← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 125

Sashe 2

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin wani katon duplex ya yi parking, suka sauka daga motar da gudu kowanne ya nufi apartment ɗinsu, sai da suka gama sauka sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar amma ga mamakinta sai ta ji shi a rufe, ta juyo ta ɗan kalleshi taga danna wayarsa yake hankali kwance, muryarta na rawa ta ce"ka buɗe min zan tafi gurin Amma" shiru ya yi mata, ta dinga kallonsa kafin ta sake cewa"Yaya Sultan ka buɗe min zan sauka" ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleta, idanunta sun cika taf da hawaye ya ajiye wayar ya gyara zamansa yana kallonta ya ce" me ki ka ce ɗazun? Ba zaki zauna kusa da namiji ba" ɗauke kanta ta yi ta dinga kallon compound ɗin gidan wanda ya cika da shuke-shuke. Hannunsa ya sanya ya jawota ta juyo da sauri tana kallonsa, tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta ta ce"dan Allah Yaya ka bar ni, ka rabu dani na tafi" hannunta ya kama duk biyun ya riƙe cikin nasa still looking at her ya ce"Nana ni ki ke sharewa ko? Baki sona ko? Ni Yayanki dan nace ina sonki shikenan ki ka daina zuwa inda nake ko, ki ke gudana ko?" Fashewa ta yi da kuka ta shiga girgiza kanta tana cewa"Ni Yaya ka barni na tafi, ka barni naje naga Amma"

Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen sannan ya ɗan hura mata iska a fuska, lumshe idanunta ta yi saboda ƙamshin mouth listener ɗin daya daki hancinta. Ya ɗago fuskarta yana kallonta sosai ya ce"kin san yanda nake sonki kuwa Nana? Ina son ki amince na aureki kin ji, zan je na faɗa Hajiya Babba nasan ba zata ƙi ba Nana, na aureki muyi rayuwarmu cikin farin ciki, kinji cutie ɗita"

Kallonsa ta dinga yi can kuma ta janye hannayenta daga nasa, ta juya tana kallon waje ta ce"ka buɗe min mota na fita" yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗan kalleta, ya sauke numfashi sannan ya yi unlocking motar. Da sauri ta buɗe ta fice ko takan jakarta bata bi ba, ta nufi hanyar apartment ɗinsu da gudu. Sultan yabi bayanta da kallo yana jin wani irin so da ƙaunar yarinyar a cikin ransa.

Yana shirin sauka daga motar idanunsa ya sauka akan wani yanki, ɗauka ya yi ya dinga juyashi kafin ya warware a hankali

“Karki manta dani, ina sonki Nana! Ina son ki! Sannan ina muradin na aureki, dake zan ƙare rayuwata, ki jirani! Wait for me NAANAH!”

08106608363
Nanameera.*🌹NAANAH🌹*

Page 2...

Sultan yaja dogon numfashi ya sauke har sannan idanunsa na zube kan yankin, ya karanta rubutun yafi sau biyar kafin ya linke ya ajiye gefe, ya sauka daga motar kai tsaye kuma apartment ɗin su ya nufa. Knocking ƙofar ta dinga yi kamar zararriya tana kiran "Amma! Amma!" Kusan mintuna biyu kafin azo a buɗe ƙofar, wata farar mace ce fuskarta ɗauke da mabayyanin murmushi take kallonta, ihu ta saki sannan ta rungumeta tana wata irin dariya. Amma tayi murmushi ta ɗagota tana kallonta ta ce" Yaushe zaki girma Nana?" Langwaɓar da kai ta yi ta sake rungumeta tana cewa"nayi missing naki ne fa Ammata" girgiza kai kawai Amma ta yi ta janyenta daga jikinta ta yi ta ce"to shigo ciki" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta nufi cikin parlon da sauri. Tamkar wadda ta warke daga ciwon makanta haka ta dinga bin ƙaton parlon nasu wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa. Ta lumshe idanunta saboda ƙamshin turaren wutar daya game ɗakin mai matukar daɗi, daman in dai ana maganar tsafta da ƙamshi to Amma ƙarshe ce.

"Idan kin gama kallon sai ki shiga ciki ki yi wanka ki zo ki ci abinci"

Amma ta ƙare maganar hannunta riƙe da remote tana rage gudun ac. Kallonta Nana ta yi ta ce"Amma me ki ka dafa?" Ganin irin kallon da ta yi mata ya sanya bata sake cewa komai ba, ta nufi hanyar ɗakinta. A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin nata, ta dinga taka fluffy rug ɗin dake shimfide akan tiles, sanyin ac da kuma turaren wuta ya daki hancinta, ta sauke ajiyar zuciya. Ɗakin nata neat and organized, royal bed ɗinta madaidaici a tsakiyar ɗakin mai shimfiɗe da farin bedsheet,sai katon teddy bear a gefe. Daga can kusurwar ɗakin a saman study table an jera littattafai na makaranta,da yar ƙaramar fitilar karatu a gefensu. Ko ina tsaf yake tamkar tana rayuwa a ciki, duk da bata nan hakan baya hana Amma gyara mata shi kullum. Ta ƙarasa ta zauna gefen gadon ta jingina da jikin fuskar gadon ta ja idanunta ta rufe tana jin wata irin nutsuwa na saukar mata. Kasancewar ta gaji sosai ga kuma yanayi mai daɗi data samu ya sanya bacci ya ɗauketa a wajen.

