Sashe 105
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai Haule bata ce komai ba, Sai kallon ta take. Atta ta kalli Nana wadda ta yi shiru ita ma ta ce“Ke kawon faranti nan” Tura baki Nana ta yi tana miƙe ƙafarta ta ce“Ni fa Atta na gaji” Duka Atta ta kai mata tana cewa“Kin gajin uban ki? Dalla tashi ni!” Kamar zata yi kuka ta sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin. Zaune ta hange shi kan kujera, Abba na kusa da shi yana masa magana, Nana ta tsaya a wajen tana kallon sa, gaba ɗaya kamar bashi ba, Ya ɗan yi duhu ya kuma rame. Ta jima a wajen ganin bai ganta ba ya sanya ta nufi kitchen ɗin da sauri, Koda ta dawo parlourn bata same shi ba sai Abba kawai. Ta kalleshi ta ce“Abba!”
Kallon ta Abba ya yi ya ce“Na'am Nana”
“Ina uncle ya tafi?”
Ta tambaya tana kallon sa itama. Dan murmushi Abba ya yi yana miƙe tsaye ya ce“Naji ya ce apartment ɗin Hajiya Babba zai je” To kawai ta ce sannan ta nufi ɗakinta da sauri. Miƙawa Atta plate ɗin ta yi, Atta ta warce tana cewa“Ke ban da banza ina ta jiran ki yarinya mai ciki kin bar ta da yunwa?” Tura baki Nana ta yi ta ce“To wai ba gashi na kawo miki ba?” Harararta Atta ta yi ta ce“Ki je dan kan ki, Ke kin zauna sa'annin auren ki duk sun kusa haihuwa ana ta abun arziki ke kin zauna!” Tura baki Nana tayi ta juya tana cewa“Ni ina ruwana! Ni yar iska ce to?”
Riƙe haɓa Atta ta yi tana ƙoƙarin buɗe warmern gabanta ta ce“Kaji banza! Dan uba ki ƙarya ki ke yi ki ce baki san namiji ba, dama a ce bashi bane da sai na yarda!” Ita dai Nana kallon ta kawai take sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Babu kowa a parlorn dan haka ta fice da sauri, Tafiya ta dinga yi tana ɗan kalle-kalle. A bakin kofar gidan Hajiya Babba ta tsaya tana tunani, Can kuma ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Shi kaɗai ta hango kan kujera yana danna wayarsa, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ƙarasa ciki, Tsayawa tayi a gabansa a sanyaye ta ce
“Uncle!”
Jan hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa bayan ya ajiye wayar hannunsa ya ce“Na'am Nana, Kin ɓuya” Kwantar da kanta ta yi akan ƙirjinsa a shagwaɓe ta ce“To ai kaina baka nemana” ɗan waro idanunsa ya yi ya ce“Ni ɗin?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗan murmushi ya ce“To na tuba. Ban samu sukuni bane, amma da zarar na samu ai zan neme ki” Shiru ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa, Sun jima a haka kafin ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“Uncle!”
“Babyn uncle!”
Ya ce yana ɗaga mata gira.
Murmushi ta yi ta ce“ka ci abinci?” Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi shima, Ta ɗan haɗe rai ta ce“Ni wallahi baka ci ba!” Ɗan zaro idanu ya yi ya ce“Ni na ce miki?” Tana ƙoƙarin yin magana aka buɗe ƙofar parlourn, Sultan ne ya shigo sai kuma ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce“Afwan pls” Ya juya ya fice daga parlon, Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, Abdusammad da ke lura da ita ya ce
“Mene ne?”
Girgiza masa kai ta yi ta ce“Ba komai.”
“Kin tabbata?”
Ya ce yana kafeta da idanu, Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh uncle” Murmushi ya yi ya ce“Alright” Ya yi maganar yana jan kumatunta. Murmushi ta yi sai kuma ta sauka daga jikinsa ta ce“Na tafi kada Amma ta neme ni” Gyaɗa mata kai ya yi dan bai ji zai iya riƙe tan ba ya ce“Okay bye” ta ɗaga masa hannu sannan ta fice daga parlourn.
Da daddare bayan ya shiga gidan ya tarar da Zahra har ta yi shirin kwanciya. Bai ce komai ba ya juya zai bar dakin, Ta miƙe zaune ta ce“Doctor!”
Cak ya tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce“Daman zan tambaye ka ne”
“Mene?”
Ya ce yana juyowa,
“Wane abinci Hajiya Babba ta fi so?”
Da ɗan mamaki ya ce“me zaki yi da sanin hakan?” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a fa kawai dai na tambaya ne, ka faɗa min idan ba damuwa” Numfasawa ya yi ya ce“Tuwon shinkafa miyar egusi” Murmushi Zahra ta yi ta ce“na gode.” murmushin shima ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta kwanta.
****
Anty Khadijah na ƙoƙarin rufe jikinta da duvet wayarta dake gefen gadon ta fara ƙara, ta sanya hannunta ta dauka ganin lambar Kaddu ya sanya ta ɗaga wayar tana murmushi ta ce
“Ƙawata ya aka yi? Fatan komai na tafiya dai-dai?” Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce
“Ke dai bari, na bata kuma ta amsa, nan bada jimawa ba zan yi Wuff...”
“Dashi!”
Kaddu ta ƙarasa tana dariya, tuntsirewa da dariya Anty Khadijah ta yi ta ce
“Nan bada jimawa ba zan zama matar Abdusammad, Zahra kuma zata fito, ita da waccan yarinyar!”
08106608363
Nanameera.Page 62.
Murmusawa Kaddu ta yi cike da nishadin jin abin da ta ce, Anty Khadijah ta ce“Ke ni sai da safe dare ya yi” Sallama suka yi sannan ta kashe wayar, Ta kwanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi a gidan Abdusammad Idan ta aure shi.
