← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 125

Sashe 122

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata san sanda ta tashi tsaye ba a mugun firgice, Ta fara girgiza kanta da hannayenta ganin yana murmushi har sannan. Ja da baya ta fara yi hankali tashe ta ce

“Wallahi wallahi uncle ban sha ba, Na rantse ban sha ba, Sai da nace bana so. Wallahi ba zan ƙara ba!”

Bai ce komai ba ya mai da maganin aljihun sa ya juya ya fice daga ɗakin. Nana ta yi zaman daɓaro a gefen gadon tana jin wani irin tashin hankali. Yaushe ya gani? Me yasa bai yi mata duka ba? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru wajen azahar. Ta tashi ta shige toilet ta wanke fuskarta sannan ta ɗauro alwala, Bayan ta fito ta gabatar da sallah sannan ta zauna a wajen, Har dare bata samu sukuni ba. Shirun da ya yi mata ta matuƙar ɗaga mata hankali, Haka ta koma balcony ta tsaya tana jiran dawowar sa, Bai dawo gidan ba har wajen ƙarfe 12:00 ta gaji da jiransa ta kwanta a wajen. Ba ita ta farka ba sai washegari wajen ƙarfe 9:00 na safe. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, Sallah ta yi sannan ta fice daga ɗakin ta nufi nasa, amma koda ta murɗa sai taji a rufe take. Ta kasa knocking haka kuma ta kasa barin wajen, Tana nan tsaye har bayan mintuna biyar taga wata maid ta hauro saman, Ta kalleta ta ce

“Excuse me pls.”

Tsayawa matar ta yi cike da girmamawa ta gaisheta, Nana ta amsa a sanyaye sannan ta ce

“Ina doctor yake?”

“He already gone”

Ta amsa cike da girmamawa. Shiru Nana ta yi can kuma ta ce“Alright thank you”

Ta ɗan sirina sannan ta ci gaba da tafiyarta, Jiki a saluɓe Nana ta koma daƙinta ta zauna. Yinin ranar ma haka ta yi shi a dame, Ko abinci kasa ci ta yi duk da yunwar da take cikinta, Sai wajen isha'i ta tashi ta sake wanka sannan ta yi sallah ta koma ta zauna. Ranar ma bai shigo gidan ba har bacci ya ɗauketa, Da asuba kuwa ta farka, Ta tashi tsam ta fice daga ɗakin gudun kada ya fita bata gan shi ba, Koda ta shiga ɗakin nasa samu ta yi ya tafi masallaci dan haka ta nufi banɗaki ta yo alwala ita ma, A ɗakin ta yi sallah dan akwai kayanta a ciki. Tana nan zaune har gari ya fara haske amma bai shigo ba, Dan haka kawai ta tashi ta fito waje ta tsaya. Ganin bashi da alamar shigowa ya sanya ta koma daƙinta zuciyarta kamar zata fito. Sai da suka jera kwana biyar suna wasan ɓuya dashi, Duk irin yanda take son ganin sa bata samun dama, Sai dai ta zauna ta yi ta kuka. Amani ta kirata yafi sau goma amma bata ɗauka ba, Daga ƙarshe ma blocking numbernta ta y, Ranar juma'a tana zaune ta zuba uban tagumi wayarta ta fara ringing, Kamr ba zata dauka ba sai kuma ta janyo wayar tana kallon mai kiran. Surry ce dan haka ta ɗaga ta kai kunne, Cikin faɗa ta fara cewa

“Nana baki da hankali ko? Baki san abin da ki ke ba ko? Akan me zaki biye wa su Amani? Bayan kina da tabbacin basu da ilimin addini. Kin san laifin wanda ya zubar da ciki kuwa? Ya za'a yi ki zubar da ciki ma? Kina hauka ne Nana? Kenan duk wanda ya baki shawara sai ki ɗauka, ba zaki tsaya ki tantance mai kyau da mara kyau ba. Nana kina son ubangiji ya dube ki kuwa?”

Allah sarki Nana, Tun da ta fara magana ta ke kuka, Ta san su Amanin ne suka faɗa mata abin da tayi. Surry taja dogon tsaki ta ce

“Ki bar wannan kukan da ba zai amfane ki ba, Yanzu ki faɗa min kin yi amfani da maganin? Kin zubar da cikin?”

Girgiza kai ta yi cikin kuka ta ce

“A''a”

Surry ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce

“To kada ki kuskura ki zubar, Ke kada ma ki sake sauraren abin da zasu ce miki”

“Tom. Ai ma Uncle ya ɗauke, kuma ya daina kulani, ko ganin sa bana yi a gidan nan”.

Cikin faɗa Surry ta ce

“To akan me ba zai daina kula ki ba Nana? Akan me? Ke ko tausayin sa bakya yi. Kina gani ƴar sa ce ta mutu ba'a jima ba, Yanzu akwai abin da yake buƙata sama da Ya'ya ne? Shi ne zaki zubar da ciki. Dole koma wane ya daina kula ki, wallahi ya yi miki da kauna ma, Da bai miki shegen duka ba, Ki nutsu ki kama kan ki wallahi, Idan ba haka ba ki gurguɗe auren ki.”

Cikin kuka Nana ta ce

“In sha Allah ba zan sake ba, Kuma ai inason na bashi haƙuri ne, amma bana ganinsa, kullum sai nayi bacci yake dawowa. Kuma da safe kafin na tashi yake fita, Yaƙi bari na ganshi”

Rage murya Surry ta yi yanda zata fahimceta ta ce

“Kina ji ki nutsu, Yau kada ki yi bacci, Ki san yanda zaki hana kan ki bacci har ya dawo.”

