← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 125

Sashe 86

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamar jira take ta ɓare masa baki ta fara kukan data saba. Ya yi shiru yana saurarenta, Can kuma ya ce“To ya isa haka ki tashi ki shirya” banza ta yi masa ta ci gaba da kukanta. Ya ɗago fuskarta ya riƙe cikin tafin hannunsa ya ce“Idan baki min shiru ba zan saka ki mai dalili.” Tura baki ta yi ta janye fuskarta, Ya tashi tsaye yana riƙe da cazbaha a hannunsa ya ce“Ki shirya kin ji. Ina zuwa”

A sanyaye ta ce to sannan ya juya ya bar ɗakin.

****
Misalin ƙarfe 6:30 ne na safe, gaba ɗaya jama'ar estate ɗin suka taru a compound ɗin gidan. Kamar yanda ranar da ya zo suka taru haka ma yau ɗin suka sake taruwa, Sai da ya yi Sallama da kowa sannan ya nufi wajen Hajiya Babba, Jiki a sanyaye ya yi mata sallama, Ta amsa babu yabo babu fallasa. Noor dake hannunsa ya ɗaga mata hannu, Murmushi Hajiya Babba ta yi ita ma ta daga mata hannun. Jiki a sanyaye ya bar wajen, A bayan mota ya sakata sannan ya sake ma su Abba sallama. Nana kuwa dakyar ta bar jikin Amma tana kuka, ko ranar da aka tafi da ita gidan bata yi kuka kamar yau ba, Dakyar Amma ta rarrasheta ta shiga motar. Tsayawa ya yi yana karewa estate ɗin da kallo, kamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamarkamar yau ya zo gashi har zai koma. Ya sauke numfashi sannan ya nufi cikin motar bayan an bude masa, Shiga ya yi yana sake daga musu hannu. Atta kuwa komawa gefe ta yi ta zauna ta dinga rusa kuka, a haka har motocin suka fara fita daga gidan ɗaya bayan ɗaya kamar dai yanda suka shigo, Ajiyar zuciya suka sauke sannan kowa ya nufi hanyar gidansa.

08106608363
Nanameera.
*🌹 NAANAH 🌹*

Follow my account
Wattpad@Nanameera08
Arewabooks@Nanameera08.

Page 52.

Around 4:00am jirgin nasu ya sauka a JFK airport na New York. Bayan sun fito daga ciki suka tarar da jerin motocin dake jiransu wanda aƙalla sun kai guda 10. Ita dai Nana sai sake jan mayafinta take saboda ɗan yayyafin da ake, Abdusammad ya shiga cikin wata Bentley black colour, Nana tabi bayansa itama. Ganin haka ya sanya Zahra yin gaba, ta buɗe wata motar ta shiga hannunta riƙe da Noor wadda ta yi bacci, Nan da nan kuma motocin suka bar wajeni.

Park avenue road,
Upper East side,
New York.

A dai-dai bakin wani madaidaicin gate motocin suka ɗan tsaya, kafin daga bisani gate ɗin ya fara zugewa da kansa, Wani irin ƙaton gida ne iya ganinka, wanda ta wajen ba lallai ka yi tunanin ya kai girman haka ba. A tsakiyar compound ɗin gidan na biyu motocin suka yi parking dan iya nan ne mota ke tsayawa, Sai a sannan Abdusammad ya sauke numfashi sannan ya zare seat belt ya buɗe motar ya fito. Jiki a sanyaye ita ma Nana ta fito tana ƙarewa compound ɗin kallo, Gurin an ƙawatashi da furanni masu kyau da ƙamshi irin su white rose da lavender. Ta ja lumsassun Idanunta ta rufe tana shaƙar iskar wajen mai daɗi, Duk yanda take jin babu daɗi data bar gida sai da ta manta. Ta gyara tsaiwarta ganin Zahra ta fito har sannan tana rike da Noor, Gaba ya yi suka fara bin sa a baya, Duk inda ya shige sai ma'aikatan wajen sun gaishesa a haka har ya shiga third gate ɗin wanda yake da launin golden, Wani irin haɗaɗɗen compound ne mai kyau da tsari. Ya lumshe idanunsa sakamakon iskar data doke shi mai ɗauke da ƙamshin mint da fresh flowers. A hankali yake taka pathway ɗin wanda ya ɗan lanƙwashe har zuwa ga kofar entrance ɗin gidan, Nana kuwa tun da ta shigo idanunta ke kan fountain ɗin dake ɓangaren damanta, Sai zubar da ruwa yake duk da yayyafin da ake, ga wasu leds masu kyau da haske dake ƙawatashi. A gefensa kuma flowers ɗin orchids da ross sun ƙara taimakawa wajen ƙawata wajen ɗin, Ta janye idanunta tana kallon ɗaya side ɗin, ƙananun bishiyun marble da cherry blossom ne, daga gefensu suka wasu red leds ne waɗanda ke kawowa suna ɗaukewa. Ɗaga kanta ta yi ta hangi dogon ginin gidan, lokaci ɗaya kuma ta sauke kan nata ta ci gaba da tafiya. Sai da ya saka password a jikin ƙofar entrance ɗin wadda ta kasance ta glass sannan ta zuge a hankali, Ya tura kansa ciki bakinsa ɗauke da sallama da ba lallai sun ji ba.

