← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 125

Sashe 1

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*🌹NAANAH🌹*

Repost

https://chat.whatsapp.com/Hbf1rpqVyiZCko3JyHNMcG?mode=ems_copy_c

Page 1..

AUN Academy, Yola.
1:25pm

Ranar ta kasance ta musamman, rana ce da kowacce daliba yar SS3 ke jira tun farkon shekara wato graduation day. Harabar makarantar ta cika da hayaniya, kiɗa-kiɗe da iface -iface sai tashi yake ta ko’ina. Girls ɗin boarding school ɗin suna ta zagaye da juna, wasu suna ɗaukar pictures da wayoyinsu, wasu kuma suna rubuce-rubuce a jikin graduation gown: “Don’t forget me please,” “Call me when you get home.”

A cikin dormitory kuwa, akwati da jakunkuna sun cika ko’ina. Wasu na ta nannade kayan da ba su riga sun shirya ba, wasu kuma suna jiran iyayensu su zo ɗaukarsu.Kowacce yarinya idan ka kalli fuskarta zaka ga farin ciki mara misaltuwa.

A bakin wani hostel suke tsaye, Yan' mata guda uku, farare masu kama da juna, suna sanye da rigunan graduation suna magana da juna. Da gudu ta ƙaraso wajen tana jan trolley ɗin hannunta, ta tsaya gabansu tana haki.

“Kin gama packing komai?”

Ɗaya daga cikin yan matan ta tambayeta, gyaɗa mata kai ta yi tana goge gumin daya tsatsafo, Ɗaya daga cikinsu ta matso kusa da ita ganin how weak she looks ta dafata ta ce“Ko wani abun yana maki ciwo Nana?” Girgiza kanta ta yi cikin sassanyar murya ta ce“a'a I'm fine kawai na matsu naje gida ne” Hameeda ta jinjina kanta kana ta ce“oh really, to ai dai duk saurin ki sai kin jira ko?” Nana ta ɗan kwaɓe fuska ba tare da ta ce komai ba.

Komawa ta yi ta jingina da bango suka ci gaba da kallon jama'a, iyaye sai zuwa suke ana ɗaukan yara. Wata budurwa ce ta ƙaraso wadda ba zata shige 16yrs ba ta rungume Nana tana kuka ta ce“you know what Nana? Zan yi missing ɗinki.. dan Allah karki manta dani kinji” Kukan itama ta saka tana sake ƙanƙameta. Sai da suka ci kukansu sannan ta janye jikinta tana goge hawaye ta ce“Daddyna yazo tafiya dani, Dan Allah Nana ki zo Kano watarana kinji” cikin shessheƙar kuka ta ce“Zan zo in sha Allah bestie” sake rungume juna suka yi sannan ta janye jikinta ta maida idanunta kan yan'uwan Nana dake tsaye ta ce“Hameeda, Maimoon, Amrah Allah ya ƙaddara saduwarmu”

Murmushi suka yi a tare suka ce"Amin Khadijah, ki gaida gida” ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Nana ta ce"bestie na tafi"

"Ki gaida Mommy".

Daga haka ta juya ta tafi tana ɗan waiwayenta. Tana barin wajen Nana ta sake fashewa da kuka, tasan zata yi kewar Khadijah fiye da komai, ƙawarta tun Jss1 har SS3 duk wanda ya san Nana a Aun to tabbas ya san Khadijah, yanda bata ji itama haka take bata ji, ko sanda suna Juniors senior ɗinsu basu isa suyi dealing nasu ba, har suma suka zamo seniors kuma aka basu muƙami, Nana ita ce Amira ta Aun ita kuma Khadijah ita ce health prefect. She wish a ce garinsu ɗaya da Khadijah da tabbas tasan amintarsu zata ɗore, amma yanzu kasancewar suna mabanbantan gari ta tabbata ba lallai bane su ci gaba da ƙawance.

"Ke Nana ki zo zamu tafi"

Muryar Maimoon ta dawo da ita daga tunanin da take, kallonta kawai ta yi sai kuma taja trolley ɗinta ta yi hanyar parking space na makarantar. Tana tafe student na mata magana, wasu su kirata da Amira, wasu kuma su ce A-shuwa. Har sun yi gaba sai kuma Maimoon ta dawo taja hannunta tana faɗin “Kina son a tafi a bar ki ne ko Nana?” banza ta yi mata ta ci gaba da janta suna tafiya har suka ƙaraso gaban babbar motar ƙirar Lexus jeep, black colour sai kyalli take. Tsayawa duk suka yi an kasa samun wanda zai yi knocking ƙofar, Hameeda ta ɗan kalli Nana murya can ƙasa ta ce“je ki buɗe” da sauri Nana ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai. A ƙalla sun ɗauki 3mins suna tsaye kafin Maimoon ta yi shahada ta ƙarasa ta yi knocking glass ɗin gaban motar, a hankali glass ɗin ya fara yin ƙasa, zaune yake cikin motar idanunsa sanye da shade glasses black, fari ne tas mai dogon hanci sannan ga beauty beard data cika fuskarsa. Sanye yake da wata dakkakiyar shadda milk colour sai kyalli take, Maimoon ta ɗan ja numfashi kafin ta ce"Ya..Yaya Sultan"

Shiru ya yi bai bata amsa ba, dan babu alamar ma yaji abin da ta faɗa, ta sake cewa "Yaya mu shigo?" Sai a sannan ya juyo da gaba ɗaya fuskarsa ya kalleta, Asalin kyakkyawan bafulatani mai cikar kamala da sura. Ya zare glasses ɗin idanunsa still looking at her ya ce"ance muku ni driver ne da zan tsaya ina zaman jiranku right?"