“To ai idan ya dawo ya ganni ba zai kulani ba, Ɗakinsa zai shiga ya rufe”

Shiru Surry ta yi tana tunani, Can kuma ta ce

“To yanzu ke je ɗakin nasa ki zauna, Kada ki yi bacci har ya dawo, Idan ya shigo sai ki san yanda zaki bashi haƙuri.”

Jiki a sanyaye Nana ta amsa sannan ta kashe wayar.

Da daddare tana ganin 9:00 ta yi ta tashi ta yi wanka, Ta shirya cikin kayan baccinta riga doguwa wadda ta tsaya iya gwuiwarta, Fararen ƙafafunta sun bayyana. Ta gyare gashinta sai Sheƙi yake, Hijabi ta ɗauka ta saka sannan ta fice daga ɗakin, Nasa ɗakin ta shiga ta zauna kan kujera ta yi shiru. Tun tana saka ran dawowarsa har sai da ta yi giving up, Ban da gyangyaɗi babu abin da take yi. Tashi ta yi ta buɗe balcony ta shiga, Ta dinga kallon ƙasan gidan gwanin ban sha'awa. Tana nan tsaye har after 25mins ta hango shigowarsa a mota, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin daɗi, Duk da bata san ta inda zata fara bashi haƙurin ba. Sake rufe balcony ɗin ta yi ta yi shiru tana jiransa, Tana ji ya shigo ya ajiye wayarsa da car key a gefen gado sannan ya nufi toilet. Ya jima kafin ya fito sanye da bathrobe, Ya buɗe press ɗin sa ya dauki boxer ya saka sannan ya tsaya yana shafa mai. Sai da ta yi addu'a kafin ta buɗe balcony ɗin ta fito, Sam bai ji sanda take zuwa ba sai kawai ji ya yi an rungume shi ta baya, Ta riƙe shi da iya ƙarfinta sai kuka take. Yi ya yi kamar bai san tana gun ba, Ya ci gaba da shafa man sa. Cikin kuka ta ce

“Dan Allah uncle ka yi haƙuri, Ba zan sake ba. Wallahi ba zan sake ba, Na daina, Na tuba uncle, Ba zan kuma yi maka ba. Ba zan sake ba wallahi, Na yi kuskure kuma ba zan ƙara ba, Ka yafe min dan Allah. Kada Mala'iku su dinga fushi dani...”

Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Ba zaka taɓa cewa da Abdusammad take ba, Dan ko kezau bai yi ba, ballantana ta saka ran zai ce wani abu. Sai da ya gama abin da yake gaban mirror ɗin sannan ya janyeta daga jikinsa ya karasa gaban gadon, Hawa ya yi ya zauna ya janyo laptop ɗin sa ya kunna ya fara operating ɗinta, Nana ta yi kamar statue a wajen tana kallon sa tana kuka. Can kuma ta ƙaraso ta tsuguna gaban gadon cikin kuka take faɗin

“Dan Allah uncle ka yafe min, Ba zan sake cewa zan zubar ba. Wallahi ban zubar ɗin ba, Ba zan ƙara ba. Ƙawayena ne suka ce wai baka sona saboda cikin, Idan na zubar zaka dawo yanda ka ke yi min da. Shiyasa na yarda, wallahi ba da wani abun ba, Dan Allah ka yi haƙuri, Kada ka faɗawa Abbana da Ammata. Dan Allah uncle...”

Tashi ta ga ya yi ya fice daga ɗakin, Tabi bayansa da kallo sai kuma ta kifa kanta jikin gadon tana ci gaba da kuka, After some minutes ya dawo hannunsa riƙe da mug, Ya koma ya zauna ya ci gaba da abin da yake yana sipping coffee ɗin a hankali. Bata fasa bashi haƙuri da magiya ba, Haka shima ko da wasa bai kalli inda take ba. A haka har ya kammala abin da yake a system ɗin ya rufeta ya ajiye gefe, Tashi ya yi ya fice daga ɗakin bai jima ba ya dawo ya shiga toilet, wanke bakinsa ya yi ya dawo ya haura saman gadon yana shirin kwanciya. Wata irin zabura Nana ta yi ta riƙe ƙafafunsa tana wani irin kuka kamar wadda aljanu suka shafa, Tama masa maganar sai kukan kawai take tana buga kanta akan ƙafafunsa. Ganin tana neman zare masa ya sanya shi janye ƙafafunsa, Ya ƙura mata idanu yana kallon ta can kuma ya tashi zaune muryarsa a dake ya ce

“Ɗagani”

Ai kamar ya turata haka ta ci gaba da da kukan tana ƙanƙameshi. Ya girgiza kansa sai kuma ya ce

“Me zan yi miki? Ki bar ni na huta mana, Ki yi abin da ki ke so. Ki dau duk hukuncin da ki ka ga ya dace miki, amma ki daina damuna. Ki bar ni dan Allah!”

Ya ƙare maganar a nutse, Ai kamar jira take ta shige girgiza kanta cikin kuka ta fara cewa

“Wallahi A'a uncle ba zan kuma ba, Na nutsu, Ba zan ƙara yi maka rashin kunya ba. Ba zan sake yin rashin jin magana ba, Zan zauna lafiya dan Allah ka yi haƙuri”

Taɓe baki ya yi still looking at her ya ce
Chapter 122 · 0% Book details