su. Mami ta girgiza kanta sai kuma ta ƙaraso ciki ta zauna kan sofa tana kallonsu duka ta ce
“Kukan ne har yanzu baku gama ba?”
Kallonta kawai suka yi ba tare da sun ce komai ba, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta ce“Nana kin ci abincin?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi a hankali dan har ga Allah ba son yin magana take ba. Mami ta sake cewa“to ku tashi ku shirya sai ku rakani”
“Ina zamu je Mami?”
Khadijah ta yi tambayar a sanyaye. Tashi Mami ta yi tana gyara zaman rigarta ta ce“idan mun je zaku gani” daga haka ta fice daga ɗakin. Khadijah ta bita da kallo sai kuma ta sauke numfashi tana kwanciya kan gadon ta ce“ni wallahi bana son fita” kallonta kawai Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Can kuma ta tashi zaune ta ce
“Yauwa Nana to yanzu sir Junaid ɗin ya fitar da hotunan?”
A sanyaye Nana ta ce“ban sani ba Khadijah,ina ga ya fadawa su Abba. Na san Abba yana can yana jin haushina” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Dafata Khadijah ta yi a sanyaye ta ce“ki daina kukan nan mana, kin ga dai jiya daga haka aka kai ki asibiti”
Cikin shessheƙar kuka Nana ta ce“to me zan yi? Ni gaba ɗaya bana jin daɗin rayuwar, wallahi da zan iya da sai nasha guba na mutu” saurin rufe mata baki Khadijah ta yi tana zare idanu, Nana ta janye hannunta daga kan bakinta rai ɓace ta ce
“Ni rabu dani”
Sake rufe bakin ta yi sannan ta ce“wallahi idan abin da zaki ce kenan ba za ki yi magana ba”
A fusace Nana ta hankaɗeta sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Khadijah ta tashi zaune tana riƙe bayanta ta ce
“Banza mai son faɗa kawai”
****
Aunty Khadijah ce zaune kan sofa sai Sojan a gefenta, daga ɗaya kujerar kuma Safeena ce zaune sai Ummarsu. Kamar daga sama Zahra ta shigo parlon babu ko sallama, ta ƙarasa wajen Umma ta faɗa jikinta tana fashewa da kuka.
Umma ta riƙeta da mamaki ta ce
“Zahra'u lafiya? Mene ne?”
“Ba zan iya ba Umma, ba zan jure ba wallahi. Ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba, Umma na shiga uku..”
Ta sake fashewa da kukan, Girgiza kai Umma ta yi cikin son kwantar mata da hankali ta ce
“Ya isa haka, tashi ki ji”
A sanyaye ta tashi ta zauna gefenta tana ci gaba da kukan, Umma ta dafata ta ce
“Duk abin da haƙuri bai baka ba to rashinsa ba zai taɓa baka ba Zahra'u, Idan baki hakura ba to me zaki yi?”
Cikin kuka Zahra ta ce
“umma ta ya zan jure zama da Nana matsayin kishiya bayan da ina mata kallon yar karamar ƙanwata, taya zan fara sharing mijina da ita? Wallahi ba zan iya ba!”.
Murmushi irin na manya Umma ta yi kafin ta ce“daman haka abun yake Zahra, sau dayawa abin da baka yi tunani ba shi ne yake kasancewa. Wani abun ƙaddara ce, wani kuma ganganci ne” Zahra ta tsaida kukan nata tana kallon Umma. Numfasawa Umma ta yi sannan ta ci gaba da faɗin
“Na san duk abin da ku ka aikata. Sai dai ban yi tunanin haka daga gareki ba, kin biye mata kun yi abin da ku ke ganin shi ne son zuciyarku, idan kuwa haka ne to dole ki yarda da abin da ya biyo baya.” Umma ta ƙare maganar tana kallonta, Sunkuyar da kai Zahra ta yi dan sam bata yi tunanin Umma ta san abin da ya faru ba, Umma ta girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta ta ce
“Ban ji daɗi ba! Sam bai min daɗi ba ganin yanda ki ka lalata rayuwar yarinya, kin san me yarda ke nufi? Ya yarda da ke, ta aminta da ke, tana miki kallon ƴar uwa wadda zata iya fadawa kowace damuwarta. Amma kin yi amfani da wannan yardar kin cutar da ita, kin yi mata abin da zai jawo kowa ya tsaneta, bayan ke da kan ki kin san cewa bada gangan ta yi hakan ba. To me ki ke tunani Zahra? Allah ya barki, ki ci bulus?”
Umma ta girgiza kanta sai kuma ta ce
“Inaaa ba zai taɓa yiwuwa ba, shi daman a kullum sharri ɗan aike ne, duk abin da ka ƙulla zai dawo maka, Ubangiji na kishin bawansa, kuma yana ƙaunarsa. Dan haka ya yi mata sakayya,ya nufi mijinki da aurenta.”
