← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 125

Sashe 36

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“wallahi aunty tsautsayi ne, ban yi tunanin haka daga gare shi ba, abokinsa ne ya ce min bashi da lafiya shi ne naje duba shi, ya bani lemo nasha sai bacci ya ɗaukeni, ina ga a sannan ya yi min haka, na yarda dashi but he deceive me, they trick me aunty, sun lalata min rayuwa, ya zan yi aunty? Ya xan yi dashi yanzu?”

Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, rungumeta Zahra ta yi itama tana kukan ta ce“kin yi kuskure Nana, ba'a bawa namiji yarda irin haka, kin yi kuskuren zuwa wajensa ba tare da shawara ba, amma yanzu aikin gama ya riga da ya gama, sai dai a yi addu'ar Allah ya kawo wa lamarin sauki”

“ya zan yi aunty? Ban san me zai buƙata daga gareni ba, kuma yace idan ban yi masa ba sai ya yaɗa hotuna na kowa ya gani, sai ya tabbatar ya ɓata sunan gidanmu, taya zan bari haka ta kasance aunty? Ba zan iya ba, tsoro nake ji aunty Zahra, wallahi zuciyata bugawa take yi da karfi aunty...”

Zahra ta dinga shafa bayanta tana jin yanda take kuka mai ban tausayi, tunda take da Nana bata taɓa bata tausayi irin na yau ba, yarinya ce ƙarama amma yanzu rayuwarta ta faɗa wani hali wanda Allah ne kawai zai iya fitar da ita, wace irin jarrabawa ce wannan?...

Sai ƙarfe 9:00 na dare sannan ta bar apartment ɗin Zahra, koda ta koma gida Amma ta samu zaune a parlon bayan ta haɗe kayan lefen can gefe guda, ta ƙarasa jiki a sanyaye ta zauna kusa da ita, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce“Nana sai yanzu?” gyaɗa mata kai kawai ta yi, Amma ta sake cewa“kin ci abinci?” gyaɗa mata nan ma ta yi, ta yi shiru can kuma ta ce“ko zaki ga kayan auren naki?” tashi ta yi tana girgiza kanta ta ce“a'a Amma bacci nake ji” Amma ta dinga kallonta sai kuma ta taɓa jikinta, zafi taji amma ba can ba dan haka ta ce“kuka ki ka yi ko Nana? Ba zaki yi haƙuri ki yarda da ƙaddarar ki ba kenan? Kin fi so ki ɗaga hankalinki sannan ki ɗaga namu? Ba zaki haƙura ba ko?” kasa jurewa ta yi dan haka ta fashe da kuka tana rungume Amma ta ce“na haƙura Amma, wallahi na haƙura, ba wai ina kuka bane saboda ban sami wanda nake so ba, ina kuka ne kawai saboda ban san wace irin rayuwa zan yi ba bayan auren, amma na haƙura wallahi, tuntuni na cirewa raina wannan, dan Allah ki yi min addu'a Amma, ki dinga yi min addu'a wallahi tsoro nake ji”

Amma ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin tausayin tilon ƴar tata, ta shafa kanta a sanyaye ta ce“to Nana daman ina miki addu'a kullum sannan zan ci gaba da yi miki, kema ki dinga addu'a kin ji, kuma ki daina jin tsoro babu abin da zai faru sai Alkhairi”

Jinjina kanta ta yi sannan ta tashi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai, Amma ta bita da kallo har ta shige daƙinta.

Washegari around 10:40 na safe ta fito daga ɗakinta bayan ta shirya cikin wata atampa tana kallon Amma ta ce“zan je wajen Aunty Zahra” to kawai Amma ta ce sannan ta fice daga gidan. Tafiya kawai take har ta kusa kaiwa apartment ɗin nasu ta hangoshi tsaye suna magana da Hamid, kallo ɗaya ta yi musu har ta ƙaraso inda suke ta ɗan rusuna a sanyaye ta ce“ina yini?” Hamid ne ya amsa, shi kuma ya dinga kallonta ganin zata shige ya ce“Nana zo” runtse idanunta ta yi sai kuma ta dawo ta tsaya kusa da su ta sunkuyar da kanta, Hamid y ce“to ni dai nayi gaba” okay kawai Safwan ya ce sannan ya mai da idanunsa kanta, above 5mins kafin ya ce“jiya wai kin yiwa su Siyama rashin kunya kin zage su?” da mamaki ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“wace Siyama?” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“je ki kawai” tura baki ta yi sannan ta juya ta bar wajen dan daman ba son magana take dashi ɗin ba.

Tana ƙoƙarin shiga parlon su Zahra wayarta ta yi ƙara alamar message ya shigo, ta kalli message ɗin tana kokarin buɗewa sai ga kiran waya ya shigo, tsayawa ta yi sannan ta ɗaga kiran ta kai wayar kunne, kafin ta yi magana ya ce

“Kin ga saƙona?”

