← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 125

Sashe 79

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda ta faɗi sunan nasa in a romantic style ya sanya shi mai da idanunsa kan bakinta, A hankali kuma ya sake ɗora bakin nasa kan nata ya fara tsotsa kamar ya samu alawa, yayinda hannunsa ɗaya ke bayanta yana ɓalle bra ɗinta.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 48.

Wani irin jan numfashi ta dinga yi, idanunta a rufe sai hawaye ne ke zubowa ta gefensu, Ta kasa koda motsi gaba ɗaya jikinta ya yi sanyin. Shi kuwa kamar ana ƙarar wutar abin da yake yi, Ya gyara zamanta akan cinyarsa tasa bayan ya zare bakinsa, Yana ƙoƙarin kwantar da ita kan gadon aka fara knocking ƙofar. Dakyar ya iya buɗe idanunsa, Ya janye jikinsa ya miƙe tsaye, Sai a sannan Nana ta samu damar tashi zaune ta koma can ƙarshen gadon ta cure jikinta waje ɗaya. Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi ya tsaya a jiki yana kallon ta da lumsassun idanunsa. Zahra dake tsaye ta ɗan sunkuyar da kanta kafin ta ce

“Daman Aliyu ke nemanka.”

Gyaɗa mata kai ya yi kawai sannan ya mai da ƙofar ya rufe. Wata irin zabura Nana ta yi tana sake ja da baya, Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, Ya juya ya fice daga ɗakin. Ɗakinsa ya shige kai tsaye kuma toilet ya nufa, Wanka ya yi sannan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya maroon colour mai taushi, Ya gyara gashin kansa sai sheƙi yake. Turaren oud ya fesa mai daɗin ƙamshi. Gaba ɗaya a sanyaye yake komai, Ya dafa dressing mirror yana karewa kansa kallo, lokaci ɗaya scene ɗin ɗazun ya dawo masa. Wani dogon tsaki yaja, Sam bai san garin ya ya haka ta faru ba. Hannunsa ya kai kan lips ɗinsa ya shafa sannan ya ce

“Astagfirullah!”

Ya faɗa yana barin wajen, Wayarsa ya ɗauka gefen gado ganin missed calls ɗin Aliyun ya sanya shi yin waje.

Kallon ƙofar dakin nata ya yi sai kuma ya nufi upstairs da sauri, Zaune ya samu Zahra tana cin abinci ta kalleshi amma bata ce komai ba. Kamar zai wuce sai kuma ya tsaya idanunsa a lumshe har sannan ya ce

“Ina Noor?.”

“Juwaira tazo ta tafi da ita.”

Zahra ta bashi amsa jiki a sanyaye. Bai sake cewa komai ya juya ya fice daga parlourn.

Tsaye ya samu Aliyun a balcony ya harɗe hannayensa a ƙirji idanunsa maƙale da sun glasses. A hankali ya ƙarasa cikin takunsa na isa da taƙama, Aliyu ya zare glasses ɗinsa yana kallon sa, Shi kuwa ɗauke kansa ya yi yana kallon wani wajen daban. Aliyu ya yi murmushi ya ƙaraso gabansa ya ce

“Buddy na ganka haka?”

Haɗe rai ya yi sosai ya ce“mene? Me ka gani?”

Tuntsirewa da dariya Aliyu ya yi ganin yanda ya wani cure gira, Ya ce“Gani nayi ka yi fresh da kai kamar ango, ko dai?.”

Wani banzan kallo daya watsa masa ya sanya shi tsuke bakinsa. Abdusammad ya zabga masa harara sannan ya ce“idan kaga dama ka zauna anan.” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin yin gaba, Murmushi Aliyu ya yi ya biyo bayansa yana cewa“To mene abun fusata anan?” shi dai ko kallon sa bai yi ba ballantana ya saka ran zai amsa masa, deep down nasa kuwa baya son Aliyun ya gane abin da ya faru tsakaninsa da Nana ne. Back seat suka shiga, driving ya shiga gaba suka bar gidan tare da excort ɗinsa.

