Sashe 44
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maganar Abba ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, a hankali ta gyaɗa masa kai tana ɗan kallon in da suka tsaya ɗin dan sam bata lura ma da sun daina tafiya ba. Sai da Abba ya fita daga motar sannan ta samu damar sakin wani irin kuka mai ban tausayi, a fili ta dinga faɗin
“wayyo Allahna, na shiga ukuna. Allah ka gani, kaga abin da ke damuna,Allah ka yi min maganinsa, idan ba zan iya da wannan masifar ba Allah ka ɗauki raina na huta, Allah kada ka bari na tozarta iyayena a idanun jama'a. Allah ka dubeni, Allah ka shiga lamarin nan...”
Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya kwace mata, haka ta dinga rerashi har sai da jijiyoyin kanta suka fara tashi, kanta ya yi mata wani irin nauyi, idanunta suka ƙara kumbura. Ganin Abba yana tawowa ya sanya ya tayi saurin goge idanun tana jan numfashi a hankali. Koda ya shigo bai kalleta ba ya yi wa mota key suka bar wajen.
****
Safeena ta dinga kallonta amma bata ce komai ba, Zahra da ke Ƙoƙarin haɗa miya ta sake cewa“kina ji na kin yimin banza, ban son iskanci fa”
Ajiye wuƙar hannunta ta yi tana jingina da jikin cabinet ta ce“ni ban san abin da zance mikin bane Aunty,saboda ban san yaushe ki ka sauya har ki ka fara goyon bayan su Aunty Khadijah ba. Bayan kina da tabbacin abin da suke shirin yi ba dai-dai bane. Ta ya za'a ce sauran sati ɗaya bikinta ku yi yunkurin hanata aurensa? Ba ma wannan ba yanzu ke da kanki ki ka ce kun je ƙauyensu an nuna miki ba'a son ki, sannan kuma har matar tayi iƙirarin sai ya ƙara aure, kuma fa ki ka ce Nana aka ce ya aura.”
Safeena ta yi maganar tana kallonta. Jinjina kai Zahra ta yi jiki a sanyaye ta ce“eh haka ne, amma kuma ai doctor ya faɗa min ba zai aureta ba, kuma na san tun da ya ce haka ba zai taɓa aurenta ba. Sannan kuma ya ce min nan da next week ai ta zama matar aure...” Zahra ta yi shiru tana nazarin abin da tace. Jinjina kai Safeena ta yi kafin ta ce
“you see, kin ji abin da ki ka ce da kan ki, idan har an yi auren nan next week shi ne ki ke da tabbacin ba zata auri Daddyn Noor ba. Amma idan har ki ka dage sai kin hana auren to ki sani kamar kina kirawowa kan ki kishiya ne da kanki, domin wallahi ba zasu fasa aura masa ita ba. Muddin ba'a yi aurenta da waninsa ba!”
Shiru Zahra ta yi tana kallon Safeena fuskarta cike da damuwa, kenan idan har ta matsawa Nana akan kada ta auri Safwan zata dawo ta auri mijinta?
“Impossible! Ba zan taɓa bari ba wallahi, Nana ba zata taɓa auren doctor ba”
Zahra ta ce tana girgiza kanta, Safeena ta dafata cikin sanyin murya ta ce“mu ma ba zamu miki wannan fatan ba Aunty. Amma ki sani domin ki tabbatar da Nana ba ta auri Daddyn Noor ba dole sai kin bari ta auri Safwan, ki janye jikinki daga gurinsu Aunty Khadijah, wallahi! Wallahi Aunty zasu kai ki ne su baro!”
Zahra ta dinga kallon Safeena ba tare da ta ce komai ba, gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, ba zata iya barin Nana ta auri Safwan ba muddin Siyama na son aurensa. Haka kuma ba zata bari Nana ta auri Doctor ba dan ba zata jure zama da ita a matsayin kishiya ba, to idan haka ne mene ne abun yi?
“A lalata rayuwarta, a raba ta da kowa nata, ta yanda zata gudu tabar gidan da kanta. Ta yanda zata zama abar kyama a wajen kowa, walau iyayenta ko kuma dangin gaba ɗaya!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Assalamu alaikum everyone fatan kowa yana lafiya. Kamar yanda ku ka sani I'm Nanameera, CEO NM couture, Muna siyar da kayan sakawa irinsu: Abaya, Gowns, Veils, Bags da dai sauransu, Delivery Nation wide. For more information contact me
08106608363
Nanameera.
Page 28...
Kamar daga sama haka suka ji maganar dan haka suka juya a tare suna kallonta. Aunty Khadijah ce tsaye jikin ƙofa ta harɗe hannayenta a ƙirji, Safeena ta sauke numfashi tana kallon Zahra wadda ita ma take kallonta. A hankali ta shiga takowa har gaban Zahra ta dafata cikin kakkausar murya ta ce
“Idan har ki na gudun kada daga baya ta zo ta auri mijinki to kawai a rabata da gidan, kin ga hakan zai fi mana sauki gaba ɗaya. Siyama ta auri Safwan ba tare da tashin hankali ba.”
Ta ƙare maganar tana ɗan murmushi, Zahra ta dinga kallonta da mamaki can kuma ta janye hannunta daga kafaɗarta tana faɗin “A'a aunty wannan ba shawara ba ce, kuma ni gaskiya ba zan iya saka hannu cikin lalacewar rayuwar Nana ba. Saboda babu abin da ta yi mana, kuma ni ba tsanarta nayi ba, kawai dai zan yi abin da zai sa Siyama ta auri Safwan amma ban da lalata rayuwarta gaskiya.”
