← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 125

Sashe 77

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta rushe da wani sabon kukan tana jan numfashi. Murmushi ne ya tawo masa, Ya ɗan ci mur yana takawa gabanta, gaba ɗaya ya gama gano inda ta dosa, Dan haka ya ɗago fuskarta yana kare mata kallo ganin yanda ta shagwaɓe ya ce

“Kenan ba zan je wajenta da kayan jikina ba? Ita ma kuma haka? To ai matata ce. Ko ke ɗin nan zaki iya zama a haka idan ina nan, ko baki sani ba?”

Ɗago idanunta ta yi da sauri ta kalleshi, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza kanta kafin ta ce“a'a ni a'a wallahi, ba zan iya ba. Ni bana so”

“Ko?”

Ya ce yana kafeta da idanu. Tura baki ta yi gaba tana dauke kanta daga gare shi ta ce“ni Allah bana son iskanci.”

Jinjina kansa ya yi sai kuma ya ɗan yi baya ya ce“Dan kin zauna a gurina da karamar riga shi ne iskancin?” Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta gyaɗa masa kai. Ya jinjina kansa sannan ya juya kamar zai fita, Key ya sakawa ƙofar ya rufe ruf sannan ya juyo yana kallonta ya ce

“To yanzu nake son ki yi iskancin!”

Daga haka ya nufota yana ƙoƙarin cire agogon dake maƙale a hannunsa.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 47.

Ja da baya Nana ta fara yi tana zazzaro idanu. Sai da ta kai ƙarshen bango ta maƙale tana kallon sa kamar zata yi kuka, Abdusammad ya yi wurgi da agogon kan gado ya matso dab da ita har suna jin hucin numfashin juna. Ta sunkuyar da kanta ƙasa bakinta na rawa ta ce“Nin...Ni dai uncle bana so wallahi, Dan Allah ka matsa.”

Shiru ya yi mata har sannan sai kallonta yake. Ya sanya hannunsa na dama ya ɗago fuskarta, Ya sauke wani zazzafan numfashi yana ƙarema kyakkyawar fuskarta kallo, Ita kuwa sai sake turo baki take tana ƙunƙuni. Ɗayan hannunsa ya kai ya shafi lips ɗinta, Ta yi saurin rufe idanunta lokaci ɗaya jikinta ya fara wani irin rawa kamar mazari. A hankali ya dinga shafar lips ɗin nata masu taushi, kafin daga bisani ya goge gaba ɗaya lip gloss ɗin data saka. Bata yi aune ba taki taji ya kai mata rankwashi aka, Ta dafe kanta da hannunta kamar zata yi kuka ta ce

“wayyo zafi fa uncle.”

Taɓe baki ya yi yana watsa mata wani kallo ya ce“kar na sake ganin kin shafa wannan abun kin ji abin da nace.?” Gyaɗa masa kai ta yi tana marairaice fuska. Ya ɗauke hannunsa daga kan fuskarta sannan ya ce“da ki ka je ɗakin nawa me zaki ce min?” Ya yi maganar yana ƙarasawa kan Italian bed ɗin nata, Ya zauna. Da sauri tabi bayansa ta zauna gefensa ta ɗora duka hannayenta biyu akan cinyarsa sannan ta ce“To ba yunwa nake ji ba uncle. Kamar zan mutu fa” Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba can kuma ya ce“To me ya hanaki cin abincin?”

“Uncle ai ban iya girki ba.”

Ta yi maganar a shagwaɓe, Jinjina kansa ya yi babu yabo babu fallasa ya ce“ai daman baki yi kama da wadda ta iya girkin ba.” Tura baki ta yi kafin ta ce“To bayan boarding school nayi, dan Allah a ina zan iya girkin?” sai da ya gama maƙale agogonsa ya mike sannan ya ce“haka ne.” ganin yana shirin fita yasa ta ce“uncle cewa nayi fa yunwa nake ji.”

“To Nana cinyeni”

Ya yi maganar yana kallon ta, Murmushi ta yi ta ce“to ai bana cin mutun, ni muje ka siya min abincin dan Allah.” harararta ya yi ya ce“ki je apartment ɗin Hajiya Babba a baki.”

“To Atta ce zata yimin faɗa fa.”

Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Bai sake bi ta kanta ba ya fice daga ɗakin. Nana ta yi shiru tana kallon sa, kafin daga bisani ta koma ta kwanta akan gadon tana hawaye, dan har ga Allah yunwa take ji bata wasa ba.

Ba'a fi 10mins ba aka sake buɗe ɗakin, Bata ɗago kanta ba sai kukanta da take a hankali, ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce

“taso mu tafi”

Jikinta har rawa yake ta tashi daga kwancen ta sauka daga kan gadon ta nufosa. Wani mugun kallo da taga ya watsa mata ya sanyata tsayawa, Ya kalleta frm head to toe sannan ya ce

“Kin koma kin rufe jikin ki ko sai na makeki anan?”

Jiki a sanyaye ta koma ciki, ta buɗe press ɗinta ta zaro wani hijabi har ƙasa baby pink ta saka. Ya yi kamar riga dan mai babban hannu ne, Yana kallon ta har ta gama sakawa sannan ta ɗauki wayarta dake gaban mirror. Ya ɗauke idanun sa daga kanta ya juya ya fice daga ɗakin, ta tura baki gaba sannan tabi bayansa. Babu kowa a parlourn ya yi waje abin sa tana biye dashi. Cikin wata Lexus jeep ya shiga, Nan da nan guards ɗin dake wajen suka taso, ya girgiza musu kai alamar shi kadai yake son fitar. Har ya gama warming motar tana tsaye tana bin sa da kallo, Ya ɗan kalli side ɗin da take fuska a haɗe ya ce“sai na bi ta kan ki ne?” sai a sannan ta sauke idanunta ta buɗe motar ta shiga passenger seat ɗin, Ya taɓe baki sannan ya juya ya bar wajen.