****
Washegari da safe Nana na zaune gefen gado tana danna wayarta aka buɗe ƙofar ɗakin, Haule ce ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin bowl, Nana ta kalleta amma bata ce komai ba. A gefenta ta ajiye ta juya zata fita, tashi Nana ta yi tana haɗe rai ta ce“Mene wannan?” A sanyaye Haule ta kalleta kafin ta ce“Atta ce ta kawo min, wai faten dankali ne.” Yatsine fuska Nana ta yi ta sauka daga kan gadon tana cewa“Taɓ, Ai sai ki yi ta zama tana kawo miki kayan ƙazanta kina ci.” Bata ce komai ba, Itama Nanan bata tsaya sauraren abin da zata ce ba ta fice daga ɗakin, Haule ta kalli bowl ɗin dankalin sai tiriri yake, Sai kuma ta sauke numfashi ta juya ta fice daga ɗakin. Zaune ta sameta a parlon ta kunna tv tana kalla tana cin chocolate, Haule ta nufi kitchen kai tsaye, Murfi ta ɗauko ta koma ɗaki. Ita dai Nana bata kalli inda take ba, After some minutes ta tashi tana ajiye ledar chocolate ɗin ta kunce veil ɗin data ɗaura a kanta ta yafa sannan ta fice daga parlourn. Apartment ɗin Maimoon ta nufa, Koda ta shiga zaune ta sameta akan kujera ta dafe cikinta wanda ya fito sosai. Nana ta ƙarasa ciki ta zauna tana cewa
“Sannu matar nan!”
Harararta Maimoon ta yi tana murmushi ta ce
“Yauwa sannun ki ƴar nan”
Nana ta tuntsire da dariya kafin ta ce“Me ki ka dafa?”
“Ni bani nayi girki ba, Ya Aliyu ne ya yi idan zaki ci”
Waro idanu ta yi tana murmushi ta ce“Shi Yaya Aliyun ne ya yi miki kirki ki ka ci? Lallai!”
Taɓe baki Maimoon ta yi ta ce“To mene ne? Ai shi ne yake girki yanzu, Saboda ni ba zan iya ba, wahala nake sha.” Jinjina kai Nana ta yi tana riƙe da haɓarta ta ce
“Eh lallai! Kin isa”
“Idan ba zaki ci ba ki tashi ki girka naki daban”
Tashi ta yi ta zare mayafin kanta ta nufi kitchen tana cewa“To tun da yunwa nake ji ai dole nayi girki.”
Ita dai Maimoon kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗauke idanunta, Nana na shiga kitchen ɗin ta fara buɗe-buɗen kaya tana duba abin da zata dafa, Can dai ta yanke shawarar yin shinkafa da wake dan tana ɗaya daga cikin abincin da take so. Sai da ta tsince waken wanda ya kasance manya sannan ta wanke ta zuba a tukunya ta ɗora, Ta koma parlour tana kallo time to time tana zuwa tana dubawa, Bayan ya dahu ta zuba shinkafar wadda bata da yawa sannan ta saka gishiri da maggi ta rufe, Ta tsaya ta fara yanke-yanken kayan lambunta har ta gama, ta wanke sannan ta ajiye gefe. Bayan ta sauke abincin ta zuba a plate ta zuba salad ɗin data yanka da cabbage da cucumber ta ɓare kwai guda biyu ta ɗora akai, Robar yajin da tagani a wajen ta ɗauka ta fito parlour, Turus ta yi ganin Aliyu zaune shi da Abdusammad, Maimoon na zaune tana kallon su, Jiki a sanyaye ta ƙarasa parlourn ta ajiye wayar plate ɗin akan table ta koma ta zauna kusa da Maimoon.
“Nana daman kina nan?”
Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta ce“Eh Yaya ina nan, ina kular maka da matarka” wata harara Maimoon ta watsa mata kafin ta kalleshi a shagwaɓe ta ce“Wallahi Yaya ƙarya take, tsokanata kawai take.” Taɓe baki Nana ta yi ta mai da Idanunta kan Abdusammad wanda bai ce komai ba tun ɗazu ta ce
“Unclee...!”
Ɗaga mata gira ya yi ya ce“Na'am”
“Ba zaka kulani ba?”
Ta tambaya tana marairaice fuska. Ɗan murmushi ya yi sannan ya yi mata alama da ta zo da hannu, Ta tashi jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake ta zauna gefensa. Dafa kanta ya yi murya a nutse ya ce
“Ƴar rigimar uncle”
Jingina kanta ta yi akan kafaɗarsa ta ce
“Uncle...”
Murmushi ya yi ya ce“Nana kar sunan ya ƙare”
Turo baki ta yi ta ce“To ba zan kira ka ba?” Girgiza mata kai ya yi yana kallon plate ɗin data ajiye ya ce“Ni na nace miki?” Murmushi ta yi ta tashi daga wajen tana kallon Maimoon dake kallon ta, Ta ɗauki plate ɗin ta koma inda yake ta zauna tana miƙa masa ta ce
“Uncle ga abinci da kaina na girka maka, anan gidan wai Yaya Aliyu ne yake girki..” ta ƙare maganar tana dariya, Kallon ta ya yi sai kuma ya kalli Aliyu wanda ke murmushi, Fuskarsa a tsuke ya ce
“Kai ne ka koma girkin abincin?”
Gyaɗa masa kai ya yi kafin ya ce
“Eh mana, tun da bata da lafiya ai dole na taimaketa.” Jinjina kai Abdusammad ya yi yana shafa gemunsa, Aliyu ya kalli Maimoon ya ce
“Tashi muje ciki ki kwanta”