← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 125

Sashe 76

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun zauna Aunty Khadijah ta ce“yauwa me ki ke cewa jiya a waya?” girgiza kai Siyama ta yi cike da damuwa ta ce“Mom wallahi ba Safwan ne wanda ya kamata mu rike a matsayin target ba. Mijin Anty Zahra shi ne wanda ya dace da buƙatar mu. Kin san kuwa tarin dukiyarsa? Kin san da Safwan yana bani ɗan labarin wasu daga cikin abin da ya mallaka sai da naji kaina ya yi min nauyi?. Idan fa kina neman babban mai kuɗi wanda ya amsa sunansa mai kuɗi, mai faɗa a ji to wallahi Abdusammad ne! Sam bamu yi dabara ba.”

Aunty Khadijah ta yi shiru na wasu sakwanni kafin ta sauke numfashi ta ce“To daman shi Safwan ɗin bashi da komai?” Siyama ta ce“ba wai bashi da komai ba. Yana da shi mana, Yana da arziki sosai shima, amma ba kamar wancan ba, duk fa a ƙarƙashin sa suke, kusan duk arzikin gidan nan ɗin nasa ne” Jinjina kai Anty Khadijah ta yi cike da mamaki ta ce“ikon Allah, ban ɗauka ya kai haka ba.”

“Ai wallahi Mom ya kai har ma ya wuce. Shiyasa fa kowa yake ganin girmansa a gidan nan, Ba zaki taɓa jin ya yi magana an musa masa ba. Kowa girmama shi yake har manya”

Anty Khadijah ta ce“To yanzu ke ya ake ciki dake? Babu wani labari? Ya kamata a ce kin samu ko ciki ne Siyama” Ɗauke kanta ta yi cike da takaici ta ce“Hmmm to Mom mene ne bana yi? Wallahi duk abin da muka shirya a gida babu wanda bana aiwatarwa, amma kin ganni ko sauyi ban ji a jikina ba. Kuma kin san me? Duk sauran da aka kai mu tare sun samu ciki, ina ga wannan Amran ce kawai bata samu ciki ba. Ni kaina abun sai ɗaure mun kai yake” Anty Khadijah da duk jikinta ya yi sanyi ta ce“Tab idan haka ne zama bai kamani ba. Dole na tashi tsaye, Gashi daman maganar babanki na nema ta dawo sabuwa, naji yan uwan babanki na ƙishin-ƙishin ɗin kai ni koto”

Zaro idanu Siyama ta yi sai kuma ta ce“to kuma yanzu me ki ka musu Mom?” taɓe baki Anty Khadijah ta yi ta ce“kema kya faɗa, babu abin da na musu. Shi kansa kuɗin da suke magana babu sun ƙare, Yanzu ban da gidan nan na wajenki bani da komai, ni dama yana rayen ya ci gaba da nemo mana. Amma dai nan kusa zan yi aure”

“Aure kuma Mom? Da girmanki?”

Siyama ta yi maganar a sanyaye. Wani banzan kallo Anty Khadijah ta watsa mata sannan ta ce“Ji min banzar ƴa? Har yaushe nayi girman da zan kasa aure? Akwai wani Alhaji dana samu yana da tarin dukiya nan bada jimawa ba zan aureshi, kin ga idan har mun samu yanda muke so ai babu buƙatar mu ci gaba da wannan abun, sai kawai ki kashe auren naki ki fito.”

Siyama ta girgiza kanta ta ce“a'a Mom ni ba zan kashe auren nan ba wallahi. Saboda ina sonsa har ga Allah.” Ta ƙare maganar tana harɗe hannayenta a ƙirji, Taɓe baki Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“to ai sai ki yi ta yi. Ni bari ki ga na tashi na tafi kar a zo a ganni a nan”

“Ba zaki je wajen Anty Zahra ba?”

Girgiza kai ta yi ta ce“ke bar ni da wannan shashashar, ko naje ɓata min rai zata yi a banza. Kin san ita yanzu duk Umma ta kuma canzata, ganin bukatata ta biya ya sa ban sake bi ta kanta ba.”

Siyama ta miƙe tana kallon ta ta ce“Allah sarki, wallahi tausayi take bani Mom. Kin san wannan Nanar ba mutunci gareta ba” Shiru ta yi tana tunani can kuma ta ce“to Allah ya rufa asiri, Ni babu ruwana. Daga nan ma gidan Kaddu na nufa”

“To muje na raka ki Mom” har ta yi gaba sai kuma taja ta tsaya, Siyama ta kalleta ta ce“mene ne Mom?”

“Babu wasu yan kudi a wajenki ne ki ban?”

Girgiza kai Siyama ta yi ta ce“wallahi bani da cash, amma zan miki transfer ɗazu Safwan ya bani nima.”

Jinjina kai Anty Khadijah ta yi ta ce“yauwa ai hakan yana da kyau. Ni har cash ɗin ma ki dinga amshewa, sanda muke tare da mahaifinki bai isa ya shigo da kuɗi ba sai na ɗauke ko ya bani ko bai bani ba. A haka na tara duk abin da ki ka ga na mallaka.”

Shiru Siyama ta yi jiki a sanyaye ta ce“Tom Mom.”

Anty Khadijah ta yi gaba Ita kuma ta ci gaba da bin ta a baya. Har compound ɗin su ta rakota, sai da ta shige motarta sannan ita ma ta juya ta koma ciki.

