← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 125

Sashe 75

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“wallahi Mom ban jin zan iya zaman nan. Cause gaba ɗaya ba yanda nake son namiji na gansa ba, kuma ni bana son zaman gida shi kuma ba zai bari na fita ba. Kin ga kuwa ai akwai matsala”

“Ke wace irin shashasha ce? Kina so ki ce min bashi da kuɗi ko me?” Anty Khadijah ta yi maganar rai ɓace. Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“ba wai bashi da kuɗi ba, yana da shi, amma ba kamar mijin Anty Zahra ba. Ni wallahi dana sani ma shi na ce ba wannan ba”

Numfasawa Anty Khadijah ta yi ta ce“wannan duk daga baya ne, ko kina nufin zaki auri mijin Zahra ne ku zauna tare?” Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“haba dai mu zauna tare, Ni ba zan iya zama da kishiya ba wallahi. Ita ma wannan dan ban ɗauketa kishiya bane, kin san bai taɓa kwana daƙinta ba.”

“kin ga wannan maganar bata waya ba ce, ki bari zan zo gidan na sameki.” Anty Khadijah ta faɗa saboda Umma da taga ta shigo ɗakin, to kawai Siyama ta ce sannan ta katse wayar, ta ajiye ta kan cabinet sannan ta ci gaba da abin da take.

Tana gamawa ta fito ta tsaya tana kallon Haule dake zaune har sannan a parlon ta ce“Tashi na aikeki” Toh kawai ta ce sannan ta miƙe ta zura hijabin da ke Hannunta. Siyama ta nuna mata warmern data ajiye a kitchen ɗin tana cewa“ki ɗauka ki kai wa Hajiya Babba, saura ki zauna magana.” Babu musu Haule ta shiga kitchen ɗin, ita kuma ta nufi sama don shiryawa saboda magriba ta tawo.

****
Around 9pm suna zaune a parlon, Noor na zaune a gefenta ta yi shiru tana kallonta ganin yanda take kuka kamar ƙaramar yarinya. Karasowa jikinta ta yi ta riƙeta cikin ƙaramar muryarta ta ce

“Anty stop crying! Stop plsss!”

Ta ƙare maganar tana sakin kuka ita ma, kallon ta kawai Nana ta yi sai kuma ta jawota jikinta tana ci gaba da kukanta. Suka dinga rera kukan a tare babu mai rarrashin su, wajejen 9:20 na daren aka buɗe handle ɗin ƙofar, Noor ta sauka daga jikinta da gudu ta ƙarasa inda yake ta rungumeshi. Durƙusawa ya yi dai dai tsayinta ya dinga kallon ta ganin yanda take kuka yasa ya ɗauketa yana faɗin “wane ya taɓa wa Abbie ƴar sa?” cikin shessheƙar kuka ta ce“Abbie kuka muke yi” yanda ta yi maganar cike da yarinta ya sanya shi murmushi. Ya zauna a kujerar da ke facing ta Nanar ya ɗorata kan cinyarsa ya ce

“Kuka kuma? Me yasa?”

Hannunta ta kai kan gemunsa tana murzawa a hankali ta ce“koba Anty Nana ba ce take kuka, to shi ne nake tayata.” Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Ai ko kin kyauta. Tashi ki je ki kwanta it's already late” to kawai ta ce sannan ta yi masa kiss a goshi ta sauka daga jikinsa ta ce“good night Abbie”

“Allah ya tashe mu lafiya.” ya ce yana jan kumatunta. Murmushi ta sakar masa sannan ta ƙarasa inda Nana ke zaune ta ce“good night Anty.” gyada mata kai kawai ta yi, Noor ta nufi sama tana tafe da gudu. Sai da yaga ta bar wajen sannan ya zame jikinsa ya jingina da jikin kujerar yana kallonta ya ce“zo nan” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa wajen tana goge hawayenta wasu na sake zubowa. Ta zauna gefensa ta sunkuyar da kanta. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin ya gyara zamansa yana kallonta sosai ya ce“mene ne kuma?” kamar jira take ta fashe da kuka, Ya dafe kansa a fili ya ce“oh ni Na shige su da Nana” ɗora kanta ta yi akan cinyarsa ta dinga rera kukan ta, ya yi shiru yana saurarenta kafin daga bisani ya ɗago kanta yana kallonta ya ce“rigimar mene ne? Me ki ke so?”

