← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 125

Sashe 110

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Kiraye-Kirayen sallar magribar da aka fara shi ne ya sanya shi tashi zaune, Tun bayan daya dawo daga gidan su Zahra bai sake fita ba, anan ɗaki ya yi sallolin sa. Ya ɗan yi jim sai kuma ya tashi ya zura slippers ɗin dake gaban gadon ya nufi bandaƙi, Wanka ya yi sannan ya ɗauro alwala. Yana fitowa ya buɗe press ɗinsa ya dauƙi wata embroidery jallabiya nude colour ya saka, sannan ya shafa mai da turare bai tsaya gyara kansa ba ya dauƙi ƙaramin counter dake gefen mirror ya fice daga ɗakin. Kai tsaye masallacin dake estate ɗin ya nufa,Bayan an idar da sallah suka fito tare dasu Papa.

Abba dake lura da yanayin sa tun sanda ya shigo ya kalle shi ya ce

“Abdul mene ne?”

Girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce

“Ba komai Abba.”

Ya bashi amsa yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa. Ɗan murmurshi irin na manya Abba ya yi kafin ya ce

“Alright, Ina son magana da kai”

Jinjina kansa ya yi ya ce“Nima dama Ina son zan yi magana amma a gidan Hajiya Babba.”

“Lafiya dai?”

Papa ya tanbaya yana kallon sa, Girgiza kansa ya yi ya ce

“A'a nothing serious, kawai dai ina son maganar ne.”

Jinjina kai Papa ya yi ya ce“Okay to a bari sai an idar sallahr isha'i”

To kawai ya ce sannan ya yi mus sallama ya nufi apartment din sa, Da idanu Abba ya bi shi dan ya lura akwai abin da ke damun sa. Suka yi sallama da Papa sannan ya nufi apartment din sa, Yana shiga ya tarar da Haule a parlour ita da Amma suna hira, Suka yi masa sannu da zuwa ya amsa. Ganin yana kallon su ya sanya Amma ta ce

“Lafiya dai yallaɓai?”

Girgiza kansa ya yi ya ce “Ba komai, Ina Nana ta ke?”

“Tana ɗakinta”

Ta bashi amsa tana kallon sa,

“Kira min ita.”

Ya yi maganar yana zama kan sofa, To kawai Amma ta ce sannan ta tashi ta nufi ɗakin Nanar, Haule na ƙoƙarin tashi ya girgiza kansa ya ce

“Yi zaman ki mana, yanzu zan tashi.”

Sunkuyar da kanta ta yi sannan ta ce to, Ba'a fi 2mins ba Amma ta dawo parlourn ta zauna tana cewa

“Gata nan”

Ko rufe baki bata yi ba Nana ta fito tana gyara zaman mayafin abayar dake kanta, Kujerar da yake ta ƙarasa ta zauna tana kallon sa ta ce

“Abba gani”

“Ki je wajen Abdusammad.”

Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta ce to sannan ta tashi tana shirin komawa ɗaki ya ce

“Ina zaki je?”

“Wayata zan dauƙo” ta ce tana nuna masa ɗakin,Okay kawai ya ce, Ta juya ta nufi ɗakin.. after some minutes ta dawo hannunta riƙe da wayar ta sauya riga, Ta yi musu sallama sannan ta fice daga parlourn. Sai a sannan ya tashi ya nufi ɗakin sa, Amma ta bi bayansa..

Jiki a sanyaye ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, Babu kowa a parlourn, komai a nutse. Ta nufi sama kai tsaye, ɗakinsa ta buɗe ta shiga. Zaune ta same shi kan sofa ya jingina da jikin kujerar idanunsa a lumshe kamar me tunani, Ya rame sosai, Kamar ba shi ba. Ya ɗan yi duhu, Ta sauke idanunta sannan ta ƙarasa ciki, Zama ta yi gefen sa a sanyaye ta ce

“Uncle.”