Ƙarfe 10:20 na safe ta sakko daga saman, Sanye take da wasu riga da skirt, rigar irin mai kama jikin nan, sai skirt ɗin na jeans mai ɗan kauri. Wata hula ce mai ado akanta, blue colour wadda ta yi matching da skirt ɗin. Ta yi simple make-up a fuskarta dan haka ta ƙara mata kyau. Bakin nan sai shining yake na lip gloss, kasancewar bakin nata pink colour mai ɗan zagaye kamar na liner ya sanya ta yi wani irin mugun kyau. Tun da ta sakko Zahra ke bin ta da kallo, Ita kuwa ko lura bata yi da ita ba ta nufi kitchen tana waƙar Alan walker ta Unity. Zahra dake kan kujera tana danna wayarta ta sauke numfashi, kalle-kalle Nana ta dinga yi a kitchen ɗin, ita ba wani iya girki ta yi ba dan ba yi take ba. Dan haka ta rasa abin da zata dafa ta ci, gashi yunwa take ji, haka ta ƙaraci kalle-kallenta a kitchen ɗin ta juya ta fito, Bata samu Zahra a wajen ba, dan haka ta nufi sama da sauri, master bedroom ɗin sa ta murɗa ta ji a rufe. Taja ta tsaya tana knocking a hankali, tafi minti biyar tsaye a wajen amma babu alamar za'a buɗe, kuma tasan yana ci dan yau saturday ne ba fita yake ba. Gajiya ta yi da tsaiwarsa ta juya ta bar wajen, tana ƙoƙarin shiga daƙinta ta ji kamar amon muryarsa, dan haka ta nufi ƙofar da sauri, ɗan kasa kunnenta ta yi ta ji da gaske muryarsa ne, dan haka ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige kai tsaye. Zaune ta sameshi kan gadon, Zahra na tsaye jikin mirror tana masa magana tana murmushi. Buɗe ƙofar ɗakin da ta yi ya sanya su kallon ƙofar a tare, Tsaye take kusa da ƙofa, ta kafesu da idanunta fuskarta a ɗaure. Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce

“Nana mene ne haka?”

Tura baki ta yi tana kare masa kallo, wata riga ce armless a jikinsa coffee colour mai zanen tiger a jiki. Gaba ɗaya surarsa ta bayyana, Tatoo ɗin dake gefen hannunsa na hagu ya fito raɗau, gargarsa kuma ta kwanta luf a farar fatar tasa. Ganin bata ce komai ya sanya ya sake cewa

“Mene na ce miki?”

Ɗauke idanun ta ta yi ta kalli Zahra da ke kallonta ita ma, sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin ta buga musu ƙofar. Baki a buɗe ya dinga kallon wajen, Zahra kuwa ta ɗauke kanta tana sauke numfashi, Ya sauka daga kan gadon ya zura ƙafafunsa cikin Gucci slippers ɗin da ke gefen gadon masu taushi, Ya zura hannayensa cikin aljihun 3-quater dake jikinsa sannan ya yi waje. Zahra ta bi shi da idanu sai kuma ta koma gefen gadon nata ta zauna.

A fusace ya tura ƙofar ɗakin, Ya sameta zaune gefen gado ta rufe fuskarta da hannunta sai kuka take a hankali, Karasowa ciki ya yi yana watsa mata wani mugun kallo ya ce

“And what is this? Baki da hankali ne ko me? Are you out of ur sense da zaki shigo mana ɗaki babu ko sallama ballantana ki yi alerting ɗin mu?.”

Ya ƙare maganar a zafafe, Shiru Nana ta yi masa dan ba zaka taɓa ɗauka da ita yake ba, Ya yi kwafa sannan ya sake cewa

“Na fuskanci sai na fara gyara miki zamanki a cikin gidan nan. Kina da buƙatar lesson”

Buɗe fuskarta ta yi wadda ta yi caɓa-caɓa da hawaye da majina ta ce“To ni ka sakeni mana, kawai ka sakeni, wallahi ba zan ci gaba da zama a haka ba. Tun ɗazu nake ta knocking a ɗakin ka ashe baka nan, kuma sai kaje wajenta” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Da mamaki ya dinga kallon ta, can kuma ya sunkuya daidai tsayinta ya sanya hannunsa ya ɗago kanta ya ce

“Ban ji ba sake faɗa.”

Ɗauke fuskarta ta yi ta mike tsaye bayan ta goge hawayenta ta ƙarasa press ɗinta, wata yar ƙaramar trolley ta janyo ta buɗe sannan ta fara kaso kayanta ta fara zubawa ciki tana yi tana tsayawa share hawaye. Abdusammad kuwa tsayawa ya yi a wajen kamar gunki yana kallonta, Sai da ta cikata da kaya sannan ta mayar da rufe dakyar ta ɗagata ta fito da hannunta ta fara ja tana ƙoƙarin fita daga ɗakin.

A gabanta ta gansa yana watsa mata wani mugun kallo wanda ya sanyata sunkuyar da kanta tana ci gaba da hawayenta. Ya fizge trolley ɗin daga hannunta rai ɓace ya ce“Ina zaki je kenan?” a fusace ita ma ta ce“gidan mu mana, wallahi sai na tafi gida..Ni ba zan zauna kana zuwa wajenta ba, Allah tafiyata zan yi, ai daman ban ce ina sonka ba!”

Shiru ya yi yana son fahimtar abin da take nufi, Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce“Saboda naje wajen Zahra shi ne zaki tafi? Idan ban je wajenta ba gurin wa zan je?.”

Ya ƙare maganar yana harɗe hannayensa a ƙirji, Cikin kuka ta ce“to nima ba matarka bace? Ai haka Abba ya ce min, kuma shi ne ka ke zuwa wajenta a haka?” Ta ƙare maganar tana nuna masa jikinsa, Kallon jikinsa ya yi da ɗan mamaki sai kuma ya kalleta ya ce“to me shigar jikina ta yi Nana?”

“To ni dan Allah zan iya zama a haka ne? Kuma ita ma sai ta saka riga yar ƙarama!"
Chapter 76 · 0% Book details