Ɗaya bayan ɗaya suka shiga, Nana ta tsaya tana ƙarewa ƙaton parlourn kallo, Wasu Italian sofas ne a ciki yayinda marble tiles ya yi kamar carpet a wajen, A tsakiyar parlon kuma crystal chandelier ce mai bada launin golden. Daga can left side kuma pione ground ne, wanda aka ƙawata shi da kayan sauti masu tsada. Nana ta juya ta kalli gefenta da dama daga jikin bango, fireplace ne wanda ke ci a hankali, kuma shi ne ya taimaka wajen raguwar sanyi a parlon.

Ɗaga kanta ta yi tana kallon staircase ɗin da suke can nesa da ita, Bene huɗu ne a wajen, Biyu a haɗe, biyu kuma a rarrabe. Ya jima tsaye a wajen kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallon su duka

“Nana here it's ur apartment. Ki je ki huta”

Ya ƙare maganar yana nuna mata benan dake right hand side ɗin biyun, Zahra kuwa gaba ta yi abin ta dan already ta san nata ɓangaren. Shima bai tsaya jiran amsar Nanar ba ya nufi nasa ɓangaren da sauri dan a mugun gajiye yake, Tamkar gunki haka Nana ta tsaya a wajen. Can kuma ta tura baki ta nufi hanyar benan daya nuna mata tana tafe kamar wadda kwai ya fashewa a jiki.

A hankali ta dinga taka fluffy rug ɗin dake cikin ƙaton parlourn, komai na ciki coffee and white ne, kaya masu kyau da kuma tsada, Tun daga kan kujeru har zuwa kayan wutar dake ciki, gaba ɗaya sai taga ashe parlourn ƙasa ba ma kyau ne dashi ba. Ta ja dogon numfashi ta sauke hannayenta riƙe da ƙugunta, daman tuni veil ɗin abayar ya zame ya dawo kafaɗarta sai hula ce kawai akan. Ta ja jikinta a sanyaye ta nufi ƙofar data gani wadda take da tabbacin nan ne bedroom ɗin.

Kamar yanda ta yi tunani haka ce ta faru, haɗaɗɗen bedroom ɗin mai ɗauke da furnitures kalan na parlourn, a shimfida farin bedsheet akan gadon yayinda aka ɗora duvet coffee colour. Ta jima tana ƙarewa ɗakin kallo kafin ta ajiye wayarta gefen gadon ta nufi banɗaki, Shima sai da ta tsaya ta gama dube-dubenta, ta karance duk shower set ɗin da aka ajiye sannan ta ɗauki wanda take ganin zai fi mata ta fara wankan dashi, tana gamawa ta ɗauro alwala sannan ta fito ɗaure da towel. Ta ƙarasa gaban dogon press ɗin da tagani ta buɗa. Yawancin kayan ciki English wears ne, sai dogayen riguna tsirari, ta ɗan tura baki sannan ta janyo wata riga doguwa wadda bata shige gwuiwarta ba ta zura sannan ta naɗe gashin kanta ta ɗaure da riboom. Rasa hijabin sallah ta yi, dan haka ta sake buɗe press ɗin ta ɗauko abaya da veil ɗinta ta saka sannan ta gabatar da sallolin da ake binta... Bayan ta idar ta zare doguwar rigar ta faɗa kan gadon, Taja duvet ɗin ta rufe har kanta tana jin wata nutsuwa na saukar mata, kasancewar ta gaji sosai ya sanya nan da nan bacci ya ɗauketa.
Chapter 86 · 0% Book details