Sashe 101
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta bata amsa kai tsaye. Okay kawai ta ce sannan ta mai da ƙofar ta rufe, Ta koma ta ɗauki hularta akan gadon ta zura slippers a ƙafafunta sannan ta fito daga ɗakin.
Da mamaki ta dinga kallon ƙasan, ganin duhu ya mamaye ko ina, Ta ɗan yi jim a bakin stairs ɗin benan, kafin a hankali ta fara takawa. Sai da ta sauka kasan sanan ta tsaya cak saboda bata ganin gabanta, Ta ɗan waro idanunta saboda inuwar mutum data gani. Muryarta na rawa ta ce
“wa... waye?”
Shiru ba'a yi magana ba, Ta sake cewa waye amma ba'a bata amsa ba. Shiru Nana ta yi tana kallon wajen ta cikin duhun, Lokaci ɗaya ta ga haske ya mamaye parlourn, Sai a sannan ta fara ƙarewa parlon kallo. An ƙawata shi da baloons gwanin ban sha'awa, Kafin ta yi magana taji spray na zubowa kanta, ta ɗaga idanunta tana kallon saman amma bata ga kowa ba. Murmushi ta fara yi tana kallon yanda baloons ɗin ke fashewa, Ta sauke idanun ta tana kallon jikin bangon parlourn. Wani ƙaton enlargement ɗin hoton ta ne na ranar da aka haifeta a kafe, Sai kuma wasu hotunan na sanda tana ƴar ƙarama Abdusammad ya ɗauketa, wasu tana kuka, wasu kuma tana masa dariya, Daga saman su kuma an saka "Happy birthday Naanah!"ƙasa kuma an ajiye number 1&8 wanda ya yi making 18yrs. Nana ta dinga kallon su tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta, Lokaci ɗaya ta kalli inda yake tsaye yana kallon ta sai murmushi yake, Sanye yake da suit black colour wanda suka amshi jikinsa kai ba ka ce ya taɓa raɓar ƙasar Hausa ba. Fuskarsa a sake sai murmushi yake, Da gudu ta ƙarasa inda yake tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana sakin wani irin kuka. Ya dinga dariya yana shafa kanta jin yanda take kuka tana sake ƙanƙameshi, Ɗago fuskarta ya yi yana murmushi ya ce
“Happy birthday ƴar rigimar uncle!”
Ta kalle shi sai kuma ta sake mai da kanta ƙirjinsa tana ci gaba da kuka. Sake ɗago kan nata ya yi ya ce“Mene kuma abin kuka? Or are you not happy? Uncle ya shirya miki birthday party”
Girgiza kanta ta yi tana kuka mai haɗe da dariya, ta ce“No uncle. Kawai...kawai...” ta kasa ci gaba saboda kukan daya sake kwace mata, Mai data ƙirjinsa ya yi ya rungume ya ce“Shikenan ya isa haka.”
Ta dinga gyaɗa masa kai ba tare da ta daina kukan ba, Noor ce ta sakko daga sama ta ƙaraso wajen ta rungumeta ta ce
“Happy birthday Anty Nana!”
Sai a sannan Nana ta sake shi ta durƙusa ta ɗauketa tana murmushi ta ce“thank you Noorie.”