Sun yi nisa ta kalleshi kamar wadda aka tsikara ta ce“uncle ina zamu je?”

“siyar dake zan yi.” Ya ce ba tare da ya kalleta ba, Tuntsirewa ta yi da dariya, Ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana murmushin shima. Har suka ƙarasa gaban gidan babu wanda ya sake cewa wani abu, Ya yi horn aka buɗe gate ɗin sannan ya tura hancin motar cikin babban compound ɗin gidan. Yana gama parking ya sauke ba tare da ya kalleta ba, Itama ta buɗe side dinta ta sakko tana ƙarewa gidan kallo, Babbar gida ne wanda aka yishi cikin tsari na turawa, Daga gani ka san guest house ne, Zagayowa ya yi side ɗinta ya riƙe hannunta suka yi gaba. Nana ta dinga bin sa tana mamakin dalilin zuwan su gidan.

A babban parlourn gidan suka tsaya, parlourn an ƙawata shi da kujeru na zamani masu kyau da kuma tsada, Ko ina tsaf dashi sai ƙamshi mai daɗi dake tashi wanda ya gauraye da sanyin ac ya bada wani yanayi mai daɗi. Nana ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta jingina kanta da kujerar tana lumshe idanu, Kallon ta kawai ya yi sai kuma ya buɗe wata ƙofa ya shige, Ta ɗauki a ƙalla 15mins a wajen kafin aka buɗe wata ƙofa, tabi wadda ta shigo da kallo, wata maid ce hannunta riƙe da ƙaton tray, ta ajiye a gaban Nana sannan ta koma ciki. Nana ta dinga kallon tray ɗin wanda aka cika shi da kayan shayi, tana nan zaune maid ɗin ta ƙara dawowa hannunta riƙe da warmers guda biyu. Ta sake ajiyewa gaban Nana tana murmushi ta ce

“Can i serve you ma?”.

Girgiza mata kai Nana ta yi, Ta sunkuya sannan ta juya ya bar parlour. Sai a sannan Nana ta zamo ƙasa a hankali tana sauke numfashi, Ta ɗauki tea flask ɗin sannan ta janyo wani mug ta tsiyaya shayin, bayan ta zuba wanda take ganin zai isheta ta mayar ta rufe sannan ta saka madara da kuma bounvita da yake wajen, ta saka sugar kaɗan dan bata son zaƙi. Juyawa ta yi sannan ta ajiye, Ta buɗe warmer taga soyayyen dankalin turawa a ciki sai kuma wainar kwai masu kauri, murmushi ta yi sannan ta ɗauki plate ta zuba dankalin sannan ta saka wainar guda biyu, ta tankwashe ƙafafunta sannan ta fara shan tea ɗin. Da fari sai da ta kusan amai sakamakon dadewar da ta yi bata ci abincin ba, Ta ajiye mug ɗin tana sauke numfashi a hankali. Can kuma ta fara cin dankalin tana haɗawa da kwan, idan ta ci sai ta sha tea ɗin a haka har ta cinye na gabanta tas. Ta yi gyatsa dan ta ƙoshi, amma ta gyara zamanta sannan ta buɗe ɗayar warmers, farfesun catfish ne sai tiriri yake, Ta washe baki tana dariya sannan ta saka yatsanta ta dangwali romon, lumshe idanu ta yi a fili ta ce

“woww!”

Ta ajiye murfin a gefe sannan ta janyo wani sabon plate ɗin da spoon, yanda zai isheta ta saka sannan ta zuba uban romo akai. Ta tura warmer gefe sannan ta fara ci a hankali, Sam bata lura da sanda ya shigo parlourn ba, har ya zo kusa da ita ya zauna a kujera. Ya yi Shiru yana kallon yanda take ta cin kifin tana tsince ƙaya tana tarawa a gefe. Sai da ta cinye shi shima tas sannan ta ɗago kanta tana shirin ɗaukan ruwa suka haɗa ido dashi, Ta yi saurin ɗauke nata tana tura baki. Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“har kin ƙoshi?” sai da ta ɓalle murfin robar ta sha ruwan kusan rabi sannan ta ajiye tana kallon sa ta ce“na ƙoshi sosai uncle.” jinjina kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Ta tashi ta kwashe kayan ta nufi hanyar da taga maid ɗin tayi, dan ita a rayuwarta bata son taga an bar waje da datti. Bayan ta kai kayan na farko ta dawo parlourn da niyyar ɗaukan sauran, sai dai abin da ta gani ya sanyata tsayawa cak, ta sake ware idanunta tana son tabbatar da abin da take gani. Da gudu kuma ta nufi inda Abdusammad yake ta faɗa jikinsa ta ƙanƙameshi tana wani irin kuka, Abdusammad ya riƙeta gam yana shafa kanta a hankali. Junaid dake zaune kan kujera ya dinga kallon ta idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, Sun ɗauki mintina a haka kafin ya ɗago fuskarta yana share mata hawayen ya ce

“mene ne to?”

Sake rungume shi tayi tana kuka ta ce“uncle dan Allah, dan Allah uncle, bana so. Wallahi ba zan ƙara ba, kace ya tafi, ka ce ya yi tafiyarsa dan Allah uncle...” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana jin yanda hawayenta ke zuba a jikinsa. Ya ɗago kansa ya kalli Junaid babu yabo babu fallasa ya ce

“I think kaje kawai. Komai ya shige”
Chapter 77 · 0% Book details