Iska ta dinga kaɗawa a hankali, yanayin sanyin da ake ciki ya sanya taji ta takura, ta haɗe jikinta waje ɗaya. Kallonta ya dinga yi kamar ya samu tv, ganin ɗalibai na sauri ya sanya ta ɗago narkakkun idanunta ta kalleshi, murmushi taga ya yi, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Gyara tsaiwarsa ya yi still looking at her ya ce"Kin gaji?" Ta girgiza kanta, kallon right hand side ɗinsa ya yi ya hango Senior master dan haka ya maida idanunsa kanta ya ce"yanzu zaku tafi?" Nan ma ta girgiza masa kai, ɗan haɗe rai ya yi kamar tana ganinsa ya ce"hala kina fama da ciwon baki ne?" Da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce"sai an zo ɗaukarmu" Sir Junaid ya sauke numfashi sannan ya ce"yanzu idan ki ka je gida a ina zan dinga ganinki? Zaki dinga fitowa mu haɗu? Ko ni zan dinga zuwa estate ɗinku?"

Ji ta yi gabanta ya yi wani irin faɗuwa, ta kalleshi hawaye kwance cikin idanunta ta ce"i wish so, amma ba zai taɓa yiwuwa ba, ba za'a bar ni na fito ba idan har na koma gida. Bama fita, duk abin da muke so sai dai a kawo mana, idan kaga mun fita waje to sai dai da yayyenmu maza ko kuma uncles ɗinmu and..."

"And what?" Junaid ya yi saurin tambayarta.

"Ba za'a bari ka zo gidanmu ba, ba zan sake ganinka ba idan har na shiga cikin M-Shuwa estate!"

Nana ta ƙare maganar cikin rauni. Ya dinga kallonta bai ce komai ba, ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan, Junaid ya numfasa sannan ya ce"kenan me ki ke nufi Nana? Na rabu da ke? Na rabu da soyyayar da nake miki tsayin shekaru shida? Na bari ki auri ɗan danginku? Na haƙura dake! Kin yimin adalci kenan?"

Ta girgiza kanta hawaye na zubowa kan farar fuskarta ta ce"Ya zamu yi haka ƙaddara ta zaɓa mana, ban isa na bijirewa gidanmu ba, ban isa na sauya abin da suka ginu akai ba! Ban isa..."

"Ki min shiru Nana! Kimin shiru! Just keep quiet!"

Junaid ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa, shiru ta yi ta kafeshi da manyan idanunta. Ya dinga huci kamar zaki kafin ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce"Ba zan bar ki ba, sai na tabbatar dana sameki a matsayin mata, wallahi tallahi Nana ba zan bari a rabani dake ba! Ina sonki! Ina sonki! Ina sonki Nana!"

A firgice ta buɗe idanunta, ta dinga kallon ɗakin tana zare idanu, hannunta ta sanya ta dafe ƙirjinta jin yanda yake wani irin bugu. Amma dake tsaye kusa da press tana linke wasu kaya data shigo dasu ta ce"lafiya?" Ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce"babu komai" Amma ta ɗan juyo ta kalleta sai kuma ta ce"tashi kiyi wanka, ki zo parlon ina jiranki" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet tana tafe kamar babu laka a jikinta. Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta ta mayar da press ɗin ta rufe sannan ta fice daga ɗakin.

After 20mins ta fito daga toilet ɗin jikinta na ɗigar ruwa, ta ƙarasa gaban mirror ɗinta tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta. Ta ƙurawa kanta kallo a jikin mirror ɗin, Nana fara ce tas kuma asalin bafulatanar yarinya, tana da kyau mai sanyi da ɗaukar hankali, hancinta dogo har bakinta, idanunta manya manyan kamar zasu yi magana, bakinta ɗan ƙarami kuma jajur dashi, gashin girarta a cuccure kuma mai yawa, haka ma gashin idonta zara-zara. Babu yanda za'a yi ka yi mata kallo ɗaya ka ɗauke idanunka, wannan shi ne sirrin duk wata budurwa a cikin dangin Shuwa, Allah ya yi musu kyau daga mazan su har matan.

Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta atampa ɗinkin A-shape, ta ɗaura ɗankwalin sannan ta shafa lip gloss a bakinta, she looks so quiet, ta kalli fuskarta a madubi a fili ta ce"nayi kyau sosai" ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta fice daga ɗakin da sauri. A parlon ta samu Amma zaune tana karanta wani littafi, Ta ƙarasa ta zauna kusada ita, ta ɗora kanta a gefen kafaɗarta a shagwaɓe ta ce"Ammata nagaji sosai" ba tare da ta kalleta ba Amma ta ce"ɗagani ki ci abinci sai ki huta" ɗago kanta ta yi tana kallon Amma ta ce"Ba hutawa zan yi ba wajen Hajiya Babba zan je" kallonta kawai Amma ta yi babu yabo babu fallasa ta ce"i see" sannan ta miƙe ta nufi kitchen.

Ko rabi bata ci ba a abincin plate ɗin ta miƙe duk yanda ta yi missing girkin Amman kuwa, ta miƙe tana riƙe da robar exotic tana sipping, ganin tana shirin yin waje ya sanya Amma ta ce"haka zaki fita babu ko mayafi?" tsayawa ta yi tana kallonta ta ce"Amma wajen Hajiya fa zan je, yanzu zan dawo" daga haka ta yi waje da sauri, Amma ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kai ta ci gaba da abin da take.
Chapter 2 · 0% Book details