Sashe 53
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Siyama ta sake fari da idanunta sannan ta ce“eh aurenka mana, ba yau za'a ɗaura maka aure da Nana ba?” tsaki ya yi yana kallon gefe ya ce“sai aka ce miki ita zan aura?”
Ganin kamar ransa ya fara ɓaci yasa Siyama ta langwaɓar da kanta ta ce“a'a ai haka naji ne”
“To ba ita zan aura ba. Ki je ki jirani kinji”
Siyama ta saki murmushin jin daɗi ta ce“tom shikenan sai ka zo” daga haka ta juya ta bar wajen tana tafe cike da kwarkwasa. Safwan ya haɗiye wani yawu sannan ya juya ya bar wajen.
Ƙarfe 10:00 na safe Abba ya shigo ɗakin yana sanye da wata dakkakiyar madam gezner fara ƙal ɗinkin jamfa da babbar riga, ya sanya hular zanna akansa sai zuba ƙamshi yake. Ko ba'a faɗa maka ka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe a gurin ba, Ya tura kofar dakin Amma bakinsa ɗauke da sallama. Zaune ya sameta tana sanye da wani lace mai azabar kyau da tsada itama, sai dai sam fuskarta babu annuri, musamman yanda taga Nana ta yi shiru tun ɗazu bata ce komai ba.
Abba ya dinga kallon su sai kuma ya ce“Nana ki je apartment ɗin Hajiya Babba”
Sai a sannan Nana ta ɗago kanta ta kalleshi da idanunta wanda suka sake kumbura da alama ba ƙaramin kuka tasha ba. Sanye take da wani ubansu lace blue colour mai adon pink a jiki, an yi musu ɗinkin straight gown wadda ta ɗan kama jikinta amma ba sosai ba, ɗankwalin lace ɗin na ajiye gefen gadon kanta wanda yasha gyara sai sheƙi yake. Murya a sanyaye ta ce
“to Abba”
Ya jinjina kansa sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Amma ta sauke numfashi ta kalleta ta ce“zo na ɗaura miki ɗankwalin” babu musu Nana ta tsaya ta daura mata duk da ba wani ɗaurin me kyau bane amma sai ya saka ta ƙara kyau, ta miƙa mata pink ɗin mayafinta wanda ya kasance big size ta ce“saka ki tafi” a gefe ɗaya Nana ta yafa sannan ta tashi tsaye tana gyara zaman rigar jikinta. Amma ta ce“bari naje wajensu Ramlah” to kawai Nana ta ce Amma ta fice daga ɗakin. Komawa ta yi ta zauna tana fashewa da wani sabon kukan, ta kalli wayarta sai kuma ta sake rufe fuskarta da hannayenta cikin kuka ta ce
“nashiga ukuna, ya zan yi da raina. Allah ka yafe min”
Ta faɗa tana ƙara sautin kukan nata.
****
A can compound ɗin Hajiya Babba kuwa jama'a ne a cike na birnin Yola dama cikin ƙauyuka, sai shige da fice ake ana kai komo, kowa ka ganshi tsaf dashi babu alamar babu ko talauci a tare da duk wani ɗan dangin Shuwa.
Angwayen duk sun yi shiga iri ɗaya, Shadda gezner milk colour an yi aikin sirfani da brown ɗin zare, sai baza manyan riguna ake, ko ina ka gifta sai ƙamshi ne ke tashi. Papa kuma da Abdusammad irin kaya ɗaya suka yi da Abba. Hajiya Babba ma ta ci kwalliya cikin wani tsaddajen lace ɗinkin boubou. Ta yafa mayafinta aka sai zuwa dibar gaisuwa ake, haka ma Atta irin kayan Hajiya Babba ne a jikinta amma ita sam ta kasa zama sai shiga take tana fita. Atta ta leƙa dakin dasu Maimoon ke zaune kowacce da lace irin na Nana a jikinta, ta dinga kallonsu ganin babu mutuniyarta a ciki yasa ta ce“Ke Maimuna ina Nana?” Maimoon ta miƙe tana gyara mayafinta ta ce“har yanzu bata zo ba bari naje na kirata” to kawai Atta ta ce sannan ta saki ƙofar ɗakin. Moon ta zura takalmanta wanda suka kasance pink colour sannan ta fice daga ɗakin.