A hankali ya buɗe idanun sa, Ya ɗan kalleta da mamaki ya ce“Nana yaushe ki ka zo?”

Tana kallon sa ta ce“Yanzu, Na zo ban ga kowa ba. Kuma naga kamar tunani ka ke, Me ka ke tunani?”

Ta yi maganar tana leƙa fuskarsa, Girgiza mata kai ya yi ya ce“Ba komai Nana.”

Yanda ya kira sunan nata a sanyaye ya sake tabbatar mata da akwai abin da ke damun sa, Ta haɗe rai ta ce

“To ba zaka fada min ba? Na daina kula ka!” ta ƙare maganar tana tura baki, Bai ce komai ba ya mai da kansa jikin kujerar yana sauke numfashi, Kallon sa ta dinga yi, can kuma ta miƙe a fusace ta ce

“To na tafi tun da ba zaka fada min ba. Kuma nima ba zan sake faɗa maka abuna ba!”

Murmurshi kawai ya yi ya sanya hannunsa ya jawota ta faɗo jikinsa, Ƙoƙarin tashi ta fara ya sake matseta ya ce

“Sorry mana”

“Ni ka cikani, na daina kula ka!”

Ta yi maganar tana tura baki, Gyara zaman sa ya yi ya ɗago fuskarta yana kallon ta sosai ya ce“Shikenan zan faɗa”

Tsayawa ta yi da kokawar tana kallon sa ta ce“To faɗa min.”

Ɗan murmurshi ya yi sannan ya ce

“To rufe idanun ki”

Ɗan juya idanunta ta yi ta ce

“Ni kawai ka faɗa min wallahi.”

Girgiza kansa ya yi ya ce“Ai sai kin rufe”

Ta tura baki gaba sannan ta sanya hannunta ta rufe fuskarta gaba daya, Numfasawa ya yi, Bata yi aune ba taji ya rungumeta tsam a jikinsa, Ya ɗora kansa a gefen wuyanta, Ajiyar zuciya Nana ta sauke. Ta sanya hannayenta duk biyun ta riƙe shi ita ma, Bata yi aune ba sai jin zubar hawaye ta yi a bayanta, Ta ɗago dan ganin abin da ke faruwa amma ya sake riketa gam, Yanda ba zata iya ganinsa ba. Lokaci ɗaya kuma yana ci gaba da kukansa.

“Uncle.”

Ta ce a sanyaye, Bai bata amsa ba sai sake rufe fuskarsa da ya yi a jikinta. Shiru Nana ta yi tana sauraren sautin kukansa, Gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin sanyi,Tun da take bata taɓa jin kukansa ba. Bata taɓa gani ba, Duk yanda abu ya dameshi ba lallai ya zubar da hawaye ba. Koda zai zubar Hajiya Babba da Abba ne kawai suke iya ganin hawayensa, amma yau gashi yana kuka a gabanta. Sun ɗauki mintina a haka har sai da ya yi shiru dan kansa, Abdusammad ya janye fuskarsa daga jikinta yana ƙoƙarin goge ragowar hawayen da ke kan fuskarsa.

“Uncle..”

Ta kira sunansa a sanyaye, Ɗan tsuke fuskarsa ya yi hannunsa riƙe da ƙaramin hanky yana goge hawayensa. Shiru ta yi tana kallon sa har sai da ya gama, Sannan ya buɗe bakinta tana shirin yin magana taji ya ce

“Nana!”

Yanda ya kira sunanta in a serious tone ya sanyata nutsuwa, Ta kalleshi ta ce“Na'am uncle.”

“Kar naji maganar kuka a bakin wani, Understood?”

Shiru ta yi bata ce komai ba, Ya sanya hannunsa yaja hancinta sannan ya ce

“Ina wasa da ke?”

Girgiza masa kai ta yi, Ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shige toilet. Tana nan zaune har ya fito, Ta dinga kallon sa ganin yana shirin fita yasa ta ce

“Uncle ina zaka je kuma?”