Fashewa da kuka Zahra ta yi tana danasanin abin da ta aikata, ita kanta ta san bata kyauta ba, sannan bata san dalilin daya sanyata yin hakan ba. Ta ɗago kanta tana kallon mahaifiyar tata wadda ke hawaye itama. Umma ta goge fuskarta da hannunta wanda ke riƙe da cazbaha sannan ta ce
“Na yi ƙoƙarin baku tarbiyya tun bayan rasuwar mahaifinku, na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin kun zama ya'ya nagari, kun zama mutane nagari wanda kowa zai yi alfahari dasu. Sai dai a duk lokacin daya kasance babbar ƴata bata kasance mutuniyar kirki ba, dole sai sauran sun zama haka. Dole sai taja wasu daga cikin ƴan uwanta. Kamar yanda Khadijah ta jaku ku ke ƙoƙarin faɗawa halaka”
Umma ta ƙare maganar wani kukan na kwace mata, Safeena ce ta riƙeta tana kukan ita ma ta ce
“Dan Allah Umma ki yi haƙuri. Ki daina kuka kin ji”
Riƙe hannunta kawai Umma ta yi dan bata jin zata iya daina kukan a halin da take ciki, Zahra ta girgiza kanta tana kuka ita ma ta ce
“ki yi haƙuri Umma. Wallahi ba zamu sake ba, babu abin da zai sake faruwa in sha Allah”
Tashi Aunty Khadijah ta yi ta bar wajen dan sam bata ga abin kuka anan ba, Siyama ta ƙaraso wajen ta zauna a ƙasa tana kallon Umma ta ce
“Umma ki yi haƙuri dan Allah”
Ganin duk sun ruɗe suna kuka ya sanyata tsagaita nata kukan. Ta dafasu tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce
“shikenan ya shige, Allah ya yi muku albarka ya shirya ku"
Da Amin suka amsa suna goge hawayensu..
****
Bayan sallar magriba ta dawo gidan, gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, musamman yanda taga Umma na kuka akan su. Sai taji danasanin abubuwan data aikata. Koda ta shiga gidan bata samu kowa ba kamar yanda ta yi tsammani, dan haka ta shige daƙinta ta yi wanka ta zauna gefen gado tana tunani. Tana nan zaune har aka yi sallar isha'i ta gabatar da sallah sannan ta sakko ƙasa ta shiga kitchen. Jollof rice ta yi wadda taji kayan haɗi, ta yi haɗin salad sannan ta fito ta koma sama ta zauna dan ko kaɗan bata jin yunwa.
****
Ƙarfe 9:30 na dare ya shigo ɗakin, zaune ya hangeta gefen gado ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali. Ya ƙaraso ciki yana kallonta, zama ya yi gefenta kafin ya ce
“Maimoon”
A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta mai da ƙasa tana shessheƙar kuka, Aliyu ya ɗan yi murmushi kafin ya kama hannunta na dama yana kallon red henna ɗin da aka zana mata wanda ya yi matuƙar kyau a hannunta, Ya kai hannun bakinsa ya sumbace shi yana lumshe idanu. Yana yin daya haifar mata da wani irin sanyin jiki, ta ɗago ta kalleshi a sanyaye. Ba tare da ya saki hannun ba ya janye mayafin da ta yi lulluɓi dashi, sannan ya ce
“tashi mu yi sallah”
Babu musu ta mike ta nufi toilet ta sake dauko alwala, bayan ta fito shi ma ya shiga ya yo alwalar sannan ya shimfiɗa musu ladduma. A tare ya ja su sallar nafilar bayan sun idar suka yi addu'a, daga bisani ya dafa kanta ya yi mata addu'o'i sannan ya tashi ya zare babbar rigar jikinsa yana kallonta ya ce
“Mu je ki ci abinci”
Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce“na ƙoshi”
Ya ɗan yi murmushi sai kuma ya kamo hannunta ya taimaka mata ta miƙe tsaye kafin ya ce“to muje ki ci kazarki” ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. Sosai Maimoon ta saki jikinta ta ci kazar bayan ta ƙoshi ta tashi ta bar wajen, Aliyu ya bita da idanu yana murmushi sannan ya biyo bayanta. Daren ranar haka suka raya shi cike da so da ƙauna, sam ba zaka ce ba auren soyayya suka yi ba, ya dinga riritata kamar kwai, ita kuwa sai sake narke masa take. A ɓangaren Sultan kuwa kasa taɓuka komai ya yi, ya dinga kallon Amrah da ke baccinta hankali kwance, gani yake kamar a mafarki. Zuciyarsa ta kasa aminta da cewa ya rasa Nana, idan ya kalli Amrah sai yaji damuwa ta sake masa yawa, ya so a ce Nana ce a wannan dakin, a kuma kwance akan wannan gadon, da shi kansa bai san halin da zai shiga ba. Ya ja idanunsa ya lumshe yana jin babu daɗi.
Washegari da sassafe around 7:30am aka fara buga ƙofar gidan, Aliyu ya janye jikinsa dakyar ya fita daga ɗakin bayan ya sake rufe Maimoon, yana buɗe kofar ya shigo yana kalle-kalle. Aliyu ya dinga kallonsa da mamaki sai kuma ya ce“Buddy lafiya?”
“Ina Maimuna?”
Da mamaki Aliyu ya ce“tana ciki”
“i want to see her”
Ya ce yana nufar dakin. Bin bayansa Aliyu ya yi da sauri, tsaye ya same shi gaban gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji. Aliyu ya ƙaraso ciki yana kallon Maimoon ya ce