Girgiza kanta tayi kamar yana gabanta ta ce

“A'a”

Junaid ya gyaɗa kansa sannan ya ce“okay to ba komai bane sai ina son sanar da ke cewa kisan duk yanda zaki yi kada a ɗaura miki aure da wannan mutumin, dole ne ki ƙi aurensa sannan dole ne ki gabatar dani a wajen iyayenki, ki ce musu ni ki ke so ba wanda suke shirin aura miki ba, idan ki ka yi haka to zan ƙona hotunanki da suke wajena, amma idan har ki ka saɓa abin da nace miki to wallahi sai na fitar dasu kowa ya gani, sannan har gida zan saka a kawowa mahaifinki ya gani, dan haka yanzu shawara ta rage ga mai shiga rijiya, ko dai ki yi abin da nace ko kuma na lalata rayuwarki!”

Jingina ta yi da jikin bango tana sauke numfashi da sauri da sauri, nan da nan hawaye suka ciko idanunta, ya kashe wayarsa ba tare da ya sake cewa komai ba. Kasa kukan ta yi sai ajiyar zuciya da take saukewa, above 5mins kafin ta ja ƙafafunta a hankali ta buɗe parlon ta shiga, Aunty Khadijah ce zaune sai Zahra a kusa da ita suna magana, ta kallesu muryarta na rawa ta ce“ina yini” babu wadda ta amsa a cikinsu dan haka ta haye sama abin ta, Zahra ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta ce“ina zuwa” okay kawai ta ce sannan ta tashi ta bi bayanta, tana shiga ɗakin Zahra ta buɗe ƙofa ta shigo, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“aunty yanzu Junaid ya kirani” babu yabo babu fallasa ta ce“me ya ce miki?” jiki a sanyaye ta faɗa mata duk abin da ya ce mata, Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“zo ki zauna zamu yi magana” ta ƙare maganar tana zama gefen gadon, to kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ita ma ta zauna gefenta. Zahra ta dinga kallonta can kuma ta ce“kin san me nake so dake Nana?” girgiza kai Nana ta yi ba tare da ta ce komai, Zahra ta ci gaba da faɗin

“Ina son ki rabu da auren Safwan, ina son ki ce baki son shi da kanki, idan ta kama ki ɓata da kowa ma ki ɓata amma ina so ki bar maganar aurensa!”

Da wani irin mamaki Nana ta dinga kallon Zahra sai kuma a sanyaye ta ce“Aunty idan na ce haka kowa zai tsaneni, nima bana son auren Yaya Safwan amma babu yanda na iya, ba zan iya cewa a'a ba”

Zahra ta gyaɗa kanta sai kuma ta ce“ba zaki iya ba? To ai dole ki yi Nana, saboda Yar Yayata Siyama nakeson ta auri Safwan, ki cewa Abba bakya son sa ya zaɓa miki wani, amma ba dai Safwan ba!” a razane ta tashi tsaye tana kallonta, ta dinga kallonta tana hawaye kafin ta ce“a'a aunty ki daina min irin wannan wasan, zuciyata bugawa zata yi, ki bari dan Allah” tashi tsaye Zahra ta yi ita ma ta dafa kafaɗarta tana murmushi ta ce“ba zolayarki nake ba Nana, ina faɗa miki ne a matsayin shawara, bana son mu kai jallin da zamu ɓata dake akan wannan dan haka ki rabu da Safwan kin ji” ta ƙare maganar tana jan kumatunta. Janye hannunta Nana ta yi daga fuskarta sai kuma ta girgiza kanta ta ce

“a'a aunty, A'a! Wallahi ba zan iya ba, ba zan taɓa yi ba, zan auri Yaya Safwan muddin ba shi ne ya ce ya fasa aurena ba, ba zan ɗauki wannan shawarar taki ba!”

Zahra ta kalleta sai kuma ta ce“okay wait!" Daga haka ta fice daga ɗakin, Nana na tsaye tana tunanin abin da Zahra ta ce mata har ta dawo hannunta riƙe da envelope ɗin jiya, Nana ta dinga kallonta lokaci ɗaya gabanta ya shiga faɗuwa, zaro hotunan ta yi gaba ɗaya tana bubbuɗesu ta ce

“Idan baki ɗauki shawara ba na san zaki ji barazana, dan haka ki bar maganar auren Safwan muddin baki son waɗannan hotunan naki su fita” da wani irin mamaki Nana ke kallonta sai kuma ta kawo hannunta zata karɓe hotunan, Zahra ta janye hannunta tana murmushi ta ce

“so ki ke na baki hotunan ki? Zan baki Nana, da zarar kin yi abin da nace zan baki hotunanki, amma idan har baki yi yanda na ce ba to ki sani kai tsaye Abba zan kai wa wannan hoton, sannan kuma na bawa uncle ɗin ki wasu, na san ba zaki so hakan ba ko Nana?”

Shiru Nana ta yi dan ta kasa cewa komai banda hawaye babu abin da take, Zahra ta tako har gabanta ta sanya hannunta ta goge mata hawayen tana faɗin “stop crying lil sis, ki zama yarinyar kirki kin ji, babu abin da zai sameki, ni ba zan cutar da ke ba kin ji, kawai do as i said!” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 23...
Chapter 36 · 0% Book details