****
Tafi awa kwance a wajen, Ita kanta bata san abin da ke damunta ba. Ji take yi kamar ba ita ba, Idan ta tuna abin da uncle ɗin ya yi mata sai taji kuka ya sake tawo mata, Tana nan kwance har wajen ƙarfe 3:00 na rana, Wayarta ta fara ringing. Dakyar ta tashi zaune sai a sannan ta tuna da rigarta da take a rabe, Ta ɗan kalli ƙirjin nata sai kuma ta sake fashewa da kuka, Taya ma za'a ce uncle ya yi mata haka? Akan me zai ga jikinta, ringing ɗin da wayar ta sake ne ya sanyata tsagaita kukan, Ta jawo wayartata ta kai kunne. Khadijah dake cikin mota ta ce

“Na kusa fa.”

Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta, Khadijah ta sake cewa“Nana ko bakya jina?”

Jan numfashi ta yi kafin ta ce“Ina ji. Sai kin zo”

“Kuka kuma? Me aka yi miki?”

“Babu komai fa sai kin zo.”

Nana ta bata amsa a hankali, ok kawai Khadijah ta ce sannan ta kashe wayar ba dan ta yarda da abin da ta ce ɗin ba. Nana ta miƙe tsaye a sanyaye ta nufi toilet hannunta dafe da ƙirjinta. Wanka ta yi ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga ta material mai sulɓi, Ta ɗaure kanta da ɗankwalin yadin sannan ta saka hijabi ta gabatar da sallar azahar. Bayan ta idar ta jingina da jikin gadonta ta yi shiru tana tunane-tunane, hawaye ya ci gaba da zuba daga idanunta. Bayan mintuna sha biyar wayarta ta sake ringing ta ɗaga bata ce komai ba, Khadijah ta ce

“Na sauka fa, ina Apartment ɗin ku.”

“To bari na zo mu tafi tare”

Nana ta yi maganar a sanyaye. Kafin Khadijahn ta yi magana Amma dake jin su ta ce“kin tambayeshi ne da zaki fito?”

Wata irin faɗuwar gaba ce ta risketa, ta yi saurin girgiza kanta dan ba son maganarsa take ba ta ce“A'a. Khadijah ki ƙaraso”

Toh kawai Khadijahn ta ce sannan ta kashe wayar. Amma ta mike tana cewa“bari na baki saƙo ki tafar mata dashi.” to Khadijah ta ce tana gyara zamanta.

Bayan wasu mintina aka fara knocking ƙofar daƙinta, Nana ta kalli ƙofar da sauri hankalinta a ɗan tashe ta ce“wa...wane?”

“Ke ni ce.”

Khadijah ta bata amsa. Sauke numfashi ta yi sannan ta miƙe ta zare hijabin dake jikinta ta ƙarasa ta cire key ɗin data sakawa ƙofar, Tsaye ta ganta hannunta riƙe da wata warmer tana mata murmushi. Rungumeta Nana ta yi tana sauke ajiyar zuciya, Khadijah ta ce“Ke sai kin karyani?”

Ko saurarenta Nana bata yi ba, Ta karɓi warmern hannunta sannan suka shiga ciki, Tana ganinta mayar da key ɗin ƙofar ta rufe. Khadijah ta ƙarasa ta zauna gefen gadonta tana cewa

“wash, wasa-wasa da nisa fa daga apartment ɗin ku.”

Ita dai Nana bata ce komai ba ta ajiye warmern a ƙasa sannan ta zauna gefenta. Shiru Khadijah ta yi tana kallon ta, Nana ta ɗan yi murmushi ta ce

“Na ɗauka ba zaki zo ba. Ya su Ameema?”

“mene ya same ki Nana?”

Khadijah ta tambayeta tana kafeta da idanu. Girgiza kai Nana ta yi a sanyaye ta ce“bakomai fa” wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“nabi ba komai da gudu. Just tell me my friend!”