Sai da ya ɗauki wayarsa saman kujerar sannan ya ce

“Sallah zan yi, Kema ki yi”

Tashi ta yi tana ƙoƙarin gyara mayafinta ta ce“To bari na tafi”

Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta, Fuskarsa a tsuke ya ce

“Idan ki ka bar nan sai na ɓata miki”

Turo baki ta yi ta koma ta zauna, Ya juya ya fice daga ɗakin.

****
Umma ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zahra na zaune gefen gado ta kifa kanta akan cinyoyinta sai kuka take a hankali. Umma ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tana kallon ta, Tun bayan da ta dawo ɗazu da safe bata yi shiru ba, Dakyar ta yiwa Ummar bayanin abin da ya faru da kuma dalilin sakin nata. Duk irin yanda Umma ta dinga bata haƙuri kin ji ta yi, Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, Dan kanta kuma ta gaji ta yi shiru da yamma, Bayan sallahr magriba kuma ta ci gaba da kukan. Umma ta sauke numfashi tana kallon ta ta ce

“Zahra'u”

“Na'am Umma”

Ta amsa cikin kuka, Shiru Umma ta yi zuciyarta a dagule, Ba ƙaramin tausayi ta bata ba, Gefe guda kuma ga takaicin biyewa Khadijah da tayi. Can dai ta ce

“Kenan ba ki san ƙaddara ba? Baki yi imani da ita ba? Ba zaki haƙurcewa zuciyar ki ba?”

Dakyar Zahra ta ɗago kanta tana kallon ta cikin kuka ta shiga girgiza kanta ta ce

“Wallahi Umma ina son Doctor, Ina son Abban Noor. Bana son rabuwa dashi, Zuciyata zafi take min Umma. Ji nake kamar zan mutu, Na kasa yarda ya sakeni, Na kasa Umma!”

Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Shiru Umma ta yi tana kallon ta, Can dai ta dafata cikin sanyin murya ta ce

“Na sani, Na sani Zahra'u, Amma ina so ki sani duk abin da ubangiji ya hukunta babu makawa sai ya faru. Allah ne ya hukunta zaki aure shi, Wannan shi ne dalilin daya sanya ku ka haɗu tun farko, Har ku ka haifi ƴa tare. Sannan sakin ki da ya yi shi ma Abu ne wanda ubangiji ya hukunta ba mutum ba, Shi aure rai ne dashi, Duk ranar daya ƙare to dole sai an rabu. Dan haka ki ɗauki sakin nan matsayin ƙaddara, Kada ki ce zaki damu kan ki dan Allah Zahra'u. Kada ki sakani cikin wata damuwar bayan wadda nake ciki, Ki taimaka”

Sosai Ummar ta bata tausayi, Dan ta san duk abin da faru ita ce sila, Sun kasa barinta ta samu nutsuwa, kullum cikin ɗawainiya take dasu tun bayan rasuwar mahaifin su. Ta gyaɗa mata kai duk da yanda take jin abu ne mai wahala ta manta dashi ɗin ta ce

“To Umma....”

Ta ƙare maganar cikin kuka, Numfasawa Umma ta yi ta ce

“Allah ya shige mana gaba, Ki daure ki ci abinci.”

“To Umma”

Shi ne kawai abin da ta iya furtawa, Umma ta tashi ta fice daga ɗakin a sanyaye. Zahra na ganin ta fita ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ta sani ba zata mance da Abdusammad nan kusa ba, Ba zata manta rayuwar su tare ba. Abu ne mai wahalar gaske ta iya cire shi daga ranta, Ta sake kan numfashi tana ci gaba da kukanta. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi, Ta ɗaga kanta tana kallon ta, Anty Khadijah ce ta shigo tana kallon ta, Zahra ta yi saurin tashi tsaye tana girgiza mata kai cikin kuka ta fara magana

08106608363
Nanameera.*Page 66.*
Chapter 110 · 0% Book details