Sanda ta fito har an baza carpet a compound ɗin Hajiya Babba dan daman a nan ne ake daura auren, Ta shige da sauri tana jan mayafinta ya rufe kanta.
Koda ta shiga ɗakin zaune ta samu Nana sai kuka take, ta rufe ƙofar da key sannan ta ƙarasa ciki tana kallonta ta ce“Nana wani abun kuma?”
Ɗago kanta ta yi hawaye sai zubowa yake daga idanunta ta ce”na shiga uku Maimoon, na shiga ukuna, mutuwa zan yi” da mamaki Maimoon ke kallonta, lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, ta zaune gefenta tana rike hannunta ta ce“ki faɗa min mene ne? Meya faru?”
Kasa magana ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta ɗora kanta akan cinyar Maimoon tana ci gaba da kukanta.
Ƙarfe 10:20 Safwan ya ƙaraso wajen yana gyara zaman babbar rigarsa, idanunsa ya sauka kan mutane da ke zaune a compound ɗin kowanne jira yake a zo a ɗaura auren. Ya yi jim sai kuma ya ƙarasa inda su Aliyu ke tsaye ya tsaya, kallonsa Aliyu ya dinga yi ganin yanda idanunsa suka yi jajur ya ce
“Safwan ko kai ma kukan auren ka yi?”
Cike da zolaya ya yi maganar, dan haka Hamid ya yi dariya ya ce“ai kasan ɗan auta ne zai auri yar auta za'a ga shagwaɓa” suka yi dariya duka. Shi kuwa Safwan kasa dariyar ya yi, murya can ƙasa ya ce“Yaya nifa na fasa auren nan”
Aliyu da yaji kamar daga sama ya ce“me ka ce Safwan?” ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleshi sai kuma ya ce
“cewa nayi na fasa auren nan, ni ba zan auri Nana ba!”
”What!”
Hamid ya yi maganar yana zare idanu, sai kuma ya girgiza kansa yana dafa kafaɗarsa ya ce“kai dallah kar ka kawo mana wasa anan kaji”
“Wasa? Kuma kawai sai nayi wasa? Wallahi na fasa auren nan, ba zan auri Nana ba!”
Ya ƙare maganar yana zazzaro idanu. Aliyu da yaga abun nasa na neman zama na gaske ya riƙe shi ya ce“Safwan lafiya?”
“kawai a tara kowa a Apartment ɗin Hajiya wallahi ba ita zan aura ba!”
Daga haka ya fizge jikinsa ya yi hanyar balcony ɗin Hajiya. Kamar wasu marasa wayo haka suka dinga bin sa da kallo, cike da mamakin furucin nasa, Aliyu ya numfasa ya ce“bari dai na samu na yi magana da Papa” daga haka ya bar wajen shima. Sultan kuwa shiru ya yi dan daman tun ba yau ba ya lura da take-taken Safwan ɗin.
****
Tsaye suke gaba ɗaya a parlon, Abba, Papa, Sultan, Aliyu, Hamid, Atta, Hajiya Babba, Mama. Idanunsa duka akan Safwan wanda ke tsaye tsakiyar ɗakin, kansa a sunkuye, Papa ne ya yi ƙarfin halin faɗin
“Safwan me ka mayar da mutane? Abokan wasanka?”
Shiru ya yi bai ce komai ba, dan tun ɗazu suke tambayarsa amma ya gagara cewa komai. A fusace ya buɗe ƙofar parlon ya shigo, kai tsaye wajen Safwan ɗin ya karasa yana zuwa ya ɗaukeshi da mari har guda biyu sannan ya cakumi kwalar rigarsa yana masa wani irin kallo cike da tsananin ɓacin rai ya ce
“Ashe daman baka da mutunci? Ashe baka da hankali ban sani ba? Are you out of ur sense!”