Da sauri suka shige motar sanin halin jarabarsa. Nana ta dinga kallonsu ganin sun cike backseat ɗin motar, ta tsaya kamar statue. Maimoon ce ta mata alama data shiga da ido, ta girgiza kanta kawai sai ta fashe da kuka, bin ta ya dinga yi da wani irin mugun kallo kafin ya yi kafa ya kunna motar. Da sauri Amrah ta ce"ke ba zaki shiga ba?"

Cike da masifa ta ce" to ina zan shiga? Ba yan duk kun cike motar" kallonta suka dinga yi, Maimoon ta kalli front seat ɗin ganin babu kowa ya sanya ta ce"baga gaba nan ba, ki shiga mana"

"Ni bana son zama a gaban namiji"

Da sauri ya kalleta sai kuma ya sauka daga motar, zagayowa ya yi inda take ya ɗago fuskarta a zafafe ya ce"Kee ni abokin wasanki ne?"

Fashewa ta yi da kuka ta riƙe gefen kanta ta ce" ni bana son gaba wallahi, ni a baya zan zauna"

Bai sake magana ba kawai taga ya fizge hannunta ya buɗe motar ya turata sannan ya koma ɗaya side ɗin, shiga ya yi ya kulle motar gaba ɗaya sannan ya yi mata key suka bar harabar makaranta. Kuka ta dinga yi kamar wadda aka daka, Hameeda ta dinga kallonta tana tsaki. Sun yi nisa Amrah ta ce"wai ke dallah can ki yiwa mutane shiru, wa ki ka fi iya shagwaɓa?" A fusace ta juyo baya tana kallonta fuskarta caɓa-caɓa da hawaye ta ce"ba zan yi ba ɗin, ko na shiga harkar ki?" Harararta Amrah ta yi amma bata ce komai ba. Nana ta murguɗa baki sannan ta juya ta ci gaba da kukanta.

M-Shuwa Estate,
No. 1–50, Off Girei Road,
Dougirei, Yola North LGA,
Adamawa State, Nigeria.

Tun daga bakin titin ƙaton symbol yake maƙale da sunan M-Shuwa Estate, Suka dinga kallon titin cike da murna da farin cikin dawowa gida, A bakin wani katon gate suka tsaya gate ɗin ya dinga zugewa da kansa sannan ya danna hancin motar cikin estate ɗin, M-Shuwa Estate shi ne sunan dake maƙale jikin wani dogon gini wanda yafi kowanne tsayi a cikin gidan, gidaje ne birjik a ciki kowanne ɗauke da fenti fari da zinariya, kusan duk gidajen kansu ɗaya, guda ɗaya ne wanda ya sha bambam dasu, yafi kowane gida girma da tsayi. Akwai ɗan ƙaramin clinic cikin estate ɗin, hakana akwai islamiyya a ciki da kuma masallaci wanda ke haɗa duk al'ummar dake cikin estate ɗin. Wannan estate ɗin mallakin wani babban attajiri ce wato Alhaji Muhammad Shuwa, Babban mai kuɗi a cikin Adamawa dama Nigeria baki ɗaya, yana da ƙanne guda uku, Alhaji Ahmad Shuwa, Alhaji Kabeer Shuwa, sai kuma ƙaramar wato Mariya Shuwa. Sun kasance ƙannensa wanda ya raina da hannunsa sakamakon rasuwar da iyayensu suka yi tun suna ƙananu, shi ne wanda ya kula dasu har zuwa girmansu ya kuma aurar dasu bayan shima ya yi aure, ya auri wata bafulatanar mata wato Hajiya Khadijah, Mace mai halin kirki da kuma sanin ya kamata. Alhaji Muhammad Shuwa ya gida wannan estate ɗin ne domin samun ci gaba da kuma zumunci a tsakanin ahalinsa, yana da ya'ya guda shida huɗu maza biyu mata, mazan sune Abdusammad, Aliyu, Hameed, sai kuma Safwan. Yayinda matan sune Fatima da kuma Hafsa. Duk wanda ya san tarihin estate ɗin an sansu akan halaye nagari, nagarta da kuma kamewa. Hakan yasa mutane da dama ke sha'awar haɗa zuri'a dasu, sai dai ba'a samun damar haka domin a family na Muhammad Shuwa i junansu suke aure, tun yarinya na ƙarama ake mata miji a cikin gidan, da zarar ta kammala makarantar secondary sai a aurar da ita, wannan tsari an fara shi ne tun samuwar estate ɗin, kuma har zuwa yanzu tsarin yana nan, duk da Alhaji Muhammad Shuwa ya mutu shekaru goma sha biyar da suka gabata, a lokacin Nana tana da shekara ɗaya a duniya. Ba za'a taɓa cewa baya raye ba idan har aka yi la'akari da irin yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da tsari. A yanzu Alhaji Kabeer Shuwa shi ne matsayin M-Shuwa domin shi ne wanda yake bin sa, daga shi sai Alhaji Ahmad wato mahaifin Nana. Kuma Hajiya Khadijah ita ce wadda take zartar da hukunci har yanzu a cikin gidan sannan kuma kowa yana bin ta koda baya so...
Chapter 1 · 0% Book details