Shiru Nana ta yi tana kallon ta, ba zata taɓa iya faɗa mata ba abin da uncle ɗin ya yi mata ba. Dan ta san hakan ba daidai bane, Jin yanda ta yi shiru ya sanya Khadijah cewa“Idan kina ganin na takura ki bar shi kawai.”

“Mimi baki ji ba wai na auri uncle? Bai baki mamaki ba? Dan Allah kuma sai na zauna da uncle?”

Nana ta jera mata tambayoyin tana kallon ta. Murmushi Khadijah ta yi ta ce“To mene? Ni daɗi naji wallahi, saboda na san zai kula dake fiye da kowa a gidan nan.” Taɓe baki Nana ta yi kafin ta ce“to ta ina zai kula dani ɗin? Bayan kuma yana da mata.”

Kallon ta Khadijah ta yi, kamar ba zata yi magana ba can kuma ta ce“ke wait! Ba matar dana gani a ƙasan ba ce Zahra?” gyaɗa mata kai Nana tayi. Khadijah ta ce“kenan ita ce kishiyarki yanzu?” nan ma sake gyaɗa mata kan tayi. Khadijah ta gyara zamanta sannan ta ce“Yanzu tsaya wani abun ya taɓa haɗaki dashi? Ai na san kin gane me nake nufi” girgiza mata kai Nana ta yi dan ta fuskanci abin da take nufin. Khadijah ta ce“But why? Bazai taɓa yiwuwa ba!.” Da mamaki Nana ke kallon ta, can kuma ta ce“Mimi me ki ke nufi ne? Ni ban gane ba”

Kamo hannunta Khadijah ta yi ta sake matsowa kusa da ita yanda zata fahimce abin da zata faɗa ta fara cewa“kina ji...”

****
Anty Khadijah ce zaune gaban Malam sai Kaddu a gefenta, Ganin sai dube-dube yake bai ce komai ba ya sanya ta ce“Malam lafiya dai?” ɗago kansa ya yi bakinsa ɗauke da asiwaki yana taunawa ya ce“an gama. Bukatar ki zata biya, zaki aure shi, sannan kuma waccan yarinyar zata fito daga cikin gidan ke kuma ki maye gurbinta.” wani kyakkyawan murmushi Anty Khadijah ta yi, Ta juya ta kalli Kaddu, itama murmushin take kafin ta ce

“To malam abun sadaƙa fa?”

Girgiza kansa ya yi ya ce“Kamar dai yanda aka saba. Sai dai wannan karan zan baki wani abu da zaki yi amfani dashi” Ko kaɗan bata damu ba ta ce“Tom Malam, an gode Allah ya ƙara girma.” Murmushi kawai ya yi yana kallonta ta ƙasan ido yana suɗe baki. Anty Khadijah ta kalli Kaddu ta ce“To zaki jira mu ko tafiya zaki yi?” girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“no I'll wait.”

To kawai ta ce sannan ta miƙe ta nufi ɗayan soron, Shima ya tashi yana tattare babbar rigarsa yabi bayanta.

****
Khadijah ta dinga kallon ta ganin yanda take abu kamar wadda bata da kala, Ta ɗan ja tsaki ta ƙarasa gabanta ta karɓi plate ɗin ta ce

“kin tsaya sai wani tafiya ki ke kamar kwai ya fashe miki.”

Tura baki Nana ta yi, Ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe, Saurin matsawa ta yi daga wajen tana dariya ta ce“Mimi kin ga.” Khadijah dake jera plate ɗin akan tray ta ce“mene?”

“Ya dahu wallahi”

Ajiye plate ɗin ta yi ta ƙaraso gaban tunkuyar, Leƙawa ta yi taga yanda fried rice ɗin ta yi kyau ko a ido, Ta yi murmushi tana kallon Nana ta ce“ai kuwa, ashe kin iya girkin iskanci ne.” dariya kawai Nana ta yi, ta mayar da murfin ta rufe taja ta tsaya, Khadijah ta koma ta ɗauko tray ɗin tana kallon ta ta ce“A nan parlourn zan ajiye ko a ɗaki?”

“ko a parlourn zai fi ina ga.”
Chapter 79 · 0% Book details