Murmushi duka suka yi, Ya kalle su ya ce“to a yanka cake ɗin ko? Dare nayi” Sauka daga jikinta Noor ta yi ta ce“Abbie bari na kira Ummi” Girgiza mata kai ya yi ya ce“na kirata yanzu zaki ganta.” Ko rufe baki bai yi ba Zahra ta ƙaraso wajen tana sanye cikin wata Abaya green dark ta ɗaura veil ɗin akanta. Noor ta tafi wajenta da sauri ta rungumeta ta ce“Ummi daman kiran ki zan yi, Ki zo mu yanka cake.” Murmushi Zahra ta yi ta ja kumatunta ta ce“to gani nan.” Noor ta bar wajen ta koma wajen Nana ta tsaya, Inda aka ajiye manyan cakes ɗin suka ƙarasa, Cake ne yafi kala biyar manya wasu da hotunanta a jiki wasu kuma da stickers. Abdusammad ne ya miƙa mata wuƙar yana murmushi ya ce“oyaaa” ta amsa tana kallon sa, A hankali waƙar Birthday ta fara tashi sauran maids ɗin gidan suna ta tafi, a haka Nana ta yanka cake ɗin. Koda ta ciro Abdusammad ɗin ta miƙowa, Ya ɗan ware idanunsa sai kuma ya buɗe bakin. A hankali ta saka masa, Suka sake tafi Noor sai dariya take tana tafi abin ta, Zahra kuwa kasa tafin ta yi dan ji take kamar ƙafafunta na neman kasa ɗaukanta, Danne zuciyarta kawai take yi. Shima ya yanko cake ɗin ya bata ta amsa tana murmushi sannan ta bawa Noor, Da kansa ya ƙarasa inda Zahra ke tsaye hannunsa riƙe da cake ɗin ya ce
“Haaa.”
Babu musu ta buɗe bakin ya saka mata, Ta fara taunawa tana murmushin da bai kai zuci ba. Bayan sun gama yanke-yanke cake ɗin aka fara bata gift, Noor ce ta fara bata wasu manyan chocolate a cikin kwali tana murmushi, Nana ta amsa sannan ta rungumeta ta ce“Thank you Noor, Allah ya miki albarka.” Dariya ta dinga yi, Zahra ma ta ƙaraso wajen ta miƙo mata wata ƙatuwar jaka mai rubutun Happy birthday a jiki, amsa Nana ta yi tana murmushi ta ce“Thank you Anty zahra.” Karo na farko data kira sunanta da girmamawa tun bayan abin da ya faru, Zahra ta ɗan yi murmushi without saying anything. Juyawa ta yi tana kallon Abdusammad dake tsaye ganin bashi da niyyar bata waya gift yasa ta taɓo shi, Yana murmushi ya ce
“mene ne?”
“Gift ɗina”
Ta ce a shagwaɓe.
“au nima sai na bayar?” ya yi tambayar yana nuna kansa, Tura baki ta yi tana shirin barin wajen taji ya riƙo hannunta, Ya ƙarasa da ita har gaban wata sofa wannan aka rufe da farin veil. Da kansa ya janye veil ɗin yana murmushi ya ce
“Happy birthday once again Nana.”
Kallon sa ta yi sai kuma ta kalli tarin kayan dake kan kujerar, Ta durƙusa a wajen da sauri ta shiga ɗaga su. Teddies ne irin wanda take so manya, Sai kayan zaƙi da yawa, Ta dinga bubbuɗawa tana murmushi. Wata ƙatuwar teddy red colour ta ɗauka ta miƙe tsaye tana kallon sa fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce
“Thank you Unclena... Ina sonka!”
Ta ƙare maganar tana faɗawa jikinsa, Murmushi ya yi kawai ya ce“da gaske kina sona Nana?” Gyaɗa masa kai ta yi, Ya ɗagota ya ce“tsohon?” wata irin matsananciyar kunya ce ta rufeta. Ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ce komai ba, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya shi jan kumatunta ya ce
“Kee relax, I'm just kidding.!”
Hannunta ta sanya ta share hawayenta, Ya taɓe baki sannan ya kama hannunta yana cewa“Allah ya miki sauki.” Bata ce komai ba suka koma inda su Zahra ke tsaye, Ya kalle su ya ce“muje.” To kawai suka ce sannan ya yi gaba yana rike da hannun Nana suka bi bayansa, A babban compound ɗin gidan suka tsaya, Nana ta dinga kallon motar dake gabansu wadda aka rufe da baƙin yadi. Da idanu ya yi musu alama da su buɗe, Wasu maids guda biyu suka ƙaraso wajen suka janye yadin daya rufe motar. Wata Lamborghini Aventador ce White colour, an yi mata ado da red bow wanda suka sake haskata. Nana ta dinga kallon motar babu ko kiftawa, bata san sanda ya zagaya hannunsa a jikinta ba, Kawai kallon Hannunsa ta dinga yi wanda ke riƙe da car key. Ya miƙo mata yana murmushi can gefen kunnenta ya ce
“And this na virgin gift. Allah ya miki albarka Nanata. Kin sani farin ciki mara misaltuwa, naji daɗi. Na samu nutsuwa, Thank you, na gode da ki ka kare mutuncinki har zuwa ɗakin mijin ki. Allah ya miki albarka kin ji!”
Wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, ta kasa koda motsi sai hawaye shar dake zubowa kan kyakkyawar fuskarta. Above 2mins kafin ta saki wani irin raunataccen kuka ta juya ta shige jikinsa tana kuka kamar ranta zai fita, Shiru Abdusammad ya yi ya ɗora hannunsa a bayanta yana ɗan bubbugawa a hankali, ganin bata da niyyar yin shiru yasa ya kai bakinsa kunnenta ya ce
“Ko baki so ne?”
Saurin girgiza masa kai ta yi, Ta ɗago tana kuka ta kalle shi ta ce
“Thank You... Thank you Uncle, Na gode sosai, na gode uncle. Ina sonka Uncle, ina son ka sosai, na fi kowa sonka wallahi. Ina son ka uncle ɗina...”
Caraf taji ya kame bakin maganar, ya fara kissing ɗinta a hankali in a different romantic ways. Karo na farko data fara mai da masa da martanin abin da yake mata, Hakan ya sanya shi sake chopping face ɗin su yana ci gaba da abin da yake... Ƙarar fashewar abin da suka ji shi ne ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi, Ya janye bakinsa daga nata a hankali yana sakin numfashinta. A tare suka kalli inda suke jin ƙarar, Abdusammad ya ware idanunsa yana kallon ta da mugun mamaki...
08106608363
Nanameera.
*🌹 NAANAH 🌹*
Arewapen@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 60.
Zahra ce tsaye gaban motar ta tawarwatsa glass ɗinta, Hannunta duk jini sai kuka take. Sakin Nana ya yi da sauri ya ƙarasa wajen ya finciko hannunta ganin tana ƙoƙarin sake buga flower base ɗin, Fizge hannunta ta yi cikin kuka kamar wata zararriya ta ce
“Ni ka rabu dani! Ka kyaleni, na rantse da Allah ba zan yarda ba!.”
Abdusammad ya dinga kallonta da mamaki, Nana ta ƙaraso wajen tana kallon yanda Zahra ta ci mutuncin sabuwar motar tata, Wani ihu ta saki ta yi kanta ta shaƙe mata wuya. Zahra ta fara ƙoƙarin dukanta, Kasancewar ba ƙarfin su ɗaya ba ya sanya ta murɗe mata hannu ta kifa mata mari. Bata ɗauke hannunta ba taji an sauke mata wasu tagwayen maruka akan fuskar, Ya fizge Nana yana kallon ta rai ɓace. Ɗago kanta ta yi tana kallon sa hannunta dafe akan kuncinta. Ta dinga gyaɗa kai kafin ta ce
“Doctor saboda wannan yarinyar ka mareni? Saboda wannan ƴar iskar ka mareni? Akan ta?”
Wani banzan kallo ya dinga watsa mata, Ya juya ya kalli Nana dake tsaye kusa da shi tana kuka a hankali, Bai ce komai ba ya ja hannunta suka nufi cikin gidan. Zahra ta bisu da kallo ganin ya mayar ta mahaukaciya ya yi tafiyarsa, Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan ta sake ɗaukan flower base ɗin ta ci gaba da dukan glass ɗin motar yana fashewa. Dan kanta ta gaji ta sulale a ƙasa tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. Sai da ya kai ta har Apartment ɗinta sannan ya kulle ya dawo ƙasan. Noor dake tsaye tana kuka ya ɗauka, ta yi saurin rungumeshi tana faɗin
“Abbie Ummina”