Aunty Khadijah ta yi murmushi tana gyara tsaiwarta ta ce“To kenan kin shirya zama da ita a matsayin kishiya?”
Rai a haɗe Zahra ta ce“akan me zata zama kishiyata?”
“Akan zata fasa auren Safwan mana, ko kina tunanin zasu fasa haɗata da mijinki ne?”
Aunty Khadijah ta yi maganar tana kallonta. Shiru Zahra ta yi tana tunani can kuma ta girgiza kanta ta ce“Ni na san doctor ba zai taɓa auren Nana ba, kuma shi ba'a masa dole ma, dan haka kawai zan yi abin da zata rabu da Safwan. Amma fa ki sani Aunty idan har rabuwarta da Safwan na nufin zata auri mijina wallahi sai dai Siyama ta haƙura, ta auri wani a gidan, tun da akwai sauran samari wanda basu aurar ba.”
Safeena dake gefe tun ɗazu ta yi murmushi sai kuma ta ce“Nima dai abin da nagani kenan Aunty, gara Siyama ta haƙura dashi idan yaso ta auri wani”
Wani mugun kallo Aunty Khadijah ta watsa mata wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta, Ta mai da idanunta kan Zahra fuska a haɗe ta ce
“Yanzu ke me ki ke nufi?”
Zahra ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai tana kallon gefe ta ce“ni kawai ina nufin ba zan yi abin da zai zo ya dameni ba, ba kuma zan gyara auren wata na lalata nawa ba!”
Murmushin yaƙe Aunty Khadijah ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Alright kin yi ƙokari, abin da baki ƙarasa ba ni zan ƙarasa shi da kaina”
Daga haka ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata tashi sama. Safeena ta ƙaraso gaban Zahra tana murmushi ta ce“Yauwa Aunty, kin yi dai dai. Ki bar su suje can su ƙarata”
Shiru Zahra ta yi bata ce komai ba, dan gaba ɗaya zuciyarta ba tai mata daɗi ba yanda suka yi da Aunty Khadijah. Sam bata son tana ɓata mata rai, Safeena ta dinga kallonta jin bata ce komai ba yasa ta ce
“Aunty lafiya?”
Sauke numfashi ta yi sannan ta ce“babu komai Safeena, bari na zo na tafi gida kada dare ya yi min” to kawai Safeena ta ce sai kuma ta koma ta ci gaba da abin da take.
Koda Zahra ta fito zaune ta samu Umma da Amal suna magana, kai tsaye sama ta shige ta dauƙo mayafinta da kuma jakarta sannan ta dawo ƙasan. Umma ta dinga kallonta kafin ta ce“tafiya za ki yi?” tana yafa mayafin akanta ta ce“eh Umma dare ya fara yi” Umma ta jinjina kanta ta ce“haka ne, ki gaida mutan gidan”
“Zasu ji in sha Allah Umma”
Ta ce tana ɗaukan wayarta da ke kan kujera. Amal ta kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“ki gaida gida”
“Zai ji”
Zahra ta amsa tana yin waje cikin hanzari.
****
Kaddu ta dinga kallon Aunty Khadijah sai kuma ta ce“to yanzu mene ne abun yi?” tsaki Aunty Khadijah ta yi rai ɓace ta ce“to nima ina na sani, kawai ya cuceni a banza gashi gaba ɗaya asirin nema yake ya saketa” girgiza kai Kaddu ta yi ta tashi daga zaunen da take ta shige bedroom ɗinta. After 5mins ta fito hannunta riƙe da mayafi tana ƙoƙarin yafawa ta ce“tashi mu je kiga”
“Ina zamu je?”
Aunty Khadijah ta tambaya tana kallonta.
“wajensa mana, komawa zamu yi ya faɗa mana yanda ya kamata a yi”
Okay kawai ta ce sannan ta dauki wayarta da jakarta suka fita.
****
Tun da ta shigo gidan take kallon motocin da suka yawaita fiyeda da, ta dinga mamaki wadanda suka zo da yawa har haka. A compound ɗin apartment ɗin su ta yi parking sannan ta sakko ta nufi cikin gidanta kai tsaye. Bata samu kowa a ciki ba dan haka ta haye sama ta shige daƙinta ta zauna tana sauke gajiya.
A can Apartment ɗin Hajiya Babba, Atta ce zaune ta hakimce kan sofa two seater tana sauraren maganar da Abba ke faɗa mata, Har ya kai ƙarshen maganar babu wanda ya ce komai ba, sai jinjina kai take kamar gaske. Sai da taji ya yi shiru sannan ta ce
“To yanzu me ku ke nufi?”
Abba ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta haɗe rai ya ce“Ai kin ga Atta kamar a bar wannan maganar ko? Tun da an riga da an gama komai na aure bai kamata a sauya ba”
Taɓe baki ta yi kafin ta ce“wato dai nufi ake ba zai aureta ba?”
Abba ya girgiza kansa ya ce“ba haka ake nufi ba Atta. Da ace ba'a fara maganar aurensu da Safwan ba sai a bari ya aureta, amma tun da har an fara magana kuma yau sauran kwanaki 4 a ɗaura auren kin ga kamar zai zama fitina abun” Atta ta yi shiru ba ta ce komai ba dan tana matuƙar ganin girman Abba, ko Papa da yake gaba dashi bata fiye yarda da zancensa ba kamar na Abba. Jin bata ce komai ba ya sanya Abba ya sauke ajiyar zuciya dan ya san ta haƙura, Above 2mins kafin ta ce