Cikin shassheƙar kuka ta ce“uncle ko ba kai bane” ta yi maganar a shagwaɓe yana sake narkewa a jikinsa. Hannunsa ya sanya yana share hawayen fuskarta ya ce“too me nayi miki?”

“Ba zaka siya min kaza ba?”

Shiru ya yi yana kallonta, can kuma ya ce“kazar mene ne Nana?”

Cikin son fahimtar dashi ta ce“kazar amarya mana. Maimoon ta ce min Yaya Aliyu ya siya mata kaza, kuma haka ma Hamida da Amrah suka ce min. To nima ba sai ka siya min ba dan Allah?” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Murmushi ne ya kusa kwace masa, ya yi gyaran murya kafin ya ce“to ai ban shirya cin amarcin ba ballantana na siya kazar amarci”

“To uncle ka shirya karɓar amarcin mana. Sai ka siya min kazar kaji!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 46.

Ta yi maganar tana marairaice fuska. Ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, bai san sanda wani kayataccen murmushi ya kwace masa ba. Nana ta sake matsawa jikinsa tana leƙa fuskar sa. Juyowa ya yi yana kallon ta, Lokaci ɗaya kuma ya tsuke fuska kamar ba shi ba. Langwaɓar da kanta ta yi taja hannunsa na dama ta ce“kaji uncle...” janye hannunsa ya yi daga nata yana cewa“to idan na shirya siyan kazar zan miki magana. Ni yanzu bani da kuɗin siyan wata kazar amarci” zaro dara-daran idanunta ta yi can kuma ta tsuke baki ta ce“uncle kai ne baka da kuɗin?” jinjina mata kai ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar, Nana ta mike tana riƙe da hannunsa ta ce“wallahi kana da kuɗi, kuma ma bayan duk ka fi su kuɗi” girgiza kansa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye dariyarsa ya ce“ni ɗin?” ta gyaɗa masa kai tana marairaice fuska. Taɓe baki ya yi ya saki hannunta ya ce“to ni bani da wani kuɗi, gara ki kama kan ki.” daga haka ya yi gaba ya barta tsaye a wajen. Ɗan buga ƙafafunta ta yi a ƙasa kafin ta ce“to ni wallahi so nake na ci kazar!” Ta ƙare maganar tana hawaye. Ko saurarenta bai yi ba ya haye sama abin sa. Ta koma ta zauna kan sofar tana matsar kwalla, Bayan wasu mintina Zahra ta sakko daga sama tana kallon ta. Can kuma ta shige kitchen abin ta, bata jima ba ta zo ta sake shigewa sama, Nana ta miƙe tana ɗaukan hular saƙin dake kanta ta nufi saman ita ma. Ɗakinta ta tashi ta ƙarasa gefen gado ta ajiye hular sannan ta zauna ta jawo wayarta da ke gefen pillow. WhatsApp ta shiga dan daman wifi ɗin ta a kunne yake, Ta yiwa Khadijah sallama. Ganin bata online ya sanya Nana jan ɗan siririn tsaki ta yi wurgi da wayar sannan ta miƙe. Toilet ta nufa bayan ta zame yar rigar dake jikinta, ta yi wanka sannan ta fito tana tsane jikinta da towel. Press ɗin ta ta buɗe ta ɗauki wata yar yalolon riga mara nauyi ta saka sannan ta nufi gaban mirror ɗinta ta shafa mai, Bayan ta kammala ta nufi kan gadonta ta faɗa tana sakin numfashi. A hankali ta dinga ɗaga ƙafafunta Salam kwanciyar ruf da cikin da ta yi, Tana nan kwance a haka har bayan kusan mintina goma wayarta ta fara ringing, Hannunta ta saka ta janyo wayar tana daga kwancen, Ganin numbern Mimi ya sanyata juyawa ta kwanta dai-dai sannan ta daga kiran. Khadijah da ke kwance kan nata gadon ta ce

“Hi Nana!”

Haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta kafin ta ce

“Sai yau zaki nemeni?”

Murmushi Khadijah ta yi ta ce“Afwan baby girl,Yar autar Ammarta.” Taɓe baki Nana ta yi ba tare da ta ce komai ba. Suka ɗan yi shiru can kuma Khadijah ta ce“gobe zan koma Kano fa”

“Daman kina Yola?”

Nana ta tambaya tana ɗan zaro idanu. Gyada mata kai ta yi kafin ta ce“eh fa. Ai da muka tafi gidan friend ɗin Daddy naje so ina can all this while.” Tashi zaune Nana ta yi ta ce“amma shi ne ko sau ɗaya baki faɗa min ba? Khadijah ki zo gidanmu dan Allah. Ki zo bestie i have alot to talk wlh, Dan Allah ki zo”

Shiru Khadijah ta yi tana jin ta, Can kuma ta ce“To bayan na ce miki goben zan koma Kano?”

“Kenan ba zaki iya zuwa saboda ni ba?”

Nana ta tambayeta muryarta a sanyaye. Khadr ta yi murmushi sai kuma ta ce“alright zan ga abin da ya kamata nayi. Idan zan zo I'll call you da safe”

Taɓe baki Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“amma kin san an yi min aure ba?”

Tashi zaune Khadijah ta yi da mugun mamaki ta ce“da wa? Yaushe kuma Nana?” ta jera mata tambayoyin tana zaro idanu. Numfasawa Nana ta yi lokaci ɗaya hawaye ya fara zuba kan fuskarta, Can numfashinta da Khadijah ta yi yasa ta ce“Nana, Are you there?”

Gyaɗa mata kai ta yi kamar tana gabanta sai kuma ta sake jan numfashi cikin shessheƙar kuka ta ce“Idan kin zo gobe zan faɗa miki.” Gudun kada ta sakata kuka yasa Khadijah ta ce“tom shikenan, goben zaki ganni da wuri in sha Allah.”

“Tom sai kin zo.” cewar Nana, Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar, Jifa ta yi da wayar can ƙarshen gado, ta koma ta kwanta tana kuka ƙasa-ƙasa ji tayi gaba ɗaya maganar auren ta dawo mata sabuwa. Ta daɗe tana rera yan matan hawayenta har bacci ɓarawo ya yi gaba da ita.

Washegari da sassafe Anty Khadijah ta zo gidan, Lokacin Safwna na shirin fita, Ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa sannan ya bar gidan. Siyama ta sauke numfashi tana kallonta ta ce“Mom welcome” Fuska babu annuri Anty Khadijah ta ce“ba wannan ya kawoni ba Siyama, muje ciki mu yi magana.” okay kawai ta ce sannan ta yi hanyar upstairs ɗin tana biye da ita. Kalle-kallen corridor ɗin ta dinga yi can kuma ta kalli Siyama da tayi gaba ta ce“Ina ita kishiyar ta ki?”

Cak ta tsaya sai kuma ta juyo ta ce“haba Mom ya za'a yi ki ganta anan parlour da safe? Ai indai mai gidan bai fita ba, ba zaki taɓa ganinta a waje ba.” jinjina kai ta yi ta ce“Hakan ma yana da kyau” Siyama ta ɗan yi murmushi sai kuma ta juya ta buɗe ɗakin.
Chapter 75 · 0% Book details