Ya ƙare maganar a tsawace yana jijjigashi, gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi sai huci yake kamar mayunwacin damisa. Abba ne ya ƙaraso wajen ya riƙe hannunsa ba tare da ya ce masa komai ba, Abdusammad ya fizge hannunsa ya ce
“Abba dan Allah rabu dani! Mu yaron nan zai zubarwa da mutunci! Da can bai ce ba zai aureta ba sai yau da aka tara dubban al'umma a waje? Shi ya isa?” ya ƙare maganar yana huci, sai kuma ya sake cakumar Safwan ya ci gaba da faɗin
“To wallahi tallahi sai ka aureta! Kai baka isa ka ce ba zaka aureta ba”
Ya hankaɗa shi har sai da ya kusan faɗuwa Papa ya tare shi. Gaba ɗaya parlon ya ɗauki tsit babu wanda ya yi magana. Safwan ya numfasa sai kuma ya ce
“Ni fa Abba ba wani abun nace ba, kawai cewa nayi ba zan auri Nana ba! Kuma ita ma yarinyar a kirata a tambayeta ta ce ba zata aureni ba, kaga kuwa babu amfanin na auri wadda bana ra'ayi kuma bata ra'ayina, dan haka dan girman Allah kada ku tilasta min, wallahi ba zan iya auren Nana ba, akwai wadda take cikin raina tun ba yau...”
Bai ƙarasa maganar ba Abdusammad ya rufe shi da duka ya shaƙe nasa wuya cikin masifa ya ce“to kar ta so kan, ko tana so ko bata so wallahi sai an yi auren nan!”
Aliyu ne ya janyeshi daga jikinsa yana fadin “Ya isa haka Buddy, abi komai a hankali” banza Abdusammad ya yi masa ya fizge jikinsa yana kwafa. Abba ya sauke numfashi sannan ya kalli Safwan ya ce
“Ka san da baka sonta ka bari muka tara jama'a Safwan? And wait, wane ya ce maka sai kana sonta sannan zaka aureta? Mu ba haka tsarinmu yake ba, kuma ku baku isa ku zo ku lalata mana tsari ba! Dole ne ka auri Nana!”
Safwan ya dinga kallon Abba dan yana matukar ganin girmansa kuma baya jin zai iya sa'insa dashi. Dan haka ya sunkuyar da kansa murya a sanyaye ya ce“ka yi haƙuri Abba wallahi ba zan taɓa auren Nana ba!”
Hajiya Babba ce ta ƙaraso wajen ta dinga kallonsa sai kuma ta dauke shi da wani marin cikin matsanancin ɓacin rai ta ce“Mu zaka wulaƙanta Safwan? So ka ke a yi mana dariya? To wallahi idan har ka sake wannan maganar sai dai ka nemi wata uwar amma bani Khadijah ba!”
Da sauri ya ɗago kansa hannunsa dafe da kuncinsa, Hajiya Babba ta maka masa wata uwar harara tana barin wajen, Papa ne ya sauke numfashi sai kuma ya ce“su wane a ciki?”
“Yaran ne”
Mama ta bada amsa. Papa ya kalli ƙofar sai kuma ya ce“to su fito” ok kawai Mama ta ce sannan ta ƙarasa ta buɗe ɗakin, suna zaune kowacce ta yi shiru jiki a sanyaye dan duk abin da ake faɗa suna ji. Mama ta ce musu su fito sannan ta bar wajen, a sanyaye suka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya, suka ƙaraso parlon suka tsuguna cike da ladabi. Papa ya dinga kallonsu sai kuma ya ce
“Ina Nana?”
“tare muka fito ta ce bari taje ta manta wayarta.”